Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya koma African Democratic Congress (ADC).
Ya sanar da ficewa daga jam’iyyar ne cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 26 ga watan Nuwamba, 2025, inda ya ce yana son taimakawa wajen gina haɗin kan ‘yan Nijeriya.
- Sabuwar Manufar Habaka Ciniki Ta Sin Ta Samarwa Duniya Manyan Damammaki
- Tawagar Shugaban Ƙasa Ta Isa Bauchi Don Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi
Bayan ficewa daga SDP, El-Rufai ya ziyarci ofishin ADC na Ungwan Sarki da ke Kaduna, inda aka yi masa rajista kuma aka ba shi katin shaidar zama ɗan jam’iyyar.
Tun da farko, shugabancin ADC ya bayyana cewa mutane masu gaskiya ne za su zama mambobinta.
Yayin da yake magana da ‘yan jarida a Gusau, El-Rufai, wanda yanzu shi ne Mataimakin Jagoran Jam’iyyar na a Arewa Maso Yamma, ya ce ADC ta mayar da hankali kan haɗin kai, da bai wa matasa damar shiga siyasa.
Ya ƙara da cewa an warware rikicin shugabanci da ya faru a Zamfara, kuma tsarin jam’iyyar a jihar yanzu ya zama mai haɗin kai.
El-Rufai ya gode wa mambobin jam’iyyar bisa kyakkyawar tarba, sannan ya roƙi ‘yan Nijeriya, musamman magoya bayan ADC, su yi rijistar zaɓe don ƙarfafa dimokuraɗiyya.














