• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tuntuni Muka Yi Gargaɗin Cewa, Zanga-zanga Za Ta Iya Zama Hargitsi – Minista Idris

by Sulaiman
1 year ago
Zanga-zanga

Tattaunawar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, da gidan talabijin na Aljazeerah a ranar Asabar, 3 ga Agusta, 2024. Ga yadda Tattaunawar ta kasance:

 

Mungode da kasancewar ka tare da mu a yau a cikin shirin Inside Story. Minista Idris, ƙungiyar Amnesty International ta ce, jami’an tsaro sun kashe masu zanga-zangar lumana 13 a faɗin ƙasar nan kuma ta yi Allah-wadai da hakan. Me gwamnati za ta ce a kan hakan?

To, da farko dai gwamnati ta nanata irin wannan tsokaci na cewa, da zarar an bar irin wannan zanga-zangar ta faru, to akwai yiwuwar ta zama tarzoma ko hargitsi. Yawancin mutanen da suka fita kan tituna a safiyar ranar Alhamis sun kasance cikin kwanciyar hankali da sanyin safiyar. Don haka ‘yansanda sun raka waɗannan masu zanga-zangar, tare da tabbatar da cewa, komai ya daidaita, kafin mutane su mayar da lamarin zuwa wata tarzoma, kuma hakan ba abu ne da za a amince da shi ba ne.

Rahoton na Amnesty International bai nuna cewa ‘yansanda ba kawai sun yi ta harbin mutane ba. Masu zanga-zangar sun bi kan tituna inda suka fara ƙona ababen hawa tare da wawushe shaguna. Ba zai yiwu ba jami’an tsaro su zauna su ƙyale waɗannan abubuwa su faru. Don haka, a zahiri zanga-zangar lumana ce ta rikide zuwa hargitsi. Gwamnati da jami’an tsaro suna tabbatar da cewa, komai ya daidaita.

LABARAI MASU NASABA

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan

Amma ku tuna cewa kafin wannan lokacin, a koda yaushe muna gargaɗin cewa, masu zanga-zangar su yi watsi da wannan shiri, domin tarihinmu ya nuna cewa, da zarar an fara fita kan tituna, akwai yiwuwar gungun masu aikata laifuka ko masu aikata miyagun laifuka su bi kan tituna su yi tashin hankali. Mun ga hakan ya faru a kai-a kai a ƙasar nan, shi ya sa muka nace a matsayinmu na gwamnati cewa, ba a buƙatar zanga-zanga.

Kafin wannan rana, za ku tuna cewa sun bayar da kwanaki ko makwanni da yawa kafin wannan ranar ta zo. Muna ta aika saƙon mu: don Allah a watsar da shi, gwamnati na sauraronku. Tuni dai wannan gwamnati ta fara aiwatar da gyare-gyare domin ganin cewa an riga an magance buƙatun da waɗannan masu zanga-zangar suka gabatar. Tattalin arziki ya kasance cikin mummunan yanayi kafin wannan gwamnatin. Ku tuna cewa, kun san babu wani tanadi da aka yi na kasafin kuɗi a watan Yuni na shekarar da ta gabata, lokacin da gwamnati ta zo a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ba a yi kasafin kuɗin ƙarin tallafi ba.

Tun da kana maganar kasafin kuɗi, masu sukar batun cire tallafin man fetur, sun ce, cire shi a lokacin da Shugaba Tinubu ya yi, hakan ya yi wuri da yawa! Sun ce abin ya yi matuƙar rikita tsarin. Me za ka ce ga ‘yan Nijeriya da ke kokawa da matsalar tattalin arziki da ba a taɓa ganin irin sa ba?

 

Mun san cewa za a samu waɗannan wahalhalu kuma za a fuskanci ƙalubale. Ina nufin, halin da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki ya yi muni matuƙa. Ba wai tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare ba ne saboda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki. Bayanan suna nan don kowa ya gani, muna cin bashi ne don ci gaba da ɗaukar nauyin wannan tallafin. Don haka, Shugaban Ƙasa ya ji cewa wannan bai zama dole ba. Ba za mu iya ci gaba da rayuwar ƙarya ba. Ya zama dole Nijeriya ta koma ta sake fasalin yanayin tattalin arzikinta, ta magance matsaloli, kuma wasu daga cikin waɗannan matsalolin na iya zama masu zafi sosai. Kuma wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnati ta zo da matakai da yawa don rage tasirin. Mun san cewa akwai ƙalubale kuma gwamnati ba ta ce ba ta san hakan ba.

Haka kuma an fitar da wasu batutuwa da dama don tabbatar da cewa duk halin da ake ciki ‘yan Nijeriya za su samu sauƙi a matsakaici da kuma dogon zango. Amma a yanzu, kowa ya jajirce domin tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare tsawon shekarun da suka gabata, shekaru da yawa na rashin kula. An yi tsare-tsare waɗanda ba don gyara tattalin arziki ba ne. Don haka yana da muhimmanci kuma ya zama wajibi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar an mayar da waɗannan abubuwa.

Menene matakin damuwa a yanzu a cikin gwamnati cewa wannan zanga-zangar za ta haɓaƙa kuma shin Shugaban Ƙasa zai sallama nan gaba?

To, gwamnati za ta ci gaba da yin duk abin da zai yiwu don tabbatar da cewa ’yan ƙasa sun samu daidai. A ko da yaushe muna cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu mai sauraro ce, ba a taɓa yin irin ta ba, sau da yawa idan ana tsare-tsare, kuma ‘yan Nijeriya ba su ji daɗin hakan ba, ko da yaushe gwamnati tana dawowa ta duba waɗannan tsare-tsaren ta yi gyara. Gwamnati tana nan don kare rayuka da dukiyoyi don tabbatar da cewa an yi gyare-gyaren tattalin arziki.

Batun ma’aikata misali ne mai kyau, inda a watan Oktoban shekarar da ta gabata aka samu kyautar albashi da gwamnati ta bayar ta naira 25,000 lokacin da Ƙungiyar Ƙwadago ta zo ta ce naira 25,000 ta yi kaɗan. Muka yi muhawara da su, kuma a ƙarshe an ba su ƙarin naira 10,000. Dubi kuma abin da ya faru a cikin kwamitin mutum uku da aka kafa don duba sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, ya zo da kuɗi kusan naira 62,000, Shugaban Ƙasa ya nemi shawara sosai, kuma a ƙarshe an samu ƙarin naira 8,000 ya zama naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya tana nan, ba abin da suke so ba ne, amma tabbas su ma sun karɓe shi, muka gama da wannan.

Da farko dai masu wannan zanga-zangar ba su bayyana kan su ba, yawancin abin da muke gani a intanet ne, a shafukan sada zumunta, suna cewa mutane za su yi zanga-zanga, kuma mun damu matuƙa, domin idan ba ku da shugabancin da ya dace, idan ba ku da shugabanni da tun farko za a iya magana da su, shi ya sa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka buƙaci waɗannan shugabannin da su fito, kuma ba shakka wasu daga cikin su sun fito a ƙarshe, amma ba a san galibin shugabannin masu zanga-zangar ba, kuma wannan ita ce damuwar da muke da ita.

Zanga-zanga wani ɓangare ne na dimokiraɗiyya, muna gudanar da tsarin dimokiraɗiyya. Shugaban Ƙasa ya yi imanin cewa ‘yan ƙasa na da ‘yancin yin zanga-zanga a duk lokacin da suka ji cewa tsare-tsare ba su tafiya daidai, amma abin tsoro a ko da yaushe shi ne cewa wannan zanga-zangar na iya komawa tarzoma kuma abin da ya faru kenan, zanga-zangar ta koma tarzoma a sassa da dama na ƙasar nan, kuma wannan ita ce damuwar da muke da ita.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari
Tattaunawa

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

October 17, 2025
Gwamnan Abba Kabir Yusuf tare da Arch. Ali Hassan
Tattaunawa

Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan

June 23, 2025
Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
Tattaunawa

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu

May 24, 2025
Next Post
Hukumar SEMA Ta Jihar Kebbi Ta Tallafa Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwan Sama Ta Shafa A Argungu

Hukumar SEMA Ta Jihar Kebbi Ta Tallafa Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwan Sama Ta Shafa A Argungu

LABARAI MASU NASABA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.