Wannan makon mun kawo ra’ayoyin masu bibiyar mu a kan kaddamar da fara hakar Man Fetur a yankin jihohin Bauchi da Gombe da Shugaba Buhari ya yi. Ko wannan zai taimaka wajen tsamo al’ummar yankin daga kangin talauci?
Sani Ladan
Masha Allah, wannan babban lamari ne kullum addu’ar mu Allah ya azurta yankin nan namu na arewa da dukiyar da ake mana takama da ita, muna farin ciki kuma muna baiwa shugabanin mu na arewa su dage su sa ido, lallai kada wani abu ya kawo cikas a kan wannan muhimmin aiki, koda Buhari yana jan kafa to ya dace su fizgeshi a guje don ya kammala aikin kafin wa’adinsa na sauka. Allah ya bamu sa a ya taimake mu, mun gode.
Comr Hassan S Umar
Alhamdulillahi, daga karamar Hukumar Minjibir. Wannan batu na hako man fetur a yankin Arewa. Mun dade muna dakon ranar domin idan baki, Mantaba tun kusan lokacin Gwamnatin Dr. Goodluck E Jonathan ake ikirarin gano rijiyoyin Man Fetur musammnan a Jihar Borno, a matsayinmu na yan gwagwarmaya da eman kawo cigaban al’umma, muna murna kuma tunda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara ikirarin Man Fetur din musamman jihohin Bauchi da Gombe muke cike da fatan samun haka domin rikicin da ke faruwa a kudu maso gabas din kasarnan. Babbar silarsa shi ne ‘Crude Oil Resources’.
Wanda batu ne me matukar fadi da ba zan iya tafashi awannan shafin ba.
Amma nasan akwai abubuwa a takaice kamar haka
-Tashe Tashen Hankula
-Samun aikin yi
-Makarkashiyar EU
Babu lokacin yin bkyani filla-filla amma abinda ba lallai kinsani ba akwai yankuna da suke da Man Fetur a kasa kamar Kano, Zamfara, Borno, Gombe da Bauchi, akwai sharshi da yawa gaskiya amma a takaice
Wannan ba karamar nasara bace, Allah ya tabbatar.
Amb Ibrahim Adam Dan-Sarauta
Idan har da gaske ne abin zai yi wu to lallai an dauko hanya ta kusa da ke shirin kawo ci gaba a Jihohin Bauchi da Gombe da ma Arewa baki daya.
Irin wannan ayyyukan na gayaran ma’adanan tattalin arizikin Arewa ba tun yanzu ya kamata a ce ana yi ba, domin su ne za su samar da habakar tattalin arzikin na Arewa da kuma magance zaman kashe wando da wasu daga cikin matasan mu suke fama da shi sannan kuma ina mai tabbatar miki da cewa za a rage harkokin ta’addanci.
Domin kashi casa’in na ‘dan ta’adda da suka addabi Arewacin kasar nan talauci ne ya ke jefa su.
Allah ya sa mu dace ya kuma ba da ikon aiwatarwa amin.
Sulaiman Muhammad
Gaskiya na yi farin ciki sosai da jin wannan labarin domin zai haifar da cigaba sosai ta fannoni da dama
Kabo Idris Saminu
Gaskiya indan da gaske wannan aikin zai tabbata ina sa rai da cewa taulaci da ake fama dashi zai ragu matuka da gaske domin za a samu ayyukan yi, babu zaman banza ya kare.
Wannan ra’ayi nane nagode da daukar sako na. Bissalam.
Zainab Danyaya
Toh Alhamdulillah Allah ya sa ya zame mana alkhairi
Baban Khairat
Wannan labari abin farin ciki ne ga al’umma yankin Arewa, amma inda gizo ke saka shi ne a cikin watanni nawa ne aikin zai kammalu? Ki duba aikin hanyar Abuja zuwa Kano har yanzu ba a gama ba, Allah ya bada Ikon yi abinda ya dace fatanmu kenan,
Yusuf Muhammad Jalingo
Muna matukar farin ciki da wannan yunkuri na shugaban kasa shi dai ya yi nashi saura kuma sanatoci da wanda abin ya shafa su cigaba da bibiyar abubuwan kamar yadda ‘yan kudu suke yi kuma kada susa son zuciya wajen kula da kuma yin aikin. Muna fatan Allah ya sa ya amfani Arewa dama Nijeriya baki daya.