Sa-in-sa da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi kan wanda zai yarda ya dauki nauyin karuwar talauci a tsakanin mutane ba shi ne abun dubawa ba.
Dukkanninsu suna neman wanda za a zarga ne a tsakaninsu a maimakon su duba mafita amma sun ki. Gwamnonin jihohin da suke gardama sun hadu a mataki daya, maimakon wani ya fara tunanin tsare-tsaren da za su kawar da talaucin da ke damun mutane.
- Banda Akwai Doka Da Mun Shiga Gidan Gwamnatin Bauchi Mun Kwato Mulkinmu —Adamu
- Shehu Sani Ya Yaba Wa ‘Yansanda Kan Cafke Wadanda Suka Farmaki Tawagar Atiku A Borno
Tarihi ya nuna cewa gwamnoni za su iya taimakawa wajen rage talaucin kamar yadda muka sani. Misali Sanata Ahmed Makarfi wanda ya bi wasu tsare-tsaren jam’iyyarsa ya gabatar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna wanda tsarin ya fara tun daga kasa. Wannan tsarin zai fi tasiri ga al’umma da suke can kasa.
A karkashin mulkin Ahmed Makarfi tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2007, gwamnatin Jihar Kaduna ta kashe Naira biliyan 98 wajen gudanar da manyar ayyuka a ko’ina cikin jihar. A lokacin da aka daidaita tashin abubuwa a shekarar 2020 jimillan yake daidai da Naira biliyan 526. Wanda yake daidai da Naira biliyan 66 a duk shekara. Wannan kudi za a ga kamar sun yi kadan. Duk da haka jihar ta yi kokarin yin ayyuka kanana da matsaikaita da kuma manya-manya.
Ayyukan dai sun hada da gina hanyoyi a birane da kauyukan jihar, da manyan gine-gine da samar da kayayyakin noma da gina makarantu da asibitoci da gina wuraren koyon sana’o’i da samar da ruwan sha mai tsafta ta hanyar haka rijiyar burtsatsi a tsakanin al’umma da samar da kayayyaki a asibitoci da sanya wutar lantarki a kauyuka da kirkirar gundumomin raya kasa.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar da wani kwamiti da ya bayyana cewa gwamnatin ta gina hanyoyi sama da 200 a fadin jihar. Wanda ya hada da hanyoyi a kauyuka da kuma birane wadanda suka hada garuruwa.
Don abubuwan ci gaba su daidai a tsakanin al’umma, an samar da yankunan ci gaba guda 46 a karkashin ma’aikatan kula da ci gaban kauyuka da al’umma. An sami wutar lantarki da yawa a kauyuka karkashin mulkin Ahmed Makarfi wanda ya tabbatar da cewa gaba dayan jihar an hada su da babban layin wutar lantarki na kasa. Gwamnatin ta gina gidajen ‘yan majalisa da gyara kwatas-kwatas na gwamnati sama da 700 tare da gine-gine gwamnati a jihar. Haka kuma mafi yawansu a yanzu an sayar da su. Ayyukan ya bai wa mutanen karkara damar samun karuwar tattalin arzikinsu wanda ya rage talauci.
A ayyukan da aka yi a birni, akwai tsohuwar gadar saman nan ta Kawo wanda ya zama na farko a Arewa don babu jihar da ta fara yin irinsa a wancan lokaci. Kuma za a iya cewa wannan aiki ne ya zama hasashe har wannan gwamnatin ta fadada shi. Gwamnatin ta kammala aikin Gamji Gate da kuma fadada Murtala Skuare da bangare na biyu na gidan gwamnati mai suna General Hassan Usman Katsina wanda ya zama na zamani.
Gwamnatin kai-tsaye tana shirin kawar da talauci ne a cikin al’umma, kamar samar da kananan basuka ga kungiyoyi da kuma daidaikun mutane. Abubuwan da aka amfana sun hada da tsabar kudi da ababen hawa da gidaje da sauran abubuwan gudanar da kasuwanci. Kananan basukan ya taimaka matuka wajen fitar da daruruwan mutane daga cikin talauci.
A bangaren lafiya kuwa, gwamnatin ta gina sabuwar kwalejin kimiyyar lafiya da kwalejin horas da masu jinya da unguwar zoma. An gina ne tare da kara darajar manyan asibito da cibiyoyin lafiya a jihar gaba daya su koma na zamani. Gwamnati ta ci gaba da samar da kayayyakin gwajin HIB da magunguna da kuma gina cibiyoyin kula da lafiyar hakora da wuraren bayar da jini a dukkanin jihar.
Idan kuwa aka koma bangaren noma, gwamnatin ta kirkiro da shirin nan na a koma gona ga mutum 2,300 da tare da shirye-shirye na musamman a kan aikin noma. Kayayyakin noma da suka hada da takin zamani sun yi sauki kuma ana samunsu a ko’ina a jihar, yayin da gwamnati ta bayar da tallafi na musamman a kan farashi mai rahusa. Ta sayi taraktoci sababbi sama da 250 tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jihar da samar da magungunan kwari da iri na zamani da kuma kayan feshin maganin. An sha yashe madatsun ruwa a jihar domin samun isasshen ruwa da kuma taimaka wa wajen noman rani. Jihar ba ta fuskanci matsala a kan noma ba da ya kai ga karancin abinci fiye da yadda ake ciki a yanzu.
A bangaren ilimi kuwa, gwamnatin ta zuba jari sosai don ci gaban mutane. Daya daga cikin aikin da ta yi da har yanzu ake cin moriyarsa a bangaren cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare su ne, kamar jami’ar Jihar Kaduna da ke cikin garin Kaduna wanda a lokacin da aka samar da jami’ar kudin makaranta yana da sauki ga talakawa. A shekarar 2022 jami’ar ta yaye dalibai sama da 10,000. Ana bayar da tallafin karatu ga ‘yan jihar wanda yake matsakaici shi ne a bai wa dalibai 12,500, amma a shekarar 2004/2005 an bai wa sama da mutum 20,000 tallafin karatu.
Haka kuma gwamnatin ta samar da wuraren koyar da sana’o’i ga mata a dukkanin kananan hukumomi 23 da suke jihar. A banagren ilimi na bai-daya, an sami azuzuwa 1,800 da ofisoshi da bayuka da magudanan ruwa a jihar duka an gina su a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2005. Haka kuma an gyara azuzuwa sama da 4,500 da ofisoshi tare da sanya kujeru wanda har yanzu ana amfani da su.
Wadannan ayyukan ci gaba ya sanya gwamnati da ta biyo baya ba ta da wasu ayyuka a wuyanta da yawan gaske. Kuma wadannan nasarori sun sanya mutane sun matso kusa da gwamnati. Sai suka rika ji su ma suna cikin bangaren gwamnati ana tafiya tare da su, an rage talauci an inganta ilimi da habaka lafiya da samar da gidaje da sauran abubuwan more rayuwa.
Lallai kuwa al’umma sukan ji dadi idan suka an sami ci gaba. Sakamakon abun da aka samu an kara abubuwan bukatuwa kamar lafiya da ilimi da kuma inganta rayuwa. Labarin nasarar da aka samu ba za a manta da shi ba. Jihohi kamar su Bauchi da Katsina har yanzu suna duba ayyukan da tsofaffin gwamnoninsu suka yi masu, Ahmed Mu’azu da Ummaru Ya’adua wadanda suka yi mulki a tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2007.
A yanzu sakamakon da yake nunawa babu kyau, wanda yake nufin tsarin da ake yi ba ya aiki. Wasu suna nuna cewa komi daidai ne, amma kuma suna tunanin samun wani sakamako daban. A shekara 2023, dole ne mu canza tsarin ta hanyar zaben wadanda suka cancanta, idan ba haka ba, za mu ci gaba da zama a yanayin da muke ciki. Allah ya kyauta.