• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaraba Ga Mata: Hanyoyin Mallakar Miji Cikin Sauki

by Rabi'at Sidi Bala
3 years ago
Mata

In kina son ki shawo kan wuta ko ki kashe ta gaba daya ba wata wutar za ki kara mata ba, nemo ruwa mai sanyi ki kwara mata ki sa ido ki gani in za ta ci gaba da habaka, haka namiji ya ke. Da wasu shawarwar a kan yadda za mallaki mijin ki.

-Namiji bai son a ce kina ba shi umurni, bare a ce kina yi masa nasiha, duk kuwa da cewa yana bukatar nasihar a zahiri, don haka in kina bukatar zuwa wani wuri kar ki ce masa “Zani wuri kaza” ki saka ta a sigar tambaya “Ina son na tambaye ka ne, dama na so zuwa wuri kaza ne” ko in kina bukatar wani abu kar ki ce “Ka ba ni kaza zan yi kaza” ki zabi lafazin da za ki yi aiki da shi, kamar ki ce “Muna bukatar abu kaza ko za sayo ne?” Da duk irin lafazin da ke nuna girmamawa da bukatar abin a wurinsa, wata gatsar take fadi, har ma ta kara da cewa “In ba haka ba sai dai a zauna haka”.

  • Amfanin Lalle Wajen Gyaran Fata
  • Jami’an Tsaro Sun Kuɓutar Da Wata Soja Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Iyakar Enugu Da Imo

 -In kuma dawowa gida ya yi, tarbe shi ku shigo tare, in yana rike da wani abin, karba masa, sai dai in ya nuna ba ya so, kamar jakar kudi da wasu abubuwa da suke bukatar sirri, kar ki yi irin abin da wasu matan suke yi, wadanda ko matsawa daga inda suke ba sa yi, sai dai su ce “Sannu da zuwa!”.

-In kuwa ya fadi maganar da kike ganin cewa kuskure ce kar ki ce ba haka ba, ki jinjina wa tunaninsa ki bar shi haka, daga baya ki dawo da ita ta wata sigar ki ba shi shawara a kai yadda ba zai fahimci cewa fito na fito kike yi da fahimtarsa ba.

– In kuma ya yi miki ba dai-dai ba kar ki kullace shi, bare har ki ce za ki rama, yafe masa, wata rana zai kyautata miki, namiji ne.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

– Duk kyautar da ya yi miki ko da ba ki bukatarta, ki nuna masa godiyarki tamkar ba abin da kike so kamarta, daga baya bayan ya manta ki nuna masa wata wace ta fi wannan, don kar ya kara kawo miki ta farko.

– In za ku shiga wuri tare ki dan yi baya shi ya fara yin gaba, sai in shi ne ya ba ki damar ki wuce.

– In yana karanto miki matsalolin da ake ciki, ki  zabi kalmomin da za ki rika karfafa masa gwiwa, ki rika yaba wa irin kokarin da yake yi duk da matsalolin da yake fadi.

– Kar ki yarda gardama ta rika hada ku, ba ta karewa da kyau, in ya ja ki sake, shi da kansa zai gano bai yi dai-dai ba, wasu mazan su kan ba da hakuri, wasu kuma sai dai su yi ta janki da wasa ko su yi miki kyautar da ba su yi niyya ba.

– In kika ba shi shawara bai dauka ba daga baya abin ya cabe masa kar ki ce “Ai dama na gaya maka” ki nuna masa damuwarki.

– In kika roke shi wani abin ya ce ba shi da shi kar ki nuna rashin jin dadinki, yabe shi ki ce “Ai kai mai yi ne, tun da ka ce babu wallahi na san babu ne, amma Allah ba zai barka haka ba zai kawo in sha Allah”.

– In ya kawo miki matsalolin ‘yan uwansa ki nuna damuwarki, kar kare su kar ki zarge su, sai iya gama ki ya ba masa a kan hakurin da yake yi da su, ki karfafa masa gwiwa, ko da kuwa kin san ba wani abin da yake yi na a zo a gani.

– In zai fita ki raka shi har bakin kofa.

– Ki tabbatar ya sa kaya masu kyau, ki goge masa takalmansa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu!
Rahotonni

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Next Post
Yanzu-Yanzu: Tsohon Paparoma Benedict XVI Ya Rasu Yana Da Shekaru 95

Yanzu-Yanzu: Tsohon Paparoma Benedict XVI Ya Rasu Yana Da Shekaru 95

LABARAI MASU NASABA

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.