Ana gobe wani uba nagari zai aurar da ‘yarsa ta tare a gidan miji, sai ya yanke shawarar fada mata wasu sirruka da za su sanya ta jin dadin zama mara misaltuwa a gidan mjinta. “Ya diyata, daga gobe za ki daina amfani da sunana. Za ki yi farin ciki domin kin auri wanda kike kauna.
Ba ki rasa ni ba saboda na cika burina a kanki, yanzu lokacinki ne ki cika naki burinki ke ma”. “Tun daga kuruciyarki na raine ki ta hanya mai kyau, na ba ki tarbiyya tare da kula da duk bukatunki. A halin yanzu lokaci ya yi da za ki shiga wani sabon babi na rayuwa, wato rayuwar aure a gidan miji. Don haka ki tattaro hankalinki wuri daya, ki bude kunnuwarki da kyau ki saurari abubuwan da zan fada miki game da zaman tare da mutumin da ya zama mijinki”.
“Kin tuna lokacin da kika rubuta jarabawar WAEC da JAMB? Kin zo gare ni kuma na ba ki Naira dubu 20,000 na rijista? To, ko da yake na ba ki, amma kudin ba nawa ba ne. Na san koda yaushe kina tunanin ni ne na biya kudaden. Amma gaskiyar magana ita ce, ba ni da kudin biya miki a wadancan lokutan, mahaifiyarki ce ta ba ni kudin. Kin dai san cewa za ta iya ba ki kudin hannu da hannu, amma sai ta yanke shawarar ta ba ni a hannuna domin in ba ki. Ki taimaka wa mijinki. Wasu lokuta abubuwa za su yi wuya…zai kasance cikin takaici. Ko da haka yana da wuya, a cikin tunaninsa ya ji tsoro. yana jin tsoron kada darajarsa ta fadi
Lokacin ne da za ki bi bayansa kuma ki yi masa biyayya.” “Hanyar da za ki bi ki nuna wa mijinki kauna ita ce ki girmama shi! Kar ki yi jayayya da shi. Wata rana za ku iya samun rashin jituwa da shi amma daga karshe, ya san yana da girma. Za ki iya tuna ranar da na yi kururuwa a wajen mahaifiyarki? Mene ne ta yi? Ta yi shiru! Kina kuma tunawa da ranar da ta yi kururuwa a kai na? Mene ne na yi? Na yi shiru! Yarinyata ki koyi zama shiru lokacin da mijinki ya fusata. Lokacin da mutum ya yi zafi, dayan ya zama sanyi. Idan dukkan ku biyu kuna yin kururuwa a lokaci daya, wannan shi ne yadda manyan matsaloli ke fara wa a cikin aure”.
“Abu na farko da ya kamata ki sani game da mijinki shi ne, abincin da yake so! Idan yana son abinci fiye da daya, to, ki rike su a cikin zuciyarki. Kar ki bari ya tambaya, ko yaushe yi kokarin ki dafa masa.” “Wata rana mahaifiyarki ta kama ni ina rike da hannun wata mace da nake so. Na yi sha’awar wannan matar amma ban riga na aikata wani ta’asa da ita ba. Lokacin da ta gan mu, ba ta yi fada da matar ba, sai ta wuce. Na ji tsoron komawa gida saboda lallai na san za a samu tashin hankali mai tsanani.
Amma lokacin da na dawo gidan ta ce ba komi. Ta ba ni abinci. Sai na sha jinin jikina. Na fara rokonta. Tun daga wannan rana, ban kara kallon mace ba sau biyu. Wane ne ya sani? Idan ta yi min wani barazana… watakila da na koma wajen waccan yarinyar mu ci gaba da soyayyarmu. Wani lokaci yin shiru ya fi bayar da fa’ida fiye da yin fada”. “Ki manta da wadannan litattafan da kika karanta lokacin kina ‘yar shekara 21.
Kin tuna da fina-finai na Indiya da na Amerika? Har ila yau, kin tuna da fina-finai masu ban sha’awa na game da shirin Afrika? Ki manta da su! Kada ki yi tsammanin rayuwar aurenki ta kasance hakan. Rayuwa ta bambanta da almara.” “Abu na karshe da nake so na gaya miki… kina tuna yadda aka haife ki? Bayan bikin aurenmu, abubuwa suna da yawa, kuma mahaifiyarki ta yi ayyuka guda biyu domin tallafa mana.
Ina komawa gida karfe shida na dare ita kuma tana komawa gida takwas na dare a gajiye. Amma idan muka kwanta… ba za ta hana ni abincin dare ba. Wannan shi ne yadda aka haife ki. Kada ki dauko wani halin da za ki hana mijinki abincinsa na dare. Ki zama matar kirki. Kullum za ki kasance yarinyar babanki”.