Connect with us

LABARAI

Tsugunne Ba Ta Kare Ba: Sabuwar Kungiya Ta Bullo A Jam’iyyar APC

Published

on

•Sun Jaddada Goyon Bayansu Ga Kwamitin Gwamna Buni

A kokarin sake fasalin jam’iyyar APC ta hanyar kokarin da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a karkashin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, wata sabiwar kungiya ta amintattu mai suna Integrity Group, wacce ta kunshi wasu amintattun ‘ya’yan jam’iyyar da su ke a kwamitin zartaswan jam’iyyar sun bayyana a cikin jam’iyyar. 

Kungiyar wanda su ka bullo daga cikin kwamitin da ban a zartaswan jam’iyyar ba har sun nada shugabanninsu, sun kuma aike da takardar sanarwar na su ga kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar wanda ya ke a karkashin Gwamna Mai Mala Buni.

Kungiyar cikin sanarwar na su wacce shugabansu Honorabul Abubakar Sadik Saadu  da sakatarensu Dabid Okumba su ka sanya wa hannu, su ka kuma raba wa manema labarai a Abuja a jiya Litinin, sin bayyana cikakken goyoan bayansu da kuma aniyarsu ta yin biyayya ga kwamitin eukon kwarya na jam’iyyar.

Sun jaddada biyayyarsu ga kwamitin jam’iyyar a inda su ke cewa, “A matsayinmu na ‘yan kwamitin zartaswan jam’iyyar a shirye muke kowane lokaci mu bayar da namu goyon bayan ga kwamitin jam’iyya wanda aka dorawa alhakin gudanar da dukkanin ayyukan jam’iyya a hannunsu.

Sun kuma yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kan rushe kwamitin gudanarwar jam’iyyar da yay I, su ka kuma nuna tabbacin da su ke da shi a kan kwamitin gudanarwan jam’iyyar da aka kafa.

Da su ke yaba cancantar shugaban kwamitin rikon kwaryan, kungiyar sun nuna kasantuwar Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin da cewa abu ne wanda ya dace kwarai da gaske.

Wakilan sabuwar kungiyar sun hada da, Hon. Abubakar Sadik Saadu – Arewa maso Yamma (Shugaba), Dakta Mrs. Racheal Akpabio – Kudu maso Kudu (Mataimakiyar shugaba), Dabid Okumgba – Kudu maso kudu (Sakatare), Abubakar A. Musa – Arewa maso Gabas (Mataimakin Sakatare), Lawal Kolade – Kudu maso Yamma (Ma’aji), Terber Aginde – Arewa ta tsakiya (Mai shirye-shirye), Hon. Muhammed S. Ibrahim – Arewa maso Yamma (Yada labarai) da Barista Tanko Zakari – Arewa ta tsakiya (Lauya). 

Sauran sun hada da, Muhammad Azare – Arewa ,maso Gabas (Jin dadi), Nduka Anyanwu – Kudu maso Gabas (Mai binciken kudi), Bolaji Repete Hafeez – Kudu maso Yamma (Mataimakin sakataren yada labarai), Hon. Ihuoma Onyebuchukwu – Kudu maso Gabas (Mataimakin ma’aji) da Abubakar Ajiya – Arewa maso Gabas (Mai tsare-tsare) sa’ilin kuma da Abdulmunaf Muh’d – Arewa maso Yamma (zai kasance mai tsare-tsare, John Uwaedu – Kudu maso Gabas (Mai Tsare-tsare), Adie Ferdinand Atsu – Kudu Maso Kudu (Tsare-tsare) da Jock Alamba – Arewa ta tsakiya (tsare-tsare)

‘Yan kwamitin amintattu na kungiyar sun hada da, Alhaji Nasiru Danu – Arewa maso Yamma(shugaba), Sunday Jacob – Kudu maso GABAS (Sakatare),Cif Koteteh Ibadan – Kudu maso kudu (wakili), Alhaji Zakari Muhammad – Arewa ta tsakiya (wakili) d Alhaji Shuaibu Abdulrahaman – Arewa maso Gabas (wakili).
Advertisement

labarai