Tsarabar Amarya

Fassarar Bello Hamza

A duk lokacin da aka ce mace za ta yi aure, burinta shi ne ta ga ta samu shiga dakin miji lafiya kuma ta yi zaman aurenta a matsayin bautar Ubangiji (SWT). Samun cikar annan burin yakan yi wa wasu sauki; wasu kuwa abin yakan ba su wahala. Domin ba da gudunmawa ga duka bangarorin biyu, mun fassaro muku wannan nasiha mai saukin aiwatarwa kamar yadda wasu magabata suka yi wa ‘ya’yansu masu zua aure. A yi kokarin karantawa kuma a yi aiki da shi:

 

‘Abd al-Malik (RA) ya ce: “Lokacin ‘Awf ibn Muhallim al-Shaybani, daya daga cikin shugabannin Larabawan da ake mutuntawa lokacin jahiliyya, ya aurar da ‘yarsa Umm Iyas ga Al-Harith ibn ‘Amr al-Kindi, lokacin da za a kai ta gidan mijinta sai mahaifiyarta, Umamah ta zo domin yi mata nasiha inda ta ce:

‘Ya ke ‘yata, idan da za mu duba kyawawan dabi’unki ne da ba za a yi miki wannan nasihar ba, sai dai da yake ya zama tilas mu yi miki a matsayin tunatarwa, domin zai tuna miki wasu abubuwan da kika manta, hakan kuma zai taimake ki.

‘Ya ke ‘yata idan a ce mace za ta iya zama babu miji, saboda dukiyar mahaifinta da kuma son da yake mata, da ke ce kika kowace mace cancanta da yin haka, to amma an halicci mata domin maza kamar yadda aka halicci maza domin mata.

‘Ya ke ‘yata, yanzu kin kusa barin gidan da kika taso, inda kika fara koyon tafiya, yanzu za ki je inda ba ki sani ba, za ki hadu da wadanda ba ki saba da shi ba. Wanda ya aure ki yanzu ya zama shugabanki, saboda haka, ki zama mai yi masa biyayya.

‘Ki lura da wadannan nasihohi guda goma, wadanda za ki dinga tuna su.

‘na farko da na biyu shi ne, ki natsu da kasancewa tare da shi, ki saurare shi ki kuma bi umarninsa saboda gamsuwa na  zuci sauraro da bin umarnin miji na dadada wa Allah”

‘Na uku da na hudu shi ne ki zama mai kamshi da kuma cikin kwalliya a kodayaushe, ka da ya ga munin ko kadan kuma ka da ya ji wani wari daga gare ki sai kanshi.

‘Na biyar da na shida shi ne ki dinga gama abinci a kan lokaci, ka da ki da me shi da surutu in ya na barci, saboda yunwa ba ta da dadi kuma tayar da shi daga barci zai bata masa rai.

‘Na bakwai da takwas shi ne, ki kula da ma’aikatansa da ‘ya’yansa tare da dukiyarsa, saboda kula da dukiyarsa na nuna yabawarki kuma kula da ‘ya’yansa na nuna kwarewarki wajen tafi da gida. ‘na tara da goma kuma su ne, ki kare sirrinsa kuma kada ki ki bin umarninsa, saboda in kin bayyana sirrinsa ba zai taba amincewa da ke ba in kin bijirewa dokarsa zai tsane ki

‘ki kula ‘ya ta, ka da ki bayyana jin dadinki in yana cikin bacin rai kuma ka da ki bayyana bacin ranki in yana cikin nishadi.

‘ki mutunta shi kwarai da gaske ki kuma yadda da maganganunsa, yin hakazai sa ya rika jin dadin hira da ke.

‘ki sani ya ke ‘yata, ba za ki cimma buri ki ba sai kin mahimmantar da bukatarsa a kan na ki, duk abin da ya so ki tsane shi, Allah Ya kare ki Ya kuma zaba maki abin da ya fi alhairi.

 

Exit mobile version