Shugaban kasar Ukraine Volodomy Zalensky, ya shaida wa shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO cewa kasarsa na bukatar dala biliyan biyar a kowane wata domin yakar dakarun Russia.
A cikin wani jawabi da ya yi ta na’ura a wani muhimin taron da kungiyar ke yi a Spain, Mr. Zelensky ya ce kasar na cikin matukar bukatar makaman yaki.
- Hadin gwiwar yankin gabas da na yamma: Mataki mai kyau wajen raya yankin Xinjiang
- Yadda ‘Yan Filato Ke Rajistar Katin Zabe Duk Da Mamakon Ruwan Sama
“Ukraine na bukatar makamai masu linzami da na’urorin kariya daga hare-hare ta sama na zamani. Kuma duk kuna da su. Idan kuka samar mana da su tun kun karya lagon Rasha na lalata birane Ukraine da firgitar da fararen hularta” .
Ya yi gargadin cewa kutsen na kasar Rasha ba zai tsaya kan Ukraine kadai ba, yana mai bayyana shi a zaman yaki makoma akidar dora duniya kan tafarki daya.
Gabanin jawabin nasa, Shugaba Biden na Amurka, ya sanar da cewa Amurka za ta kara yawan sojojinta a Nahiyar Turai saboda Shugaba Putin ya hargitsa zaman lafiyarta.
Shugaban NATO, Jen Stoltenberg, ya ce a wannan taron ana yi wa kawancen garambawul mafi girma tun bayan kawo karshen yakin cacar baka.