Allah Ya yi wa tsohon ministan kwadago, Alhaji Musa Gwadabe rasuwa.
Gwadabe ya kasance dan jam’iyyar PDP na farko kuma tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano.
- Sudan: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kwaso ‘Yan Nijeriya Ta Masar
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 29 A Kauyen Abuja
Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jajanta rasuwar tsohon ministan, inda ya bayyana rashinsa a matsayin abin bakin ciki da ba za a iya maye gurbinsa ba.
Talla
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya bayyana Gwadabe a matsayin adalin dan siyasa wanda ya tsaya tsayin daka kan manufofinsa.
Gwadabe ya rasu ne da safiyar ranar Laraba bayan ya sha fama da jinya a wani asibiti a Kano.
Ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya 11 da jikoki.
Talla