Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Umarnin Hana Sheikh Abduljabbar Wa’azi Ya Fara Aiki A Kano

by Muhammad
February 5, 2021
in LABARAI
4 min read
Sarkin Kano
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

A jiya Alhamis ne aka wayi gari da ganin dandazon jami’an tsaron farin kaya, ‘yan sanda, da jami’an tsaron fararen hula sama da motoci biyar wadanda aka girke su a kofar gidan malamin nan mai wa’azi a Kano Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda ke Unguwar Gwale a birnin Kano.

samndaads

 

Hakan dai manuniya ce kan cika umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na hana shi wa’azi. Sai dai jami’an tsaron da aka ganin, ba sa hana masu zuwa jajantawa shiga gidan malamin. Haka kuma akwai daruruwan magoya bayan malamin a kusa da Masallacinsa lokacin da wakilinmu ya garzaya yankin domin gane wa idonsa abin da ke faruwa.

Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarun Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya yi wa manema labarai bayanin hakan a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar.

Garba ya ce, gwamnatin jihar ta kuma umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan na Kano da sauran hukumomin tsaro su tabbatar da ganin an yi biyayya tare da kiyaye wannan umarni. Ya kara da cewa, an zartar da daukar wannan matakin ne a lokacin zaman majalisar zartarwar na mako-mako da aka saba yi.

Wakazalika, an umarci dukkanin kafafen yada labaru na rediyo da talbijin da ke fadin jihar ta Kano su dakatar da yada duk wani wa’azi na Sheikh Abduljabbar ko wata hudubarsa, ba tare da wani bata lokaci ba.

Kwamishinan ya ce, an dauki wannan matakin ne domin kauce wa barkewar rikici ko karya doka da oda a fadin jihar ta Kano.

A ‘yan kwanakin nan an sha jin Sheikh Abduljabbar na fitar da wasu fatawowi da ake zargin na batanci ne ga Sahabban Annabi (SWA), inda ya cigaba da jaddada matsayarsa kan abin da yake ambatawa, wanda hakan ya sa manyan malamai a Jihar Kano da ma wasu na kasa baki-daya suke ta faman kiraye-kirayen hukumomi su yi gaggawar daukar mataki kan lamarin domin riga-kafin barkewar rikici.

Sai dai kuma, LEADERSHIP A Yau Juma’a ta nakalto shugaban Kungiyar Izalatul Bid’a wa Ikamatis Sunnah mai shalkwata a garin Jos, reshen Jihar Kano, Sheikh Sani Sharif Bichi, ya bayyana cewa kafin daukan wannan matakin akwai abin da ya kamata gwamnatin jihar ta yi.

A nashi hangen, ya bai wa gwamnatin jihar shawarar cewa, kafin a dauki dakatar da  Sheikh Abduljabbar, kamata ya yi a kira shi a zauna da shi da almajiransa da kuma wadanda ya kira da “dakarun Sunnah” a ji ta bakin kowa.

Sheikh Sani Sharif Bichi ya kawo misalin cewa Abduljabbar a ina ya san Anas bin Malik, idan babu shi a ina zai san sunansa?

Malamin na wannan jawabi ne a wurin taron kara wa juna sani da aka gudanar a Masallachin Juma’a na Tal’udu da ke Kano.

Shi kuwa wani mabiyin Sheikh Abduljabbar mai suna Usman Aljabary cewa ya yi rufe Masallachin Abduljabbar tauye hakkin “miliyoyin” mabiyansa ne, yana mai cewa “malaman Tijjaniyya da Salafiyya sun kasa kare Littafan Hadisai na Sahihul Buhari da Sahihu Muslim sai Ganduje?”.

Sai dai kuma, a cikin wani fafaifan bidiyo na Yutube da Sheikh Abduljabbar ya fitar ya hakurkurtar da mago bayansa da suka halarci taron da ya yi a dakin karatun da ke gidansa inda yake shaida wa daliban nasa cewa su yi biyayya ga doka da oda kamar yadda shi ma yake yi.

 

Haka nan an ji yana barazana ga wasu malamai inda yake cewa, “…amma dai ina yi muku rantsuwa da Allah idan Shehi Shehi ko Abdulwahab wani ya yi gangancin turo ‘ya’yan wasu suka hauro mana wannan wurin za mu danne mutum ‘mu yanka’,” in ji shi.

 

Duk kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin Sheikh Abduljabbar abin ya ci tura, kasancewar ya buga lambar wayarsa ta ki shiga, sannan ya aike da sakon kar-ta-kwana shi ma babu amsa ba.

Sai dai kuma, a hirar da jaridar Daily Trust ta yi da Abduljabbar a ranar Laraba, ya bayyana cewa matakin da gwamnatin Kano ta dauka a kansa yana da nasaba da siyasa.

 

Har ila yau, wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin bangaren wasu malamai da Abduljabbar ya fi kalubalanta amma kowa ya tsuke bakinsa kan al’amarin.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taro na musamman da ya kira dukkan bangarori

na malamai da kuma limaman Juma’a, wanda a ka yi a dakin taro na Africa House da

ke gidan Gwamnati, jiya Alhamis.

Ya ce “Da can mu na ta jin abubuwan da a ke fada sai muka ce a kawo mana hujja kan

ya faru.”

Gwamnan ya shawarci limaman Juma’a da cewar ya kamata hudubobinsu na sallar

Juma’ar yau su mayar da hankali kan wannan magana da ake ciki.

“Ya kamata a kara nuna wa al’umma munin wannan babban al’amari. Da kuma neman

karin addu’o’i daga al’umma kan cewa Allah ya sa wadannan matakan da mu ke dauka

su zame mana dalilin tsira gobe kiyama.”

Sa’annan ya kara da cewa zai ci gaba da zama da malaman saboda tuntubarsu kan

yadda abin zai dinga tafiya. Ya kuma kara neman goyon bayan al’umma da ci gaba da

yi wa jihar ta Kano addu’o’i kamar yadda a ka saba yi.

Daga cikin malaman da su ka tofa albarkacin bakinsu, sun hada da dan’uwan

AbdulJabbar na jini, wato Alkali Mustapha Sheikh Nasiru Kabara, wanda ya bayar da

shawarar cewar “Wannan

SendShareTweetShare
Previous Post

Faisal Maina Ya Tsere Zuwa Amurka – EFCC

Next Post

Hadarin Kebance Fulani Da Miyagun Laifuka A Nijeriya -el-Rufa’i  

RelatedPosts

Hadiza Usman

Hadiza Bala Usman Ta Yi Ta’aziya Ga Iyalan Marigayi Dikko Inde

by Sulaiman Ibrahim
1 hour ago
0

Daga Abdullahi Sheme A ranar juma'ar da ta gabatane shugabar...

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

by Sulaiman Ibrahim
1 hour ago
0

Daga Bello Hamza, Abuja Masana da masu ruwa da tsaki...

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

by Muhammad
2 hours ago
0

Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa an ceto...

Next Post
Fulani

Hadarin Kebance Fulani Da Miyagun Laifuka A Nijeriya -el-Rufa’i  

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version