A yau Laraba, 29 ga watan Janairu, 2025, Æ™asashen Nijar, Mali, da Burkina Faso wa’adin ficewarsu daga Ƙungiyar Raya Tattalin ArziÆ™in Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ya cika.Â
A watan Janairun na bara ne ƙasashen uku suka sanar da aniyarsu na ficewa daga ECOWAS, bayan sun zargi ƙungiyar da yin biyayya ga Faransa.
- Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Mashawarta 11, Ya Horesu Da Aiki Tuƙuru
- Gwamnan Bauchi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta DaÆ™ile Satar Yara A BauchiÂ
Daga bisani, suka kafa sabuwar ƙungiya mai suna Haɗin Kan Ƙasashen Sahel (AES).
A yayin taron shugabannin ECOWAS da ya gudana a Abuja a watan Disamban 2024, Æ™ungiyar ta amince da ficewar Æ™asashen uku, tare da ba su wa’adi domin sake tattaunawa da yiwuwar komawarsu cikin ECOWAS.
Bugu da ƙari, kasashen AES sun sanar da kafa rundunar soji ta haɗin gwiwa mai ɗauke da sojoji 5,000, tare da kayan aikin sama da na ƙasa, domin yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke addabar yankin Sahel.
Duk da ficewarsu daga ECOWAS, Æ™asashen AES sun yanke shawarar cewa ‘yan Æ™asashen ECOWAS za su iya shiga Æ™asashensu, domin Æ™arfafa dangantakar hada-hadar kasuwanci a tsakanin yankin.
Wannan ficewa na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Sahel ke fama da matsalolin tsaro, wanda ya haifar da juyin mulki a ƙasashen uku.
Yanzu haka, suna fatan sabuwar ƙungiyarsu ta AES za ta taimaka wajen magance waɗannan matsaloli da inganta tsaro a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp