Mahdi M Muhammad" />

Tsoho Mai Cutar Kanjamau Ya Yi Wa ‘Yar Shekara Biyar Fyade

Fyade

Wani dan shekaru 70 da aka bayyana da suna Nicholas Akeh, ya shiga hannun ‘yan sanda na reshen jihar Benuwe bisa zargin yi wa yarinya ’yar shekara biyar fyade a jihar.

An kama wanda ake zargin mai cutar kanjamau ne a Naka, karamar hukumar Gwer da ke jihar.
An tura shi hedikwatar ‘yan sanda da ke Makurdi a ranar Talata don ci gaba da bincike.
Wanda ake zargin ya bayyana wa ‘yan sanda cewa, ya yaudari karamar yarinyar ne ya ba ta garri ta sha, sannan ya yi mata fyade.
Ya yi ikirarin ya kwashe shekara 20 yana dauke da kwayar cutar kanjamau (HIb), kuma tun lokacin da matarsa ta yi watsi da shi, abin da kawai yake da buriin yi shine ya tilasta kansa akan ‘yan mata don biyan bukatarsa ta jima’i.
Kakakin rundunar, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce, “wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma ana ci gaba da bincike”
“An tsare wanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda ta Benuwe yayin da ake ci gaba da bincike. Nan da mako guda za a gurfanar da shi a gaban kotu,” inji ta.

Exit mobile version