Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Hukumar kula da ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya EU wato UNICEF kan lafiyar mata da ƙananan yara da kuma samar da abinci mai gina jiki, za su fara shirin ba da tallafin kuɗi wa mata masu ɗauke da juna biyu waɗanda suke ziyartar asibitoci akai-aikai a faɗin jihar Bauchi. za kuma a fara gudanar da shirin ne a ƙananan hukumomin Bauchi, Misau da kuma ƙaramar hukumar Katagum.
Hakan na cikin wata darace ta samun ƙaruwar masu halartar asibitoci a kan lokaci domin duba lafiyar junabiyunsu da kuma na ‘ya’yanensu. Batun tallafin wanda ya fito daga bakin shugaban UNICEF.
Kwararre a hukumar UNICEF mai kula da shiyyar Bauchi ta Kudu Dakta Emanuel Emale Idoko shi ne ya bayyana hakan a wata ganawa da al’ummar garin Luda da ke Bauchi.
Hakan ya kuma yi ƙira ga al’ummar garin na Luda da su yi ƙoƙarin amfana da shirin da aka kawo musu domin inganta lafiyarsu a kowani yanayi, ya ce tsarin tallafin zai yi matuƙar taimaka wa iyaye mata.
Mataimakiyar jami’in kula da lafiyan mata da ƙananan yara na hukumar kiwon lafiya daga matakin farko na jihar Bauchi Hajiya Jamila Muhammad Inuwa ta ce dalilin ganawar nasu shine domin su wayar da kan al’umman yankin a bisa shirin da aka shigo da shi domin neman goyon bayansu “wannan tallafin da ake bayarwa an ba su ne domin ya taimaka musu suna zuwa asibiti domin su ƙarɓi abubuwan da suka dace na kiwon lafiya da ake gabatarwa a asibitoci”. A cewarta
Hajiyan sai yi ƙira ga magidanta da suke barin matayensu domin ziyartar cibiyoyin jinya domin kula da lafiyarsu da na ‘ya’yensu “shi wannan tallafin ya dangancin nayain yauwan zuwan mata asibiti ne. idan ta zo asibiti sau uku ko sau huɗu za a bata naira dubu 4, idan ta zo ta haihuwa a asibiti za a bata tallafi na dubu 2, sannan kuma za a zo a bata tallafi idan ta kawo ɗanta rigakafi sau biyar kowace zuwa tana da dubu ɗaya-ɗaya, baya ga nan idan kuma matan nan ta zo ta amshi katin shaidar haihuwa na ɗantan nan shi ma tana da dubu ɗaya. Idan ka haɗa dukkanin waɗannan kuɗin za ka samu kuɗin ya kai naira dubu goma sha biyu, matuƙar mata ta bi waɗannan hanyoyin za a bata waɗannan kuɗaɗen domin inganta mata rayuwarta da na jaririnta”. A cewarta
A jawabinsa na godiya ɗaya daga cikin manyan ƙasa a garin na Luda Musa Musa Bayero ya ba da tabbacin cewar za su yi aiki wajen faɗakar da matayensu muhimmancin wannan shirin, da kuma faɗa kai daga kuma ya shaida cewar za su taimaka sosai domin shirin ya kai ga nasara.