Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande Ya Rasu

Tsohon gwamnan jihar Legas, kuma gwamna farar hula na farko a jihar, Alhaji Lateef Jakande ya riga mu gidan gaskiya; Alhaji Lateef ya rasu yana da shekaru 91 a duniya.

Gwamnan Jihar Legas, Cif Sanwo-Olu ne ya sanar da lamarin a shafin sada zumuntar shi na Twitter.

Alhaji Lateef ya yi mulkin jihar ne a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983 wato daidai da lokacin shugabancin Marigayi Alhaji Shehu Shagari kenan.

Exit mobile version