Umar Faruk" />

Uwargidan Sanata Aliero Ta Bayar Da Tallafi Ga Mata A Birnin Kebbi

A jiya ne uwargidan Sanata Muhammad Adamu Aliero, Hajiya Maimuna Muhammad Adamu Aliero ta bada tallafi kaya da kuma kudi Naira dubu goma ga mata na mazaba goma shabiyar a karamar hukumar mulki ta Birnin- Kebbi a jiya .

Kayan sun hada da keken dinki, injimin mika da kuma kudi Naira dubu goma ga wasu matan na daya daga cikin mazabun da maigidan da yake wakilta a karamar hukumar mulki ta Birnin Kebbi da ke daya daga cikin kananan hukumomin da yake wakilta a Kebbi ta tsakiya a majalisar dattijai.

An gudanar da bukin rabon kayan tallafin ga na karamar hukumar mulki ta Birnin- Kebbi a harabar gidan shugaban kwamitin dattijai na jam’iyyar APC a jihar Kebbi, Alhaji Sani Hukumar Zauro da ke a cikin GRA Birnin- Kebbi a jiya.

Mazabun da suka ci gajiyar tallafin uwargidan Sanata Muhammad Adamu Aliero sun hada da Marafa, Dangaladima, Nasarawa 1, Nasarawa 2, Kola-Tarasa- Badariya, Makera, Maurida, Gawasu da kuma kardi.

Sauran mazabun Sun hada da Gulumbe, Lagga, Ujariyo, Ambursa, Gwadangaji da kuma Zauro.

Da take jawabinta ga uwargidan Sanatan, Hajiya Maimuna Muhammad Adamu Aliero ta bayyana wa manema labarai cewa ta bayar da tallafin kayan ne ga mata na mazabu goma shabiyar ne domin su samu sana’ar da zasu iya dogaro da Kansu da kuma nuna musu cewa Sanatan kebbi ta tsakiya Muhammad Adamu Aliero zaben sune.

Har ilayau ta ci gaba da cewa kowace mazaba za a ba mata goma shadaya tallafin keken dinki da injimin nika da kuma Naira dubu goma a kashin farko har a tabbatar da cewa kimanin kashi tamanin zuwa dari na matan kananan hukumomi takwas sun samu tallafin Sanata Muhammad Adamu Aliero insha Allahu. Tace wannan tallafin ba karamar hukumar mulki ta Birnin- Kebbi ne kawai aka bada wannan tallafin ba, dukkan kananan hukumomin takwas da Sanata Aliero ke wakilta zasu samu wannan tallafin, inda wasu kananan hukumomin sunriga sun karba, kamar karamar hukumar mulki ta Aliero, Jega, Gwandu da kuma Maiyama sun samu gashi kuma Birnin- Kebbi zata karba a yau.

Bugu da kari tayi kira ga mata na wannan kananan hukumomin takwas da su tabbatar da cewa sun yi amfani da wannan tallafin Sanata Muhammad Adamu ta hanyar da yadace domin samu su dogaro da Kansu. Kazalika ta yi godiya ga matan kananan hukumomin takwas kan irin goyun bayan da suke baiwa maigidanta Sanata Muhammad Adamu Aliero da ke wakiltar su a majalisar dattijai.

Daga nan ta godewa jama’ar jihar Kebbi da kuma ‘yan siyasa kan irin goyun baya da kuma gudunmuwar da suke baiwa maigidan ta Sanata Muhammad Adamu Aliero kan wakilcin da ya keyi ga mutanen jihad ta Kebbi.

Hakazali tayi kira ga al’ummar jihar Kebbi da su ci gaba da bada goyun bayansu ga gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari domin irin kyakyawan shugabancin da su keyiwa al’ummar kasar nan.

Daya daga cikin shugabanin matan mazabun na karamar hukumar mulki ta Birnin- Kebbi wanda ta cigajiyar tallafin Hajiya Hafsat Umar Nasarawa 2 a wata zantawa da tayi da LEADERSHIP A Yau inda ta bayyana irin jindadinsu da kuma godiyarsu Allah da kuma Sanata Muhammad Adamu Aliero da kuma matarsa Hajiya Maimuna Muhammad Adamu Aliero kan irin kulawa da kuma tallafin da ake baiwa Mata a Kebbi ta tsakiya domin da yawan mata a jihar ta Kebbi sun samu abin yi domin dogaro da Kansu kuma dauki nauyin yaransu. Saboda haka amadadin mata “ muna godiya ga Sanata Muhammad Adamu Aliero da kuma gwamnatin APC kan irin tunanin da sukayi na tsayar da Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya”. Shugabar ta ci gaba da cewa Sanatan yana yi musu kyakkyawa wakilci a majalisar dattijai da ke Abuja.

Daga karshe ta yi kira ga ‘ yan uwanta mata da su ci gaba da ba gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu da kuma Sanata Muhammad Adamu Aliero kai har da shugan kasa Muhammadu Bahuri domin kara cin gajiyar damukuradiyya da kuma ci gaban al’ummar jihar Kebbi da kuma kasar Nijeriya baki daya.

Exit mobile version