Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Tandja Mamadou Ya Rasu

Daga Rabiu Ali Indabawa

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou ya rasu bayan da ya yi fama da rashin lafiya. Tanja ya rasu ne da yammacin Talata a Niamey babban birnin kasar. Wata sanarwar daga fadar shugaban kasar Nijar ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar.  Sanarwar ta ce za a yi zaman makoki na kwana uku a duk fadin kasar.

Tarihin Rayuwar Tandja

An haifi Tandja ne a 1938 a Maine Soroa a yankin Tafkin Chadi a kudu maso gabashin Nijar. Ya yi aikin soja, inda har ya kai mukamin kanar. A 1974 ya kasannce ya na da hannu a juyin mulkin da aka yi wa shugaban kasar na wancan lokaci Hamani Diori.

Tandja ya taba zama jakadan Nijar a Najeriya na tsawon shekara biyu

Ya kuma ta ba zama ministan cikin gida na Nijar a 1990. Bayan ya yi ritaya daga aikin soja, ya yi yunkuri har sau biyu na zama shugaban kasar a shekarun 1990 amma bai yi nasara ba. Ya ci gaba da yin adawa da gwamnati inda har aka taba kama shi, kafin daga baya ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasar.

Rayuwarsa a Siyasa

Tandja ya zama shugaban kasar Nijar ne bayan ya lashe zaben 1999, inda ya sha alwashin dawowar zaman lafiya na siyasa a zaman wata hanyar sake gina tattalin arzikin kasar. An kuma sake zaben shi a karo na biyu a 2004. A 2005, babbar jam’iyyar adawa a kasar ta yi wa Tandja kakkausar suka kan yadda ya tafiyar da matsalar yunwa lokacin da kasar ta yi fama da fari da kuma annobar fari wadanda suka lalata amfanin gona.

A 2009 lokacin da wa’adi na biyu na gwamnatinsa ya kare, Tandja ya shirya zaben raba gaddama na neman kara wani wa’adin mulki, yana mai cewa ‘yan kasar suna son ya ci gaba da mulki don tafiyar da aikace-aikacen samar da sinadarin uranium da kuma man fetur da kasar ta gano.

A Nijer din dai, Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wani taron hadin gwiwa da kungiyoyin kasa da kasa a Jamhuriyyar Nijar da suka hada da kunigiyoyin EU, ECOWAS da CENSAD da nufin jan hankulan bangarorin siyasar kasar kan batun zaman lafiya game da tsare tsaren zabukan watan Disamba mai zuwa.

Sanin rikicin da ke tattare da sha’anin zabe a kasashen Afrika, inda a sau tari ‘yar karamar magana ke rikidewa ta zama tashin hankali, ya sa Majalisar Dinkin Duniya da wasu manyan kungiyoyin kasa da kasa suka shirya babban taron, domin tunatar da ‘yan siyasar kasar muhimmancin zaman lafiya a daidai wannan lokaci da kasar ke tunkarar babban zabe.

Manzo na musamman na a Majalisar Dinkin Duniya a yankin Afrika ta yamma Dr. Mohammad Ibn Chambas ya ce, babban nauyi ne, kuma ya rataye a wuyan ‘yan siyasa domin dorewar yanayin zaman lafiya. Ya kuma ce akwai a mayar da hankali wajen darajanta juna da musayar yawu akan gaskiya, wani abu ne da zai taimaka a fahimci juna a yayin gudanar da wadanan zabubbuka. Mutunta ka’idodi shi ne kadai hanyar da ta zama dole a bi wajen warware kowane irin rikicin zabe.

Sarakunan gargajiya na da rawar takawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasa, saboda haka aka bukaci gudunmuwarsu don ganin an cimma burin da aka sa gaba a karkashin wannan taro. Sarkin Tsibirin Dogon Doutsi mai martaba Samna Boubacar Marafa ya yaba da wannan tsari.

Wasu daga cikin ‘yan takara sun amsa wannan gayyata ta MDD da nufin jaddada goyon baya ga wannan yunkuri. Dr. Souleyman Abdallah, dan takarar jam’iyar NIGERINA, ya ce, sun gamsu da irin wannan taron, kuma suna fatan za a yi zaben lafiya. Kungiyoyin mata sun sha alwashin ci gaba da ba da shawarwarin da aka tsayar a wannan taro zuwa sassan kasa ta yadda za a kare matasa daga bangar siyasa aikin da shugabar kungiyar CONGAFEN Madame Kako Fatima ta ce, yana bukatar samun hadin kan kowa.

A bara Majalisar Dinkin Duniya ta shirya makamancin wannan taro a Najeriya gabanin zabe, domin riga kafin barkewar rigingimu masu nasaba da zabe, haka kuma an yi irin wannan zama a jajibirin zaben Burkina Faso wanda aka yi a ranar lahdi 22 ga watan Nuwamba. Kyakkyawan sakamakon da aka samu a karkashin wannan tsari ya sa MDD shirya irinsa a Nijer, wanda kuma nan ba da jimawa ba ake saran gudanar da makamancinsa a Ghana don ganin zabubukan da wadanan kasashen ke shirin gudanarwa a watan gobe an yi su salum alum.

Exit mobile version