Hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta tabbatar da ruftawar wani gini a yankin Sabon Lugbe na Abuja, inda mutane bakwai suka rasa rayukansu.
Lamarin ya faru a unguwar rukunin gidaje na Gidash kusa da hanyar filin jirgin sama, inda masu tara kayan sharar gida suka girgiza ginin yayin da suke ƙoƙarin cire sandunan ƙarfe da wasu kayan.
- Za Mu Fara Kamen Mabarata A Abuja – Wike
- ‘Yansanda Sun Yi Artabu Da Masu Garkuwa Da Mutane A Abuja
A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta babban birnin tarayya (FEMD), an yi wa ginin alamar rusa shi ta hannun ma’aikatar ci gaban birane, kuma masu aikata wannan aika-aikar sun yi amfani da ƙarshen mako domin kwashe kayan ginin.
Daraktan riƙo na FEMD, Injiniya Abdulrahman Mohammed, ya bayyana cewa wannan aiki na jari bila haramtaccen aiki ne wanda ya yi sanadiyar ruftawar ginin.
Haka kuma, an ceto mutane bakwai daga wurin, kuma FEMD ta kammala bincikenta, ta tabbatar da cewa babu sauran mutane da suka maƙale a ƙarƙashin ginin.