Tsoffin ƴansandan Nijeriya sun gudanar da wata zanga-zanga a Abuja ranar Litinin don nuna rashin jin daɗinsu game da tsarin fansho da kuma rashin kyakkyawan tsarin walwala bayan ritaya.
Zanga-zangar, wadda Ƙungiyar Tsoffin Ƴansanda ta Ƙasa ta shirya, ta fara ne daga harabar Majalisar tarayya da nufin ci gaba zuwa shalƙwatar Ƴananda.
- Abin Da Ya Sa Nake Rungumar Ɗana Ina Wakar Soyayya – Tsohuwar Matar Adam Zango, Amina
- ‘Yan Kasuwa Na Shirin Yi Wa Dangote Zanga-zanga Kan Rage Farashin Gas
Tsoffin ƴansandan sun bayyana tsarin fanshonsu a matsayin mai nuna bambanci da zalunci, inda suka ce da dama daga cikinsu sun mutu ba tare da sun karɓi haƙƙoƙin fanshonsu yadda ya kamata ba.
“Ƴan’uwammu na mutuwa cikin wahala,” in ji ɗaya daga cikin masu zanga-zangar. “Muna neman adalci da mutunci bayan shekaru da muka shafe muna bauta wa ƙasar nan.”
Duk da gargaɗin da kwamitin hulɗa tsakanin Jama’a da Ƴansanda (PCRC) ya bayar, tsoffin jami’an ƴansandan sun dage akan buƙatunsu, inda suka nemi a cire su daga tsarin fanshon haɗakar kuɗi gaba ɗaya a mayar da su tsarin fansho kamar na Sojoji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp