Matsalar tsaro na ta kara damun al’ummar arewacin kasar nan, musamman wadanda ke nesa, ganin yadda ake ta gudanar da harkokin yau da kullum cikin zulumi da fargaba. A makon da ya gabata kadai, rayukan mutane da dama suka salwanta tare da yin garkuwa da mutane domin samun kudaden fansa.
Ganin yadda wannan lamari ke kara ta’azzara ne ya sa dattawan arewa ke shirin gayyatar gwamnonin yankin Arewa domin jin dalilansu na kin yin abun a zo a gani game da rashin tsaro a arewacin Nijeriya. Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa a Kudancin Nijeriya, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya bayyana wa manema labarai matsayinsu, inda ya bayyana cewa shugaban kasa yana da mutane wadanda ya kamata ya ja su a jikinsa, domin su ba shi bayanin abubuwan da suke faruwa, amma kuma bai yi amfani da wannan damar, sai dai ba a sani ba sakaci ne ko girman kai ko kuma wani abu ne wanda ba a sani ba.
“Amma dai muna ci gaba da tattaunawa a tsakaninmu da sauran bangarori daban-daban dangane da abubuwan da suke faruwa. “Idan a yankin Kudu ake yin irin wannan kasan kiyashin da ake yi a arewa, to da tuni duniya ta saka baki. Gwamnati ta siyo makamai wanda har yanzu ba a gani a aikace ba. Shugaban kasa sai dai a dunga kawo masa labari a rubuce ba tare da bin diddigi ba ko labarin nan gaskiya ne ko akasin haka.
“Domin abubuwan da suke faruwa ya yi yawa. Ko kasar Mali wanda sun san cewa Turawa ne suke daukan nauyin ta’addanci, amma sun tashi tsaye wajen kama ‘yan ta’addan tare da mika su wurin da ta dace wanda an kasa gudanar da hakan a Nijeriya saboda munafurci ba zai bari ba,” in ji shi. Ya ce kungiyarsu ta zaburar da matasa wajen shiga cikin harkokin siyasa domin a dama da su.
Sai dai ya ce matasa ba su da kudi a hannunsu wanda ya hana su shiga cikin harkokin siyasa gadan-gadan. Ya ce idan mutum yana dan talaka duk irin karatun da ya yi ba zai samu aiki ba, domin burin wadannan shuganinmu shi ne, idan suka tsofa ‘ya’yansu su ci gaba da mulkanmu tun da dai ba mu da ‘yanci wanda ba a dauke mu mutane ba, musamman ma mutanen arewa.
Ya ce mutumin arewa bai isa ya fito zanga-zangar lumana ba, idan ma ya yi yunkurin hakan, jami’an tsaro za su harbe na harbewa tare da kama na kamawa wanda ba a yin haka a yankin kudu. Ya kara da cewa a wannan karon matasa suke sha’awar a bai wa mulkin kasar nan tun daga kan shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisu na tarayya da na jiha.
Ya ce tun da dai matasa talakawa ba su da karfin aljihu da za su iya tsawa tarara, manya wadanda suka kwashe kudaden kasa su bai wa ‘ya’yansu damar gadar mulkin Nijeriya, amma su ba sa bukatarsu a kan karagar mulkin kasar nan saboda a bai wa matasa damar tafiyar da harkokin mulki a Nijeriya. A cewarsa, idan Allah ya bai wa matasa mulkin kasar nan, za a samu damar gudanar da harkokin mulki cikin basira da dubaru na zamani fiye da wanda shekarunsu suka ja.
Ya ce ko a cikin matasa akwai abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su kafin daurasu a kan karagar mulki, daga ciki akwai nagarta wanda matasa sun san masu nagarta a cikinsu, ba wai gwamnati ta fitar da dan takara ba wanda zai kare muradin gwamnati ba talakawa ba.