• Leadership Hausa
Tuesday, February 7, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Rahotonni

Batun Kare Martabar Kyawawan Al’adun Hausawa

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
in Rahotonni
0
Batun Kare Martabar Kyawawan Al’adun Hausawa

Fili na musamman domin makaranta, wanda zai rika ba wa kowa damar tofa albarkacin bakinsa kan abin da ya dame shi cikin zuciya, na rayywar yau da kullum, ko makamancin haka.

Filin namu na yau yana tafe da bayanin Abba Abubakar Yakubu, dangane da abin da ya dame shi cikin zuciya. Inda ya fara da cewa:

  • Ra’ayoyinku A Kan Batun Hako Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe
  • Yadda Za A Kula Da Tafin Kafa Lokacin Hunturu

“Al’adun da kuke kyama, yanzu sun zama abin kwalliyar ku, saura ku karbi addininmu!”. Wadannan wasu kalamai ne na izgili da wani wanda ba musulmi ba ya rubuta a kasan jikin wani hoton wasu ma’aurata sabbin aure, wato Ango da Amarya, wanda aka dauka lokacin wani shagalin bikin aure.

Yanayin hoton ya nuna Angon cikin shigar kananan kaya ya sa kwat da wando da madaurin wuya, yayin da ita kuma Amaryar ta sanya farar rigar leshi da siffar dinkin Amaren turawa, kai ka ce dai bikin na wadanda ba musulmi ba ne.

Ba su kadai ba, hatta ga sauran abokai da kawayen Amarya ma duk irin wannan shiga ta kananan kaya suka yi, wasu ma kansu babu kallabi. Sai dai mai yiwuwa ka yi mamakin jin cewa, wannan Amarya da Ango ‘Ya’yan Musulmi ne, kuma ma cikakkun Hausawa ne, Amina da Bashir.

Labarai Masu Nasaba

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (II)

Ko da yake da gani ka san biki ne na wasu ‘ya’yan masu hannu da shuni, ‘yan siyasa ko wasu hamshakan ‘yan boko, saboda irin yadda aka kawata wajen bikin da kuma irin manyan mawakan da aka gayyata daga kudancin kasar nan.

Ba ina nufin yin irin wannan shigar ta sabawa koyarwar addini ba ne, wannan hakkin malamai ne su inganta ko su tsawatar a kai, amma ni abin da ya fi daukar hankalina shi ne; kayan da suka sa sun sabawa bikin aure na al’adar Bahaushe. Idan mun lura, saboda sabawar ce ma har wani yake ganin, saura kiris a ajiye addinin ma a gefe.

Na fara rubutu na da wannan salo ne domin nuna mana irin lalacewar da al’adun Malam Bahaushe suka samu kansu a ciki, musamman a bangaren bikin aure, kuma abin takaici masu fada a ji daga cikin al’ummar Arewa na daga wadanda ke kara angiza irin wannan lalacewar tarbiyya da al’ada.

Abin takaici ne yau ka je wajen bikin ‘ya’yan manyan kasar nan ka ga irin bidi’o’in da aka shirya da abubuwan da ake gudanarwa da sunan biki, wadanda ko kusa ba su yi kama da na Hausawa ba, kuma ma ba su dace da koyarwar addini ba.

Idan mai karatu ya lura da kalaman da na rubuta a farkon wannan sharhin na san zai yi tunanin lallai sauran abokan zaman mu su kansu suna mamakin yadda garin kwaikwayonsu da muke yi har mun kusa wuce makadi da rawa.

Kalaman da aka yi amfani da su a farkon wannan rubutu ba kirkira ba ne, tabbas! haka wani ya rubuta a shafin Instagram na wasu masu biki da suka sa hotunan auren su.

Ashe kenan idan har wadanda ba Hausawa ba za su rika mamakin yadda rayuwar mu ta canza, muka manta da namu kyawawan al’adun muka koma kwaikwayon wasu, za mu yi takaici da cizon yatsa kan wasu abubuwan da ke faruwa a rayuwar akasarin Hausawa ko ‘yan Arewa, ba kawai a sha’anin biki ba, har ma da sauran harkokin mu na rayuwa.

Matasa da iyayensu sun rungumi wasu halaye da suka saba da asalin tarbiyya, yakana, kunya da mutunta kai da aka san Hausawa da su.

Haka mutum zai yi ta ganin wasu abubuwan takaici da ke faruwa, tsakanin masu shirin aure, wanda ake kira hotunan kafin biki (Pre-Wedding Pictures), wani salon daukar hoto na ‘yan zamani.

Yadda za ka ga masoyan ko masu shirin auren na rungumar junansu, sumbatar juna da wasu sassan jikinsu, za ka rantse ma’aurata ne, sun yi aure tuni, ba wai shirin auren suke yi ba. To, in ma auren suka yi, haka addinin Musulunci da al’adar mu ta koyar a rika yi, don bayyana soyayya da burge mutane?.

Wasa a hankali muna kara yin baya baya da tarbiyyar mu ta addini da wanda iyaye da magabatan mu na kwarai suka dora mu a kai.

Muna rungumar wasu al’adu da ba su dace ba, kuma wata rana za mu ji kunyar a danganta mu da su, musamman idan yaran mu suka taso suka ga abubuwan da muka aikata a lokacin kuruciyar mu. Wanne abin koyi muke bar musu? Wacce rayuwa muke fatan su yi nan gaba, a matsayin su na manyan gobe?

Daga Abba Abubakar Yakubu.

Tags: Al'adun HausawaAureBiki
Previous Post

Tsokaci A Kan Mazan Da Ba Su Yi Wa Matansu Kwalliya A Gida

Next Post

An Rantsar Da Ademola Adeleke A Matsayin Gwamnan Osun Na 6

Related

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri
Rahotonni

Dalilan Da Ke Hana Kwamfuta Da Wayoyin Hannu Sauri

2 days ago
’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (II)
Manyan Labarai

’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (II)

1 week ago
GORON JUMA’A
Rahotonni

GORON JUMA’A

2 weeks ago
Ra’ayoyinku A Kan Wa’adin CBN Na Dakatar Da Karbar Tsofaffin Takardun Naira
Rahotonni

Ra’ayoyinku A Kan Wa’adin CBN Na Dakatar Da Karbar Tsofaffin Takardun Naira

2 weeks ago
Bukatar Daukar Mataki Kan Kisan Da ‘Yansanda Ke Wa Fararen Hula
Rahotonni

Bukatar Daukar Mataki Kan Kisan Da ‘Yansanda Ke Wa Fararen Hula

3 weeks ago
Tabarbarewar Aikin Gwamnati A Matakin Jihohi
Rahotonni

Tabarbarewar Aikin Gwamnati A Matakin Jihohi

3 weeks ago
Next Post
An Rantsar Da Ademola Adeleke A Matsayin Gwamnan Osun Na 6

An Rantsar Da Ademola Adeleke A Matsayin Gwamnan Osun Na 6

LABARAI MASU NASABA

Karancin Mai: Kungiyoyin Sufuri Za Su Yi Zanga-Zanga A Hedikwatar NNPC 

Karancin Mai: Kungiyoyin Sufuri Za Su Yi Zanga-Zanga A Hedikwatar NNPC 

February 7, 2023
Yadda Aka Yi Wa ‘Yan Nijeriya 16 Kisan Gilla A Burkina Faso

Yadda Aka Yi Wa ‘Yan Nijeriya 16 Kisan Gilla A Burkina Faso

February 7, 2023
Tinubu Ya Bai Wa Iyalan Wadanda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Kyautar 100m A Katsina

Tinubu Ya Bai Wa Iyalan Wadanda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Kyautar 100m A Katsina

February 7, 2023
Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Shugaban EFCC A Gidan Yarin Kuje 

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Shugaban EFCC A Gidan Yarin Kuje 

February 7, 2023
Hadin Gwiwar BRICS Ya Nuna Halin Ci Gaba Mai Kyau

Hadin Gwiwar BRICS Ya Nuna Halin Ci Gaba Mai Kyau

February 7, 2023
Kotu Ta Yanke Wa Wani Tsoho Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Har Abada Kan Laifin Fyade A Jigawa

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da CBN Da Buhari Ƙara Wa’adin Maye Tsoffin Kuɗi

February 6, 2023
EFCC Ta Cafke Manajan Banki Kan Daukar Sabbin Kudi Da Bayar Da Su A Abuja

EFCC Ta Cafke Manajan Banki Kan Daukar Sabbin Kudi Da Bayar Da Su A Abuja

February 6, 2023
An Samar Da Damar Dawo Da Zirga-zirga A Dukkan Fannoni A Tsakanin Hong Kong Da Babban Yankin Kasar Sin

An Samar Da Damar Dawo Da Zirga-zirga A Dukkan Fannoni A Tsakanin Hong Kong Da Babban Yankin Kasar Sin

February 6, 2023
Shugaban Kasar Sin Ya Mika Sakon Jaje Ga Takwarorinsa Na Turkiyya Da Syria Bisa Ibtila’in Girgizar Kasa Da Ya Shafi Sassan Kasashen Biyu

Shugaban Kasar Sin Ya Mika Sakon Jaje Ga Takwarorinsa Na Turkiyya Da Syria Bisa Ibtila’in Girgizar Kasa Da Ya Shafi Sassan Kasashen Biyu

February 6, 2023
Tawagogin Sinawa Masu Yawon Shakatawa Sun Sake Fara Ziyara A Ketare

Tawagogin Sinawa Masu Yawon Shakatawa Sun Sake Fara Ziyara A Ketare

February 6, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.