Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Huriyya Dauda Lawal, haɗin gwuiwa da Hukumar Zakka da wakafi, ta biya wa mutane 1,500 da ke tsare a gidan gyara hali da masarautun faɗin jihar saboda bashi.
Babbar Mataimakiya ta musamman ga Uwar gidan gwamnan, Zahara’u Musa ce ta bayyana haka cikin wata takardar da ta fitar, inda ta ce matar gwamnan ta bayar da tallafin kayan abinci da kudi ga marasa galihu don rage raɗaɗin talauci a jihar haɗa kan iyalai da bai wa al’ummar damar dogaro da kai.
Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa kimanin mutane dubu ɗaya ne ke cin gajiyar shirin tallafin basussukan da kayan abinci da kudi ta hannun hukumar zakka ta Zamfara, ƙarƙashin kwamitin mai shari’a Kwanturolan gidajen yari da Malamai, wanda aka dorawa alhakin dai-daita basussuka da kuma taimakawa wajen dinke matsalar ma’aurata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp