Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, Shafin da ke tabo batutuwa da dama wanda suka shafi al’umma, domin tattaunawa tare da samun mafitar matsalolin da aka tattauna akai.
Tsokacinmu na yau zai yi magana ne akan Maza marasa yi wa matansu kwalliya a gida. Idan ba a manta ba kwanakin baya kadan mun yi magana akan yadda wasu matan ba sa iya yi wa mazajensu kwalliya sai in za su fita, sai dai a yau akalar shafin ya karkata ga bangaren Maza game da wannan batun.
- Ra’ayoyinku A Kan Batun Hako Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe
- ‘Yan Siyasa Da Masu Zabe: Wane Gauta Ne Ba Ja Ba?
A duk lokacin da aka yi maganar kwalliya a cikin gida babu wanda ake ambata sama da Mata, duk da cewa su ma Mazan suna daya daga cikin wadanda za a ambata sai dai mata su aka fi sani da kwalliya kamar yadda ake fada. Da yawan matsaloli na faruwa a fannin zamantakewar aure, wanda idan aka yi duba da bunciken wasu abubuwan sukan shafi wannan babin, domin kuwa kamar yadda Maza ke son Matayensu su yi musu kwalliya, haka su ma Matan ke bukatar Mazajensu da su yi musu kwalliya su zauna muddin kuwa ba fita za su yi ba. Dan na tabbata babu macen da take son ganin mijinta cikin kazanta, ko kuma zama da jallabiyya ba tare da kaya masu kyau ba.
Wannan matsalar a bayyane take domin kuwa ko wadda ba ta yi aure ba ta san da hakan, tunda ta kan shiga wasu gidajen na unguwa ko gidan kawa ko ‘yan uwa ko makamancin haka, in ba ta gani a wani gidan ba za ta gani a wani gidan, ta yadda duk zuwa sai ta ci karo da hakan. Ba kowanne namiji ne baya yi wa matarsa kwalliya a gida ba, akwai ‘yan wanka wadanda su daman gayun kwalliyar ya samo asali ne tun daga kuruciya, ko samartaka, ko kuma ta dalilin matar, idan ta zamo ‘Yar Kwalliya ce. Duk da cewa wasu Mazan sukan zubar da gayun kuruciya bayan an yi aure a ganinsu an riga da an saba an zama daya, sai dai kasancewarsa namiji ya na jin kansa shi ne me gida da ci gaba da yi wa sauran ‘Yan Mata na waje kwalliya su kalla, ita kuwa matar gida an gama yayin yi mata nata Kwalliyar, daman cen yana yi ne dan gudun ka da wani ya fi shi a wajen neman aurenta.
Akwai Maza masu zama da kaya guda muddin suna cikin gida dan inda sabo ta riga da ta saba gani, musamman jallabiyya da mafi yawan mutane sun fi sanin wasu mazan da ita a cikin gidajensu. wata ma idan ta so canja mijin dan koya masa yin kwalliya da dabarun kalamai da dabarun labarai sai ya nuna mata cewa shi fa ba kazami bane, domin kuwa zai yi wankan ba wai ba zai ba. Wani tun bayan da aka gama amarcewa yake maida kansa me kaya guda wanda muddin ba fita zai ba su zai saka.
Da yawan mata na mamakin da rashin gane dalilin da yasa wasu Mazan ba sa iya yi wa matansu kwalliya idan har babu in da za su je, ko dan gudun ka da kayan su lalace ne?, Ko kuma kada gugar da ke jiki ta ware ne?, ko kuma saka kayan ba tare da ‘yan mata sun kalla ba asara ce a wajensu?, ko kuma sabida matar ba ta yi ne ya sa shi ma ba ya yi?, ko kuwa wata ka’ida ce da duk wanda yayi aure aka bashi damar yin hakan matan ba su sani ba? Tun da kuwa wasu Mazan kayan a goge suke a ajjiye sakawar ce kawai sai in za a fita, tamkar masu tattala kayan kar guga ta ware, ko ma dai mene amsar tana ga masu yin hakan. Akwai batutuwa da dama game da wannan matsalar, wanda wajen yayi kadan a fade su, domin za mu ji ta bakin mabiya wannan shafin game da na su ra’ayin akan wannan batun. Ko me yake kawo hakan?, Wanne irin matsaloli hakan ke haifarwa?, ta wacce hanya za a magance matsalar? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Amina Umar Sa’id daga Jihar Kano:
Tabbas! hakan na faruwa, Abin da yake kawo hakan rashin sanin mahimmancin soyayya ne daga bangaren Mazan sai ka ga namiji a gida ya zauna tun safe da Jallabiyya bai yi kwalliya ba, amma in zai fita sai ya sha kwalliya ya fuce, Gaskiya irin wannan dabi’a tana kashe soyayya a tsakanin ma’aurata. Maza dai su dinga yi wa matayensu kwalliya a gidan ba sai za su fita ba. kuma suma Matan su dinga yi wa mazajensu kwalliya suna kashe dauri. Shawara dai ita ce; a dinga kulawa da darajar aure sosai kuma a dinga yi wa juna kwalliya da bada kulawa a tsakani.
Safiyanu Auwal Garba daga Jihar Kano:
Tabbas! akwai Mazan da ba sa yi wa matansu kwaliya. Aman mafi yawanci daga matan ne saboda idai ita za ta iya yi masa ko da yaushe shi ma zai ji kishin yayi, sai dai idan daman baya yi ne gaba daya. Gaskiya idan aka sami namiji mara tsafta wanda ko kafin lokacin idan ka ga yayi kwaliya toh! zance zai je, kun ga kuwa idan ya samu yayi aure idan matar ba mai kulawa bace tabbas! hakan zai kasance yana zama. Matsala ta farko dai duk ranar da yayi kwaliya zai kasance a cikin zargi ne zai je wajan wata ne kuma ba ma a gun mutar ba har wajen abokai ma. Mata su dinga yawan yin kwaliya lokacen dawowar mazajinsu.
Rabiatu Ahmad Mua’zu (Rubby) daga Jos Jihar Filato:
Kwalliya dai tana daga cikin abin da yake kara dankon soyayya, muddin kina ganin abokin rayuwar ki cikin kwalliya a ko da yaushe wani shaukin farin ciki da jin dadi ne yake mamaye zuciyar mace, a duk lokacin da ta bude ido ta yi tozali da mijinta ya tsala kwaliya, ba wai don zai fita wani waje ba a’a ya zauna kawai a gida su yi hira sai kuga nishadi da farin ciki bayyane a fuskar ta, yana faruwa sossai ka ga wasu mazan ko in ce maza da yawa basa kwalliya sai idan za su fita, wasu mazan sun saba da hakan ne, wasu kuma ra’ayinsu ne hakan, wasu kuma rashin yaba kwalliyar ta su ne daga wajan matansu, shiyasa suka fi yin kwalliyar yayin da za su fita. Hakan yana iya haifar da matsalolin cikin gida ta yadda za ka sa matar ka ta dinga ganin wasu mazan a waje suna burge ta saboda kwalliyar da suke yi, sai ka ga wata wannan kwalliyar ta su ya fara tasiri matuka a zuciyar ta tunda kai da kake tare da ita baka yi mata, balle ta gani ta ji dad’i a ranta, kullum idan ka yi kwalliya to fa ba nata ba ne na ‘yan waje ne. Hanyar da za a magance kuwa shi ne; ya zama kana ware lokuta da za ka yi kwalliya ta musamman ka zauna a cikin gidanka kai kanka za ka yi farin ciki, domin kuwa za ka ji ka wani daban a wanan lokacin, ya zamana a domin matar ka hakan zai faranta mata rai sossai. Duk namijin da ya san baya yi wa matar shi kwalliya ya daure ya fara, domin kuwa yana tasiri sosai a zuciyar mace, ka sanya farin ciki a zuciyar matar ka, ta hanyar yi mata kwalliyar ko shigar da ka san tana matukar so, sai ku kara farin ciki a cikin rayuwar auren ku.
Masa’ud Saleh Dokadawa:
Gaskiya ne yana faruwa, yawancin maza suna fita da safe ba sa dawowa sai yamma ko dare daga wuraren neman abincinsu ko ‘office’. Ba kowanne namiji ne ma ya san cewa yi wa matarsa kwalliya a cikin gida ibada bane. Wasu mazan suna la’akari da matansu suma ba sa kwalliya sai za su je unguwa. Karancin lokacin zaman gidan ga maza na jawo hakan, musamman ma ‘yan kasuwa, masu aikin karfi da kananan sana’o’i, don su ba su da hutun karshen mako. Rashin jindadin zaman gidan na jawo haka, saboda ba su sami farin ciki da kwanciyar hankali ba, ina maganar kwalliya. Talauci da rashin wadata, yana hana yin kwalliya don abincin da za su ci ma baya samuwa, don haka ba ta kwalliya suke ba. Yana haddasa rashin jin dadin zamantakewar aure, musamman ma masu kudi, Yana rage samun ladan zamantakewa, Yana jawo wa Matan su ma su daina yin kwalliya sai za su fita. Farko wayarwa gami da ilimantar da ma’auratan akan yin tsafta da kwalliya a cikin gida ibada be. Matan su nunawa mazan cewa suna son yi masu kwalliya duk ranar da ba za su fita ba, Yawaita Ado da Kwalliya ga matan a lokacin da mazan suke gida, zai sa mazan suma su yi wa matan. Su ji tsoron Allah su daina son sabawa zaman takewar aure ne. Kwaliyya tsafta ce, kuma ita ce; cikon addini. In ba su daina ba hakan zai iya jawo tabbatuwar kazanta a gidansu.
Hafast Yusuf Muhammad daga Jihar Kano Karamar hukumar Gwale, Unguwar Gadon Kaya:
Abin da za a cewa mazan da ba sa yi wa matansu kwalliya a gida sai dai Allah ya shirye su ya kuma ganar dasu, kuma gaskiya ne hakan yana faruwa sosai fatanmu kuma Allah ya sa su gyara hakan ameen. Abin da yake jawo hakan wani tun farko kazami ne tun daga gidansu dama sai zai fita ake yin wanka, toh! yayi aure bai fasa ba ita kuma matarsa sai ta gyrashi yana wanka ta zabo masa kayan da take so a ranta, ta fesa masa turare ta karya masa hula a gaban goshi wallahi sai ya saba. Yana jawo matsaloli masu tarin yawa tunda idan ya fita ‘Yan mata suna ganinsa ya sha wanka za a yi ta rububunsa, amma a gidan kazami ne sai dai ya yi ta yawo da jallabiyya a gidan, dole ya samu matsaloli a gidansa. Hanyar da za a magance matsalar guda daya ce addu’a, kuma matarsa kar ta gaji ta dinga nuna masa yau da gobe zai gyara in sha Allah. Ita kuma kar ta fasa Allah zai ba ta lada. Shawarar da zan bawa mazajen da suke irin wannan dan Allah su daina kazanta idan ka yi wa matar ka ba wani abu bane baka fadi ba, kai ma Allah zai baka lada sabida ta ji dadi, kuma duk yana cikin shakuwar aure fa.
Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Hakan na faruwa sosai kuwa, yawancin maza ba su cika zama da kwalliya a cikin gida ba. Wasu idan ka ga sun sa manyan kaya an karya hula to fita ce za a yi, da an dawo gidan kuma wanka za a yi asa kananan kaya. Ga masu tsaftar kenan, wani namijin kuma tsaftar ce gaba daya babu ko a wajen ma yana buga tsami. Amman shi yana son matar shi tai mishi kwalliya har ka ji suna korafi akan hakan, duk gayun namiji sai dai ka ga suna kankankan da matar shi da wuya ka ga matar da mijin ta ya fita kwalliya ana samun hakan kadan, amman duk matar da ta bari mijinta ya fita kwalliya ta zama ziro (0) domin ita mace ‘yar kwalliya ce. Abin da ke jawo hakan anan gurin kuma akwai laifin mace, dan ita ya kamata ta rinka nuna masa abin da take so tun farkon aurensu ba sai lokacin da abun ya zamar masa jiki ba, a tunani na idan mace tana nuna ba ta son irin shigar da ya ke mata a gida tun farko auren nasu zai saba da wadda ta ke so. Nayi la’akari da matan da suke auren kazamin namiji kuma ka ga cikin kankanin lokaci sun gyara shi yayi fes da shi. Sai dai kuma akwai maza masu taurin kai, dole babu yadda matan za su iya da su, sai dai ayi ta samun matsala na rashin zaman lafiya, dan dole sai macen ta rinka jin haushin mijin a kasan zuciyar ta. Dan yadda kake son ka ga ta kashe daurn dankwali ita ma haka take son taga kayi gayu. Idan ba ta kashe dauri ba za ka kalli wata waje ka ga ta burge ka to ita ma macen fa ba makauniya ba ce. Shawara ta ga maza anan su daure su dinga yi wa matansu kwalliya a cikin gida da fesa turare na ta na musamman ko dan kishin iyalinsu. Allah ya sa mu da ce.
Hamidan Badamasi Rijiyar Lemo (Kano):
Babu shakka mafiya yawan mazaje ba sa yi wa matansu kwalliya wanda har hakan ya zama al’ada ga wasunsu duk lokacin da ka ga sun yi kwalli babu shakka za su fita ne, iyaka abin da za mu gaya musu shi ne; a duk lokacin da suka ga matansu sun canza daga halin tsafta zuwa halin kazanta kar su zargi kowa su ne matsalar domin mata suna son ayi musu ado kamar yadda muke so su yi mana. Mafi yawan abin da ke sanya wadansu rashin kwalliya wa matansu shi ne; sun dauka zaman gida kamar Islamiyya ce kullum Uniform 1 ake bukata, wasu kuma suna ganin kamar bata lokaci ne, har za ka ji wasu na cewa “kwalliyar me zan yi tunda an zama daya”, ai mata sune ‘yan kwalliya, Babu shakka rashin kwalliya wa matar ka yanada matukar matsala wadda idan ba Allah ya kiyaye ba idan ka samu mace mai masifar kaunar kwalliya ga namiji tana iya jarabtuwa da son wani a waje, wanda hakan na iya bayuwa zuwa ga fara samun sabani ko kuma ita macen ta fara cin amanar mijinta, domin kwalliya na da matukar tasiri wajen janyo hankali ko sha’awa. A iya tunanina hanyar magance wannan matsala tana hannun matan ne wadanda mazajen nasu basa yi musu kwalliya, abin da ya kamata shi ne; duk macen da ta tsinci kanta a irin wannan hali, lallai tayi amfani da hanyoyin masu kyau cikin hikima domin wajen tilastawa me gidan nata, idan kina son gyara mijinki ya zamana kullum idan ya dawo daga kasuwa ya zamana ace kin kai masa ruwa bandaki, sai ki yi amfani da dabaru masu tausasa zuciya, a haka a haka za ki ga ya koma dan gaye a gidan. Shawarata su ji tsoran Allah su sani mata suna bukatar irin abin da muke bukatuwa gare su, duk abin da kake ganin idan mace tayi aibi ne ka sani kai ma hakan yake gare ka, kuma ai za ka zama cikakken maigida ne idan iyalinka na samun farin ciki da kai, ya kamata ka gyara.
Zahra’u Abubakar (Dr. Zara) Karamar hukumar Nassarawa Gama-D Jihar Kano:
Eh! gaskiya hakan yana faruwa mafi yawancin maza ba sa yi wa matansu kawlliya sai in za su fita aiki ko majalisa ko wani uzurin duwa unguwa, nasu dai na kansu hakan na faruwa sosai gaskiya. A nawa tunanin gaskiya abin da ke kawo hakan baya wuce yadda su mazan suke gani kamar ai ba komai bane ko kuma ba dole bane su yi wa matar su ko iyalinsu kawlliya ba, nafi yawansu a lokutan zance ne kafin aure suke wa ‘yan matansu kwalliya Amma da zaren an yi auren to shikenan in ka ga wani namijin yayi kwalliya to daman dayan biyu ne ko dai zai je zance ko zai je unguwa. A gaskiya hakan zai iya haifar da matsaloli, musanman idan abokiyar zaman nasa mebson kwalliyar ce, hakan zai rinka bata mata rai da kuma jefa ta a cikin wani hali na bacin rai, a duk sanda kuma ta ga mijin wata fes! fes!! da shi dole za ta ji ranta ya baci ta ji haushin yadda nata baya kwalliya. Hanyar da za abi a magance matsalar shi ne; su mazan su rinka kwalliya, sannan kuma su daina ji a ransu kamar yi wa matar ka ta gida ta sunna kwalliya bata lokaci ne ko kuma ai ba dole bane ko kuma in nayi ina zan je?, so in suka cire wannan daga ransu suna kwalliyar suma sai sun fi jin dadin jikinsu, ai tsabta na da dadi ko don jin dadin jiki, kuma da kare hakkin abokin rayuwa ko ba ka da ra’a yi sai kayi, domin tana kalla ta san dan ita kayi kuma za ta ji dadi sosai. Kamar yadda na fada a baya shawarar da zan ba wa masu kin yi wa matansu kwalliya don Allah su tunkude wannan a gefe su sani kwalliya ba karamin fito wa da mutum kimar sa take ba ga ladan yi wa iyali kwalliya ga shi kasa su a Nishadi ga tsabta kamar yadda na ji hausawa na cewa “suttura ita ce mutum to haka ma kwalliyar za ka zauna tas! tas babu datti sai farin ciki da godiya ga Allah.