ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaron Iyakoki: NIS Ta Yaye  Zaratan Jami’ai Mata Masu Ɗaukar Makami A Karon Farko

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
Tsaro

A ƙoƙarin tabbatar da tsaro a iyakokin ƙasa da magance aikata lailufa a iyakokin ƙasar nan, Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta yaye zaratan jami’ai mata masu ɗaukar makami a karon farko da ta horar domin gudanar da aiki na musamman.

Da yake gabatar da jawabi wajen faretin yaye jami’ai matan guda 61 a ranar Juma’a, Shugaban NIS, Isah Idris Jere ya bayyana cewa babban aikin hukumar shi ne samar da tsaro a iyakokin ƙasa domin ƙarfafa tsaron cikin gida.

  • Aisha Buhari Ta Janye Kara Kan Aminu Mohammed Da Ya Ce Ta Yi ‘Bulbul’

ADVERTISEMENT

“A wannan biki na yau, rana ce ta ƙarfafa mana giwa na ƙoƙarin tabbatar da cewa mun tsare iyakokinmu da rayuka da dokiyoyin mutanenmu.

“Hukumar NIS tana da muhimmiyar rawa da take takawa wajen yaƙi da ‘yan ta’adda, laifukan iyakoki da kuma sauran duk wata barazanar tsaro da ke fuskantar ƙasarmu. Domin ƙara ƙarfafa abubuwan da muka daɗe muna gudanarwa na tsawon lokuta, shugabancina ya mayar da hankali ne kan wasu ɓangarori guda uku waɗanda suka hada da: Kula da jin daɗin jami’anmu, gudanar da aiki ba tare da jinkiri ba da kuma inganta aiki irin wanda ake yi a ƙasashen da suka ci gaba a duniya wajen tabbatar da tsare iyakokin ƙasarmu.

LABARAI MASU NASABA

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

“Bisa waɗannan ɓangarori da na lissafo, NIS a ƙarƙashin jagorancina, a ko da yaushe ina muhimmanta kyautata jin daɗin jami’ai da ba su horo a-kai-a-kai ta yadda za su iya fuskantar ƙalubale daban-daban da ƙasarmu ke fuskanta. Za mu ci gaba da bayar da horo da sauran wasu shirye-shirye masu muhimmanci a gida da kumą ƙasashen ƙetare domin ƙara samun ilimi da shirya jami’anmu ta yadda za su iya sauke nauyin da ke kansu.”

Jere ya ƙara da cewa wanna biki wani mataki ne da zai ƙara kwazon aikin hukumar wajen inganta ayyukan jami’a a yankunan da ke fama da rashin tsaro a wurin gudanar da ayyukan ƙasa kamar yadda ake buƙata a lokaci bayan lokaci.

Ya ce waɗannan jami’ai guda 61 dukkansa mata ne waɗanda suka samu horon aiki kan yadda ake sarrafa makamai, kakkaɓo jirgi, tsaron iyakoki, yaƙar ‘yan ta’adda da sauran harkokin bincike da kuma horon sirri.

“Kamar yadda kuke iya gani a yau, waɗannan jami’ai sun nuna zimma tare da aiki kafanɗa da kafaɗa da maza wajen yi wa ƙasarmu hidima. Ina sanar muku da cewa a yanzu haka hukumar ta ɓullo da shirin horar da jami’ai sama da 1000 a makarantar bayar da horo da ke Kano da kuma makarantar horar da jami’an kwastom da ke Goron Dutse a Kano. Muhimmancin bayar da wannan horo shi ne, tabbatar da cewa jami’anmu sun samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasarmu da kuma yin kafaɗa da kafaɗa da takwarorinsu na duniya wajen gudanar da ayyukan shige da fice.

“A wannan gaɓa, ina taya murna ga kwamandan NITSA da ma’aikatansa bisa kafa tarihi a yau, gaskiyar magana ita ce, aiki ne na farkon wanda ya horar da waɗannan zaƙaƙuran jami’ai, da farko sun kasance kamar ba za su iya ba, lallai ka gudanar da gagarumin aiki wanda ka cancanci yabo, hukumar gudanarwa ta NIS tana alfahari da kai bisa jajircewa wajen gudanar da aiki.” In ji CGI Jere.

Ana sa rai waɗannan jami’ai mata su taimaka wa ƙarfafa tsaron iyakokin da za a tura su kamar yadda NIS ta ƙudurta bisa jagorancin

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Next Post
Shugabannin Kasashen Afirka Da Na Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Nuna Alhinin Rasuwar Jiang Zemin

Shugabannin Kasashen Afirka Da Na Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Nuna Alhinin Rasuwar Jiang Zemin

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.