• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

UNICEF Ta Nemi Dala Miliyan 250 Don Tallafa Wa Yara A Sakkwato, Zamfara Da Katsina

by Hussein Yero
9 months ago
UNICEF

Hukumar UNICEF ta ce tana buƙatar sama da dala miliyan 250 don magance matsalolin da suka addabi yara ƙanana a Jihohin Sakkwato, Zamfara, da Katsina.

Daga cikin adadin, jihohin uku za su ci daga dala miliyan 100 domin samar da abinci mai gina jiki, kiwon lafiya, da ilimi ga yara.

  • Yajin Aikin Likitoci Ya Tsayar Da Al’amura A Asibitocin Abuja
  • Sabon Albishir Ga Masu Kawo Ziyara Ko Yada Zango A Birnin Beijing Na Kasar Sin

Da ta ke magana a taron manema labarai a Gusau, wakiliyar UNICEF, Ms. Cristian Munduate, ta bayyana cewa a Zamfara kawai, yara 400,000 ‘yan ƙasa da shekaru biyar suna fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

Sannan yara sama da 200,000 a yankin Arewa Maso Yamma ke buƙatar shirye-shiryen Abinci Mai Gina Jiki (RUTF) a 2025.

Haka kuma, yara sama da 300,000 a jihohin Sakkwato da Zamfara ke buƙatar rigakafin cutar ƙyanda, sannan mutane miliyan biyu a jihohin biyu suna buƙatar magani da shawarwari kan abinci mai gina jiki.

LABARAI MASU NASABA

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Ms. Cristian ta yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su:

  • Faɗaɗa ayyukan kiwon lafiya da ƙarfafa shirye-shiryen kiwon lafiyar al’umma.
  • Samar da abinci mai gina jiki ga yara masu rauni.
  • Haɓaka ilimi da kayan makaranta.
  • Samar da rigakafin yau da kullun don kare yara daga cututtukan da za a iya hana su.

Ta ce ɗaukar matakin gaggawa yana da muhimmanci don ceto rayuka da gina kyakkyawar makoma ga yara a Zamfara, Sakkwato, Katsina, da sauran yankunan Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
Manyan Labarai

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kai Farmaki, Sun Kashe Ƴan Ta’adda Masu Yawa A Neja

Sojoji Sun Kai Farmaki, Sun Kashe Ƴan Ta'adda Masu Yawa A Neja

LABARAI MASU NASABA

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025
Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

November 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.