Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa dake buga gasar Firimiya, Unai Emery, ya sake rattaba hannu akan ƙarin kwantiragin shekaru 5 a ƙungiyar.
Unai ya jagoranci Aston Villa inda ta kare a matsayi na hudu akan teburin gasar Firimiya ta ƙasar Ingila kuma ta samu damar buga gasar zakarun nahiyar turai (Champions League) bayan shafe shekaru masu yawa ba tare da samun irin wannan damar ba.
- Wacce Kungiya Ce Za Ta Iya Lashe Gasar Firimiya?
- Arsenal Ta Sake Tabbatar Da Cancantar Lashe Firimiya
Shugaban Aston Villa Nassef Sawiris ya ce; “muna gina wani abu na musamman a nan Aston Villa tare da Unai kuma muna jin dadin sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar har zuwa 2029“.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp