Assalamu wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Masu karatu da ke biye da mu, a makon da ya gabata mun kawo darasi na biyu a kan tsantseni da gudun duniya na Manzon Allah (SAW), to har yau dai za mu dan karasa bayani kadan kafin mu shiga sabon darasinmu na yau.
Sayyada A’isha ta ce, na kasance ina yi wa Annabi (SAW) kuka don jinkai game da halin da nake ganin shi amma haka ya so, wani lokacin har sai na shafa cikinsa sabida halin da cikin ya shiga na daga yunwa, sai na fada masa, raina fansa a gareka, me ya sa ko abin da za ka ci ba za ka tambaya ba? Tun da ba ka son me yawa. Sai Annabi (SAW) ya ce min, ya ke A’isha! Wai meye ya hada ni da Duniya ne? Abin da nake tsoro, ‘yan’uwana, Annabawa Ulul’azmi (Annabi Nuhu, Ibrahim, Musa da Isa), ma’abota kokari, sun yi juriya a bisa abin da ya fi wannan halin da nake ciki na tsanani kuma suka shude a kan haka, suka tafi wurin Ubangijinsu a haka, Allah ya girmama makomarsu, so kike in je in sami Ubangijina ina jin kunya ban yi komai ba? Sabida ni kawai dangata ne?
- Tsantseni Da Gudun Duniya Na Annabi S.A.W (2)
- Tausayi Da Kyawon Cika Alkawarin Annabi Muhammadu (SAW) II
Sabida haka, Shehu Tijjani Abul Abbas (RA) ya ce, ibadar ‘yan Darikarsa, godiya ce ga Allah. Misalin yadda abun yake shi ne, tafiyar Hajji daga Nijeriya a zamanin baya – kusan shekaru 10 ake shafewa a hanya kafin a karasa Makkah, amma yanzu a irin wannan zamani – cikin wasu ‘yan sa’o’i kawai mahajjata suke tashi daga Nijeriya su isa Makkah. Idan dai a je a yi aikin Hajji a ziyarci Annabi (SAW) shi ne Hajji, to, har yanzun ana aikin hajji amma in wahalar da ake yi ne aikin hajji, to, yanzun ba a aikin hajji.
Annabi (SAW) ya ci gaba da bai wa Sayyada A’isha amsa, yana mai cewa, kina so ne gobe ranar Alkiyama Allah ya takaita min mukamina da cewa, ba zan iya zuwa wurin ma’abota himma ba, ni kuma babu wani abu da na fi so sama da in je in hadu da ‘yan’uwana ma’abota himma a lahira. Sayyada A’isha ta ce, bayan wannan hirar da muka yi da shi Annabi (SAW) bai wuce wata daya ya kara a duniya ba ya rasu.
Wannan sabon Babin zai yi tsokaci ne kan Tsoron Allah da Ibadar Annabi (SAW) ga Ubangijinsa.
Tsoron Allah da biyayyar Annabi (SAW) ga Ubangijinsa, gwargwadon saninsa ne ga Ubangijinsa.
Masanin Allah (Arifi) yayin da ya kara nisa wurin sanin Allah, lokacin ya ke kara tsoron Allah, sabida ya san babu sai Allah, shi ne mai komai da komai, to, ta ina babu za ta yi girman kai? Da samuwar halitta da komai nata, Annabi (SAW) ya ce mafarki ne da fadinsa cikin wani Hadisi “Mutane duk a cikin barci suke, yayin da suka mutu, lokacin suka farka”. Don haka, wanda ya fi sanin Allah, ya fi kowa tsoron Allah. Wanda ya san Allah, yana bauta masa ne don kunya da soyayya ba sabida tsoron wuta ba, don haka, ibadar Arifi da wanda ba Arifi ba, ba su zama daya ba.
Sabida haka, duk ibadar da Annabi (SAW) yake yi, godiya ce ba don tsoron wuta ba, ya yi bauta tun lokacin babu wutar, babu sama, babu komai sai Zatin Allah. A lokacin sunansa Ahmadu (Mafi godiya) kafin ya zama Muhammadu (shayabon halitta).
Shehu Ibrahim Inyas yana cewa, “Annabi (SAW), Manzo ne tun kafin Allah ya halicci wani abu, kuma ya kadaita Ubangijinsa, sai Zatin Allah ta yi masa Salati don biyan bashi”.
Bambancin aikin Arifi da Mahjubi shi ne, Arifi aikin godiya yake yi, Mahjubi aikin lada yake yi. Misalin haka, wani mahaifi ya siyo abinci buhu-buhu aka kawo gidansa aka ajiye a kofar gida, sai ya kira makwabta ya ce su kai masa gida zai biya su lada, amma kuma dan mahaifin yana wurin, sai shi ma ya fara kwasan kaya zuwa cikin gida sabida na mahaifinshi ne, in an zo ana biyan lada, dan maigida ba zai zo ba sabida shi dan gida ne, ya yi aiki ne don godiya. Kuma duk in ka gode wa Allah, zai kara maka, “La’in shakartum la’azidannakum”. Yayin da Arifi ya yi fana’i sannan kuma ya dawo ya yi Baka’i, sai Allah ya yi ta kara masa Ma’arifa.
A takaice dai, Ibadar Annabi (SAW) gwargwadon saninsa da Ubangijinsa ce, don haka, babu wanda ya isa ya yi kafada da Annabi (SAW) wajen sanin Ubangijinsa.
An karbo Hadisi daga Abi Hurairah ya kasance yana ce wa, “Annabi (SAW) ya ce, da kun san abin da na sani, da kun yi dariya kadan kun yi kuka da yawa”
A wata ruwaya kuma, daga Abi Zarril gifari, ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Ni fa ina ganin abin da ba ku gani, ina jin abin da ba ku ji, sama tana kugi, kuma ya cancanta ta yi, sabida babu wurin ajiye yatsu hudu a sama face akwai wani Mala’ika ya ajiye goshinsa a wurin yana wa Allah Sujjada. Annabi (SAW) ya yi rantsuwa, wallahi da kun san abin da na sani da kun yi dariya kadan kun yi kuka da yawa, kuma da ba ku iya kwana da matayenku ba a kan shimfida, da kuma kun fita daga gidaddajinku zuwa saman dutsuna kuna kankan da kai ga Ubangiji”
An karba Hadisi daga Mugira ya ce, “Annabi (SAW) ya yi Sallah wata rana har kafafuwansa suka kumbura” a wata ruwaya kuma “Annabi (SAW) ya kasance yana sallah har kafafuwansa su kumbura” wata kila sai aka ce masa, yanzu za ka dora wa kanka wannan ga shi an gafarta maka abin da ya gabata na daga zunubanka da wanda ya jinkirta, sai Annabi (SAW) ya ce “To kuma ba zan zama Bawa mai godiya ba?”
An karba wani Hadisi makamancin haka daga Abi Salamata da Abi Hurairah, Sayyada A’isha ta ce, aikin Manzon Allah (SAW) ya kasance dauwamawa, waye a cikinku zai iya? Duk abin da ya dauka yana yi, zai ci gaba da yin abin har mutuwa. Duk ranar Alhamis sai Annabi (SAW) ya ziyarci Masallaci da mutanen Kuba, sabida a nan ya fara sauka da ya yi Hijira zuwa Madina.
Sayyada A’isha ta ce, da yawan lokuta Annabi (SAW) yakan yi Azumi har sai mun ce, shi ke nan ba zai kara cin abinci ba, wani lokacin kuma zai sha ruwa har sai mun ce, wata kila ya daina yin Azumi (duka ana maganar Nafila ba farilla ba).
An karbo irin wannan Hadisin daga Ummu Salamah da Abdullahi bin Abbas da Anas, ya ce “ko waye kai, ba ka taba nufin ka je ka ga Annabi (SAW) yana Sallah ba face ka gan shi yana Sallah, haka kuma, in kai nufin ka gan shi yana barci, za ka je ka gan shi yana barci”.
Ausu dan Malik ya ce, wani dare na kasance tare da Annabi (SAW), sai ya farka ya yi Asiwaki sannan ya yi Arwala ya fara Sallah, nima sai na zabura na yi Arwala na bishi, sai ya fara da Suratul Bakara kuma baya shige wata ayar Rahama sai ya tsaya ya roki Ubangiji tabaraka wata’ala in kuma ayar Azaba ce sai ya tsaya ya nemi tsarin Ubangiji har sai da ya kai karshen Surar sannan ya yi Ruku’u. Gwargwadon nisan tsayuwar da ya yi, irin shi ya sake yi a Ruku’un, sannan ya karanta zikri a ruku’un yana ce wa “Subhana zil jabaruti wal malakuti wal kibriya’u wal azamati – tsarki ya tabbata ga ma’abocin rinjaye mai dimbin yawa, tsarki ya tabbata ga mai iko kuma mai jin Mulki da girma” sannan ya yi sujada sai ya taso kuma ya sake karanta Suratu Ali Imrana gabadayanta a raka’a ta biyu, sannan ya dinga karanta sura bayan sura.