Biyo bayan arcewar fursunoni da ke gidan gyaran hali na Suleja a jihar Neja, rundunar ‘yansandan jihar Kwara da ke makwabtaka da Neja, ta ce, ta sanya jami’anta cikin shirin ko-ta-kwana.
Rundunar, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Toun Ejire-Adeyemi, wacce aka bayyanawa manema labarai a Ilorin ranar Lahadi, ta bawa mazauna jihar tabbacin kariya da shirin ko-ta-kwana.
- Zainab Youssef: Mace Ta Farko Da Ta Samu Lasisin Injiniyar Jiragen Sama A Sudan
- Sharhi: Bukatar Sake Farfado Da Kiwon Tarwada A Nijeriya
“A ranar 24 ga Afrilu, 2024, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da daddare, wanda ya yi sanadin rugujewar katangar gidan yari da ke Suleja a jihar Neja, hakan ya yi sanadiyyar tserewa fursunoni 118.”
Toun ta kara da cewa, kwamishinan ‘yansandan ya tabbatar wa da jama’a cewa, an samar da isassun matakan da za su hana duk wani yunkuri da fursunonin ke yi na shiga ko haddasa barna a jihar.