An bukaci sabon babban sakatare na musamman (PPS) da aka rantsar, Farfesa Bello Ayuba, da kuma mai kula da birnin Kaduna (KCT), Samuel Aruwan, da su nuna kwarewarsu akan nadin da aka yi musu don ci gaban jihar Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ne ya bukace su da hakan a lokacin da yake rantsar da manyan jami’an gwamnatin biyu a dakin taro na gidan gwamnati (Sir Kashim Ibrahim House) a ranar Litinin.
Ya kuma bukace su da su yi amfani da sabbin mukamansu wajen fifita bukatun jama’a akan na su, yana mai cewa, wadanda aka nadan sun kasance kwararrun ‘yan jarida ne kafin su kai ga matsayin da suke a yanzu.
Ya ce, “Farfesa Bello Ayuba ya taba zama Shugaban Ofishin Jarida ta ‘Today’s newspaper’ ta Bauchi, Shugaban Kungiyar Marubuta Wasanni ta Nijeriya (SWAN) da sauransu, kafin ya koma bangaren karantarwa a jami’a inda ya bayyana kansa a matsayin kwararre a fannin ilimi da kuma gudanarwa.
“Shi kuma mai kula da babban birnin Kaduna, Samuel Aruwan ya yi aiki da jaridar ‘Daily Independent, LEADERSHIP da Blueprint’ kafin ya shiga aikin gwamnati inda kuma ya rike mukamai daban-daban, ciki har da kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida.”
Da yake zantawa da manema labarai bayan rantsar da shi, Farfesa Bello Ayuba, ya bayyana kudirinsa da himmarsa na yin aiki tukuru domin ci gaban jihar, inda ya ce, ashirye yake da ya taimaka wa shugabanmu, gwamna Uba Sani don samun nasara akan karagar jagorantar jihar Kaduna.
Hakazalika, Samuel Aruwan, shugaban hukumar kula da birnin Kaduna (KCT), ya bayyana kudurinsa na ganin birnin Kaduna ya zama birni mai kyau da zaman rayuwa wanda zai yi gogayya da sauran biranen duniya.
Gwamna Uba Sani ya sake nada Samuel Aruwan kwamishinan kula da ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na wucin gadi kafin a nada sabon kwamishinan ma’aikatar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da jami’an gwamnatin biyu a dakin taro na gidan gwamnati da ke Kaduna a ranar Litinin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp