A wanna makon mun kawo muku tattaunawar da wakiliyarmu Bilkisu Tijjani Kassim mta yi wata matashiya mai suna Zainab Alhassan wadda ta rungumi sana’ar dinki. Ta bayyana yadda sana’ar ya rufa mata asiri ta kuma bayyana wasu daga cikin tarihin rayuwarta. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Da farko za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Assalamu alaikum warahmatullah. Da farko sunana Zainab Alhassan an haife ni a Garin Kaduna, na yi makaranta tun daga Firamare har zuwa sikandire duk a Kaduna, bayan na kammala sikandire dina na je na yi TBA dina a De-sass health foundation duk a garin Kaduna, bayan na kammala TBA dina na so na ci gaba da karatuna tun da dama can yana daga cikin burina, to amma Allah bai nufa ba abin bai yiwu ba kin san komai da nufin ubangiji ne.
Shin Zainab matar aure ce?
A a ban yi aure ba tukunna
Ke ‘yar kasuwa ce ko ma’aikaciya?
Ni ‘yar kasuwa ce
Wanne irin kasuwanci kike yi?
Kasuwancina ya hada da sana’ar dinki da nake yi, kawo yanzu dai da su muke ta maneji kafin Allah ya cika min burina na ci gaba da karatuna insha Allah.
To Malama Zainab ya maganar aure fa kina da niyar yi ko kuma karatun kikafi bukata?
Maganar aure insha Allah inda niyar yi idan Allah ya kawo miji nagari.
Me ya ja hankalinki har kika fara sana’ar dinki?
Gaskiya abin da ya ja hankalina har na fara sana’ar dinki shi ne, tunanin in fara kasuwanci shi ne tun tasowata gaskiya ba na son zaman jiran a bani, ba na son bani- bani, shi ya sa na yi runanin ya za ai na inganta rayuwata kafin cikan burina ba sai na yi ta damun iyayena da ‘yan uwana da bani-bani ba.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
Kalubale ai a rayuwa babu yadda za ai ka ga komai ya tafi maka daidai yadda kake so dole wata rana sai Allah ya jarabce ka da wani lamarin daban don haka ai ba a rasa kalubale a rayuwa akwai su kam sai dai mu ce Allah ya shiga lamurammu kawai.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika Samu?
Alhamdulillah nasarori sai dai mu ce Alhamdu lillahi, duk da ba mu kai inda muke fatan mu kai din ba amma a hakan har wasu muke taimakawa kin ga kuwa ai sai dai mu ce Alhamdu lillah kwalliya ta biya kudin sabulu.
A da can da kike karama mene ne burinki?
A lokacin da nake karama babban burina shi ne in zama cikakkiyar likita, to amma kin san kana naka Allah ya riga ya yi nasa, amma a yanzun ma muna kan hanya za mu kai har inda muke son kai wa insha Allah.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Babban abin da ya fi faranta min rai a sana’o’ina shi ne in ka sayi kayana ko in na yi maka aiki ka same shi yadda kake so koma fiye da hakan, gaskiya farin cikin masu sayen kayana yana daga abin da yake saka ni nishadi, a bangaren harkokina aiki da kuma kasuwancina.
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Alhamdu lillah ina tallata kayana a soshiyal midiya kamar su Facebook, Instagram, WhatsApp, talegram da dai sauransu, da kuma a tsakanin mutanena don yanzu kusan mutane da dama sun san me nake saidawa.
Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?
Gaskiya ina so, kuma ina fatan mutanena su rika tunawa da ni wajen gaskiyata da kuma rikon amanata. Ina fata wannan kyakkyawan shaidar ta bini har kabarina.
Ga dinkin da kike ga kuma sana’o’inki shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
Gaskiya komai ina kokarin bashi lokacinsa, duk da wani lokaci dinkina yana kokarin shiga lokacin baccina, ko kuma ki ga kasuwancina din ya nemi ya shigar min lokacin aikin nawa saboda da safe ina chemist sai na tashi nake zuwa sauran harkokina idan na kammala sai na koma gida to fa in na koma gidan sai na hau keke, na kan kai har dare ko asuba ina aiki, wani lokacin ma sai bayan Sallar Asubah nake samun bacci a haka zan dan matse zuwa karfe bakwai na safe, na tashi na yi shirin fita kuma, to kin ji yadda nake tafiyar da al’amuran nawa.
Wacce irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Gaskiya idan na ji ana ce min Allah ya jikan mahaifiyarki ya kai aiki alkhairanki gare ta, Allah kuma yaba ki miji nagari, mijin marainiya, Allah ya raba ki da mahaifinki lafiya to kin ga in aka yi min wadannan addu’o’in gaskiya ina jin dadi mara misali.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Ina samun goyon baya don akwai lokacin da wasu ‘yan matsaloli suka taso min har na ce ni fa na hakura da wannan kasuwanci, amma ‘yan uwana suka rika bani kwarin gwiwa suna kwantar min da hankali dukkan su. Don haka a har kullum nake alfahari da su kuma a har kullum suna kara nusar da ni muhimman cin kasuwanci da kuma aikin suke, da kuma tunatar da ni ci gaba da rikon gaskiya da amana su kan ce min ki riki tsoron Allah a duk inda kike da kuma dukkannin harkokinki.
Kawaye fa?
Ba ni da kawaye.
Me kika fi so cikin kayan sawa, da kayan kwalliya?
Gaskiya ina son a baya kuma bana jin tsadarta ko nawa take. Bangaran kayan kwalliya kuma ina matukar son turare don ni ba ma’abociyar kwalliya bace can-can, na fi ga bangaren kamshi gaskiya, don duk yanayin da za ki same ni bakya rasa kamshi a jikina gaskiya. Turare ko nawa yake bana jin kyashin sayensa.
A karshe, wacce irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Shawaran da zan ba wa ‘yan uwana mata ita ce, kowacce ta tashi ta kama sana’a ko don tsira da mutuncin kanta. Hakika sana’a tana da rufin asiri, ba za a gane hakan ba sai kin fara ki ga yadda za ki rika kashe ma kanki bukata da kuma ‘yan uwanki da abokan arziki a nan ne za ki kara jin dadin kiji ki cikin farin ciki marar misali hakika sana’a tana da dadi. Mu tashi mu kama sana’a.
To mun gode
Ni ma na gode