Connect with us

LABARAI

Tsaro: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa Da Mutane

Published

on

… Mutum Biyar Kawai Na Taba Kashewa –daya Daga Cikinsu

Jami’an ‘yan sanda na musamman masu kai samamen masu laifi, ‘Intelligence Response Team’ sun yi nasarar cafke wani shahararre kuma makashi a kungiyar garkuwa da mutane, mai suna Musa Umar, inda ya bayyana cewa, shi ke yin kisa a kungiyar ta su, wanda ya kashe mutum biyar daga cikin wadanda suka kama.

Musa Umar dan kimamin shekaru 22 a duniya, ya gabata tare da sauran mutane 20 ‘yan kungiyar ta su, a gaban Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, DCP Frank Mba, a ranar Larabar ta da gabata, a garin Abuja.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa, ya shiga cikin kungiyar ne a Jihar Kaduna kimanin shekaru uku da suka gabata, kuma aikin sa shi ne kashe wadanda aka sato, kuma ya zuwa lokacin da aka kama su ya kashe maza uku da mata biyu, dukkansu daga Jihar Katsina.

Da yake magana, Musa yk bayyana cewa, “ni manomi ne kuma haka zalika mai garkuwa da mutane. Ni ne mai kisa a kungiyar mu, ya zuwa yanzu, na kashe mutane biyar, a cikin su akwai maza uku da mata biyu kuma dukkaninsu daga Jihar Katsina suke”.

A halin da ake ciki yanzu, Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kama ‘yan ta’adda 24, daga cikin su akwai masu garkuwa da mutane, ‘yan kungiyar asiri, ‘yan fashi da makami, da kuma masu satar motoci wadanda ake zargi da tayar da zaune tsaye a cikin al’ummar Abuja.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Bala Ciroma ya bayyana cewa, wasu daga cikin ‘yan kungiyar asirin da aka kama, an kama su ne yayin da suke kaddamar da wani bikin bakin gatari ‘Black Ade’ ga mambobin kungiyar.

Ciroma ya ce, “a ranar 12 ga Yuni, 2020, yayin kaddamar da wani aiki, jami’an ‘yan sandan mu daga sashen Anti-One Chance Unit, sun samu nasarar kama wasu daga cikin ‘yan kungiyar asirin ‘balck Ade’, wanda a cikin akwai mai suna, Prosper Jerry 21, Jeff Ikenna 34 da Uche Uzosike 41, kuma dukkanin su maza ne.

Wadanda ake zargin sun bayyana cewa, su mambobi ne a kungiyar asiri na Black Ad, kuma a wasu lokutan sukan kike bindiga mai kirar Pistol.

Har ila yau, “Tsakanin Ketti, Gwagwalada da Zuba, jami’an rundunar ‘Anti-Kidnapping Skuad’ sun kama mutane hudu da ake zargi da laifin satar shanu da satar mutane a yankin.

Wadanda ake zargi, Jubril Muazu 21, Abdullahi Muhammed 27y, Adamu Musa 34 da Babuga Ardo 19, sun yi bayanin matsayin su kungiyoyin ta su.

Jami’an sun kuma yi nasarar kwace makamai da sanduna a hannun wadanda ake zargi. Haka kuma, “a ranar 26 ga Yuli, 2020 bisa korafin da ake yiwa ‘yan sanda akan garkuwa da mutane, rundunar ‘yan sanda daga sashen Anti-One Chance ta kama Sarauniya Torkwase  Ayakpa mai shekaru 37 a kauyen Mashafa, Mpape bayan ta hada kai da wata mai sun, Fidelis Ikule 36, wajen basaja akan cewa an sace ta.

“Wanda ake zargin ta bayyana cewa, ta yi basajan ne don karban dubu 20,000 daga hannun babbar yar ta. A cewar ta, manufarta ita ce ta yi amfani dubu 20,000 din don fara kasuwanci.

A yayin kama masu garkuwa da mutane, Hukumar ta ce, “a ranar 18 ga Yunin 2020, Jami’an leken asiri na ‘yan sanda daga rundunar yaki da satar mutane, a yayin sintiri sun samu damar kama masu satar motoci, a cikin su akwai, Zakari kaura 41, Sirajo Ibrahim 38, Usman Adamu 43, Tasiu Abdullahi da Abdulkadir Muktar 32 duka maza, akan hanyar Utako-Berger, da makullan da suke amfani dasu wajen bude kowane irin mota

Rundunar ‘yan sanda ta kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa laifukan su, kuma sun bayyana cewa, sun saci sama da motoci 10, akan hanyar Utako-Berga

A cewar wadanda ake zargin, mafi yawan motocin da suke sata suna sayar wa ne a wajan Nijeriya. An kama su da motar sata mai kirar Pontiac bibe.

Jami’an sun bayyana cewa, za su ci gaba da kokarin dawo da motocin da wadanda ake zargin suka sace.
Advertisement

labarai