Abba Ibrahim Wada" />

United Ta Tuntubi Barcelona A Kan Suares

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tuntubi kungiyar Barcelona akan ko zata siyar mata da dan wasanta na gaba Luiz Suares a kakar wasa mai zuwa kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Suares dai yakoma Barcelona ne daga kungiyar kwallon kafa ta Liberpool shekaru biyar da suka gabata kuma tun bayan komawarsa kungiyar ya taimaka mata wajen lashe kofuna daban daban ciki har da gasar zakarun turai.
Sai dai a wannan kakar dan wasan, dan asalin kasar Uruguay baya kokari yadda yakamata bayan daya zura kwallaye biyu a raga cikin wasanni 10 daya bugawa kungiyar a baya halin dayasa kungiyar tafara tunanin rabuwa dashi.
Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa tuni kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara Magana da Barcelona akan dan wasan wanda take ganin zai taimaka mata wajen ganin ta dawo ganiyarta ta baya.
Barcelona dai tuni tafara zawarcin ‘yan wasan gaba a kakar wasa mai zuwa domin maye gurin na Suares wanda ya zura kwallaye da dama a kungiyar kuma ko a watan Janairu sai da kungiyar ta dauki dan wasan gaba, Kebin Prince-Boateng a matsayin aro.
Sai dai watakila shi kuma dan wasa Suares zai iya kin amincewa da komawa Manchester United bayan da a baya ya buga wasa a abokiyar hammayarta wato Liberpool kuma a lokacin da yake Ingila yasamu sabani dayawa da magoya bayan Manchester United.

Exit mobile version