- An Nada Shi Ne Don Huce Takaicin Jonathan
Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, a ranar Talata ya bada dalilinsa da suka sanya shi warware rawanin Malam Muhammadu Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14, ya na mai cewa, da ma tun da fari bai cancanci zama Sarkin Kano ba, illa dai kawai an nada shi ne, don muzguna wa tsohon Shugaban Nijeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan.
Gwamnan ya shaida cewar, ya dauki wannan matakin ne domin ceto bangaren sarautar gargaji daga fada wa cin zarafi da zubar ma ta da kima.
A cewarsa, Sanusi ba shi ne wanda ya fi dacewa da cancantar zama Sarkin ba a lokacin da aka nada shi a watan Yuni na 2014, kawai dai an nada shi kan kujerar Sarkin ne, domin a bata ran tsohon Shugaban Kasar Jonathan bisa matakan da ya dauka a kansa.
Jonathan dai a watan Afrilun 2014 ya tsige Sanusi a matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) bisa ikirarin da tsohon Gwamnan CBN din ya yi na cewa, wasu mutane a karkashin mulkin Jonathan sun sace dala biliyan 49 ($49 billion).
A cewar Ganduje sake bayanin da tsohon gwamnan CBN din ya yi ga jama’a ya sanya cece-kuce da har ya jawo bacin rai a maimakon ya dauki matakai sanar da Jonathan a sirrince, domin ba shi damar bada umarnin gudanar da bincike kan zargin.
Gwamna Ganduje ya shaida cewar wannan dalilin ya sanya Jonathan daukar matakin tsige Sanusi a matsayin Gwamnan CBN duk kuwa da cewa matakin ya jawo ma wasu bakin jini.
“Lokacin da Sanusi ya sake zargin da ke cewa wasu sun sace dala biliyan 49, na ce a raina ina ma da bai yi hakan ba, da ya tattauna batun a sirrince da Jonathan da ya fi fa’ida. Hakan zai ba shi damar gudanar da bincike kan lamarin da gano inda aka boye kudaden.
“Bayanin da shi tsohon Gwamnan CBN ya yi a bainar jama’a na ce bai yi ta yadda ya dace ba, domin hakan ya jawo bakin jini sosai ga wasu.”
A watan Yuni na 2014, kasa da watanni biyu da tsige Sanusi a matsayin Gwamnan CBN, Sanusin ya samu nadin Sarkin Kano, Ganduje ya ce tun da fari ma bai cancanci zama a kan wannan kujerar ba.
Sanusi ya zama Sarki ne a lokacin da gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ke matsayin gwamnan jihar, yayin da shi kuma Ganduje ya ke matsayin mataimakinsa, da ya samu nasarar gadar Kwankwaso a zaben 2015.
Ganduje ya ce, “Tun da farko nadin Sanusi kan Sarkin Kano bai dace ba domin ba shine ya fi cancanta kan kujerar ba, kawai an yi ne domin ramuwa kan abun da Jonathan ya yi masa.
“A lokacin da aka nada shi a matsayin Sarki, jama’a da dama sun yi ta kona tayu a kan hanyoyi su na nuna adawa. Amma da ya ke gwamnati na bayanshi hakan dai aka tabbatar da shi.
“A lokacin da ni na zama gwamna, (shi ya sa za ku yi dariya…) na ce eh lallai maganin Jonathan magani ne mai amfani domin na warkar da marasa lafiya.
“Wannan maganin dai, duk da ya ke ni ba likita ba ne, amma wannan maganin zai yi amfani wajen magance rashin lafiya iri daya, kan cuta iri daya domin baiwa marar lafiya ya sha don samar masa da magani.
“Don haka, na dauki maganin Jonathan wajen ceto tsarin Sarautar gargajiya wajen yin maganar matsalar da ta addabe fannin. Don haka ni da Jonathan muna kan layi daya. A zahirance kuma a gaskiya bana nadamar hakan ba kuma zan yi nadamar hakan ba,” inji gwamnan.