Tsananin matsin rayuwa da jama’a ke ciki ya fara jefa mutane neman tallafi ko ta halin kaka, inda a ‘yan kwanakin nan ake samun turmutsitsi a wuraren rabon tallafin kayan abinci da kudi.
Masana sun misalta lamarin da cewa halin kunci ne da ake ciki ya kai matukar kurewa. Idan za a tuna dai a ranar Juma’ar da ta gabata ne daliban Jami’ar jihar Nasarawa su biyu suka rasa rayukansu a turmutsin neman tallafin kayan abinci da gwamnatin jihar ta shirya raba musu.
- Manyan Daraktocin Kamfanonin Ketare Sun Amince Da Makomar Kasuwar Kasar Sin
- Kungiyar Tsoffin Jami’an NIS Ta Yaba Da Nadin Sabuwar Kwanturola Janar Ta Hukumar
Ganau sun shaida wa wakilinmu cewa wasu mutum sama da goma kuma sun ji raunuka a cikin daliban. Shugaban kungiyar dalibai ta kasa reshen Jihar Nasarawa, Yunusa Baduku, ya nuna takaicinsu kan lamarin tare da cewa dukkanin daliban da suka jikkata an kaisu asibiti.
Gwamnan jihar, Abdullahi Sule ta cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun babban sakataren yada labaransa, Ibrahim Addara, ya nuna matukar damuwa kan lamarin tare da jajanta wa wadanda tsautsayin ya shafa. Ya ba da umarnin a gaggauta kaddamar da bincike domin gano musabbabin turmutsitsin.
Kazalika, kwanaki biyu bayan wannan, sai kuma aka sake tashi da wani mummunan labari na mutuwar mata da yara a wajen amsar kudin Zakkah da wani hamshakin dan kasuwa a jihar Bauchi ya shirya. Turmutsitsin da aka yi ya hallaka mata 8 da jikkata wasu da dama.
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da Gidauniyar Abdulmuminu da ke karkashin jagorancin fitaccen mai sayar da man fetur AYM Shafa ta shirya rabon kudin Zakkah na naira dubu goma ga kowane mutum.
Wurin rabon ya hargitse ne a lokacin da dubban mata suka yi kokarin kutsa kai cikin ofishin attajirin da ke kan hanyar Jos a cikin garin Bauchi. Bayan faruwar lamarin, tawagar gidauniyar ta ziyarci gidajen iyalan wadanda suka rasa rayukansu domin jajanta musu.
Fitaccen malami a Jihar Bauchi, Malam Ibrahim Disina, ya yi magana a madadin tawagar, a gidajen wadanda suka rasa rayukansu, inda ya nuna alhininsu da jimami tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
Tawagar ta bada tallafin Naira 250,000 da kuma kayan abinci ga kowane gidan da aka rasa rai.
Dangane da riga-kafin aukuwar hakan a gaba kuwa, mahaifin wata ‘yar shekara 13, Aisha da ta rasu a turmutsitin, Usman Abdulmumini, ya nemi AYM Shafa da sauran masu biyan Zakkah a irin wannan mawuyacin halin su canza salon tsarin bayar da Zakkarsu.
“Ina addu’a Allah ya yi rahama ga ‘yata da sauran wadanda suka rasu tare. Shi kuma (Shafa) ina mai ba da shawara a matsayinsa na mai arziki da Allah ya taimake shi yake duba talakawa, abun da yake zuciyarsa Allah shi ya sani, a yi kokarin kawo gyara a cikin wannan al’amarin. Hanyoyi na tallafawa suna da yawa za a iya sanya wasu kwamiti wanda a tunani za a iya karbar ko fom a cika a samu wadanda ake bukata a sanya asusun banki da suna, duk lokacin da Allah ya kawo za a yi rabon sai mutum ya ji alert in yana ko tana da rabo.
“Domin sau da yawa ana samun kura-kurai in ka tara mutane ba ka isa ka shawo kansu ba, amma in ka kira za su zo musamman a yanayin da muka samu kanmu na rayuwa in an ce maganar kudi ne ko na abinci to wasu na ba da jininsu da lokacinsu ne. Amma in an ce a zauna a gyara kowa zai samu. Muna bada shawara a gyara muna adduar Allah ya sa wannan abun shi ne na karshe da zai faru.”
Shi kuma wani dattijo Sulaimanu Adamu Duguri wanda ya rasa ‘yarsa Maryam Sulaiman ‘yar shekara 20 a duniya, ya shaida wa tawagar cewa an shirya auren diyarsa bayan sallah da mako biyu sai wannan tsautsayin ya rutsa da ita.
“Komai ya zo daga Allah ne a matsayinka na musulmi komai ya zo ka yi imani da shi don har an sanya ranar aurenta, da za mu yi aurenta kafin wannan azumin amma aka dan samu matsala sai muka daga zuwa bayan sallah da sati biyu. Mijin da zai aurenta ya zo ya yi ta kuka muka ba shi hakuri,” ya shaida.
Kazalika, mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya mika ta’aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu da fatan wadanda suka jikkata za su samu sauki. Kana ya shawarci mai gidauniyar Abdulmuminu da sauran masu gudanar da ayyukan jin-kai da tallafi da cewa ka da wannan lamarin ya sanyaya guiwarsu.
Ya kara da cewa, shi kansa ya kadu inda nan take ya ziyarci wurin da abin ya faru a ranar domin ganin hanyoyin da za a bi wajen kiyaye faruwar hakan a nan gaba.
Wakilinmu ya zanta da wasu masu sharhin lamuran yau da kullum inda suka tofa albarkacin bakinsu.
Daya daga cikinsu, Sulaiman Maijama, ya ce, wannan matsalar na nuna halin matsatsi na rayuwa da al’ummar Nijeriya suka samu kansu a ciki. “Idan ka yi dubi, adadin mutanen da suke bayar da Zakkah ya yi karanci sosai da adadin mutanen da suke bukatar taimako. Yanzu mutum daya ne zai bayar da Zakkah amma a ce mutane dubbai su je su taru masa, kuma hakan ba shi ne ke nuna wai dukka mabukatan ne suka zo ba.
“Wannan yana nuna maka cewa ‘yan Nijeriya suna cikin hali na matsin rayuwa ta yadda har mutum zai shiga halin da zai iya rasa rayuwarsa a kan neman tallafi, mutum fa ya je neman ya rayu ne amma sai ya kare da rasa rayuwarsa.”
Masanin ya ce, abun da ya sanya mata da yara suka fi tururuwa wajen neman tallafi a duk lokacin da aka yi yekuwar wani tallafi, ya ce, matan su ne talauci ya fi shafa, “Wallahi mata da kananan yara suna cikin wani hali. Mazaje abun ya fi karfinsu, labarai da yawa suna fitowa cewa mazaje da yawa suna guduwa su bar iyalansu, wasu mazajen sun mutu sun bar matansu sun zama zaurawa da barinsu da yara marayu.
“Wasu kuma wahalar rayuwa ta musu yawa sun gudu sun bar iyalan. To su kuma mata a yanayinsu na tausayi ba za su iya barin ‘ya’yansu ba. Wasu lokaci fa iyaye mata ba suna kokuwar neman tallafi domin su samar wa kansu ba ne, domin kawai su samar wa ‘yan yara kanana da suke karkashinsu ne. Mata su ne suka fi shiga matsatsin rayuwa.” In ji shi.
Shi ma Alhaji Adamu Sambo, cewa ya yi, da dukkanin masu hannu da shuni za su rika biyan Zakkah da talakawa sun samu waraka, “Wannan lamarin da ke faruwa ni dai yana tada min hankali sosai. Na shiga damuwa da na ga yadda mata suka yi cincirido a ofishin Shafa, yawancin matan nan fa ba kiransu ko gayyatarsu su zo za a ba su Zakkah aka yi ba, wannan ya nuna maka asalin talauci da matsi da mutane ke ciki.
“Kuma abin takaicin fa yawancin matsalar kowa na kokuwar ka da ya rasa ne. Kowa dai neman a ba shi tallafin yake, matsi ya kai matsi matuka. Duk da wannan halin da ake ciki a kasar nan, da a ce masu hannu da shuni za su sauke nauyin Zakka kamar yadda Allah ya umarta da za a samu saukin wasu matsalolin.”