Jihar Kaduna, jiha ce mai muhimmanci, wacce ke da mazauni a tsakiyar Nijeriya, kasa ce mai dimbin albarkatu amma a halin yanzu tana cikin tarko da tarin kalubalen shugabanci. Yayin da muka zurfafa bincike, mun ci karo da zaren tashin hankali na rashin tsaro, wasan barkwanci da wasan kwaikwayo na siyasa, abubuwan da ke tattare da ci gaba da nada mukaman siyasa, da gudanar da kasafin kudi da kuma matsalar bashi, haka nan ma ‘yan kasa suna fatan samun ci gaban ilimi, burinsu na kiwon lafiya da habakar noma da kiwo.
Labarin Fadar Gwamnati na Sir Kashim Ibrahim
Kasafin kudin jihar na shekarar 2024 mai taken Canja Karkara don Cigaban Alúmma wanda ya kai Nb458.3 ya kunshi manyan ayuka na kudi Nb318.8, aikace-aikace na yau da kullun na Nb139.4 da niyyar tafiya da kokon bara na karbar bashin Nb150.1 don samun isassun kudade na kasafin kudin.
Ana sa ran sashen ilimi zai samu Nb115.4. Kaduna,wanda aka fi sani da cibiyar ilmantarwa tana da jami’o’i 6 da sauran manyan makarantu, fannin ya ci gaba da zama maras armashi, saboda rashin isassun malamai,ga fama da cunkoson ajujuwa da kuma ajujuwa da babu kowa a wasu yankunan da kuma rashin issasun kayan aiki da rashin yanayi ma kyau.
A matsayin hannun waraka, sashen Lafiya zai karbi NbN71.6. Sashin yana fama da rashin kyawon tsari, rashin isassun kayan aiki, karancin ma’aikata na kiwon lafiya, da karancin kudi, tare da mazauna jihar suna fuskantar cikas na rashin ingantaccen kulawa, asibitoci da dakunan shan magani sau da yawa saboda cunkoson jama’a, na fama da matsananciyar wahala, karancin magunguna masu mahimmanci da kyau. Duk da kokarin inganta harkokin kiwon lafiya ta hanyar tsare-tsare kamar tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kaduna, har yanzu akwai rashin kyawun sakamako a bangaren kiwon lafiya.
Yayin da bangaren noma zai samu Nb22.5 domin shirye-shirye da nufin samar da ingantattun iri da takin zamani, duk da haka, ya gaza wajen samar da wadata ta hanyar daukar wani kaso mai tsoka na al’umma aiki don habaka noma. Fannin ya shiga wani yanayi na lalaci saboda rashin samun dama na dabarun noman zamani, rashin isassun ababen kayan aiki, rashin daidaito da aiwatar da manufofin da ba su dace ba, duk suna iyakance yiwuwar ci gabanta da rage talauci.
Dangane da fuskokin jama’a, Hukumar Kididdiga ta Jihar Kaduna (KDBS) ta kiyasta yawan mutanen jihar a mutane miliyan 10.4 a shekarar 2024. Wannan takobi ne mai kaifi biyu, yayin da yake ba da damammaki biyu, don bunkasa tattalin arziki ta hanyar fadada kasuwanci, a daya bangaren kuwa akwai kalubale domin yana matsa lamba sosai kan kudaden wata-wata na FAAC da jihar ke samu daga Abuja.
Tabarbarewar tsaro sakamakon harin ‘yan fashi da garkuwa da mutane ba wai ya kawo cikas ga harkokin yau da kullum ba har ma ya kawo cikas ga ayyukan ci gaba musamman a yankunan karkara, da noma da kiwo, da kuma ruguza tattalin arzikin kananan hukumomi da jiha.
Wani batu da ke gaban jihar shi ne karuwar basussukan da ya kai makura inda bashin cikin gida ya kai Nb321.54, bashin kasashen waje ya kai Dala miliyan 587.07 da kuma bashin kwangilar da ya kai Nb115 a watan Disamba, 2023 tare da karin Nb2.9 na wutar lantarki da gwamnati ta sha tare da saura offisoshinta a jihar.
Ana sa ran samun kudaden shiga na cikin gida na jihar a shekarar 2024 a kan Nb62 wato Nb5 duk wata.
Tsakanin Janairu zuwa Yulin 2024, rasidin FAAC na Kaduna ya fuskanci hawa da gangara inda jihar ke samun kwatankwacin Nb7 kowane wata. Wannan matakin samun kudin shiga da aka gaya mana, ya shafi tattalin arzikin jihar kai tsaye na biyan albashi, da maganar jin dadin ‘yan kasa, da samar da muhimman ayyuka da kuma biyan bashin da ya rataya a wuyanta.
Dogaro da jiha keyi kan rabon kudi da ga gwamnatin tarayya, da rashin daidaituwar kudaden shiga na IGR na nuna bukatar samun horon dabarun samun kudi da kuma samun wasu hanyoyin kudin shiga, amma ta yaya?
Wasan Barkwancin Siyasa
A nan ya ta’allaka ne da abin da ya daure kai, kwamitin wucin gadi na Majalisar Dokokin Jihar, ya tuhumi tsohon gwamnan jihar da majalisarsa a kan zargin almundahanar kwangila da kudin rance, da almundahanar kudi har naira biliyan 423. A halin da ake ciki kuma tsohon gwamnan ya shigar da kara kotu inda a baya-bayan nan kotun ta ki amincewa da karar da cewa ba ta da hurumin sauraro.
Wani abin da aka sani shi ne cewa kusan kashi 90% na mukarraben wadanda suka yi aiki a karkashin gwamnatin da ta gabata kuma wadanda ake musu zargi har yanzu suna zaune a kan kujerunsu da kuma tasiri da matsayi mai muhimmanci a gwamnati ta yanzu.
Hasashena sune:
• Shin wannan ba son zuciya ba ne?
• Shin wannan ba cinike ne ba tsakanin abokai?
• Shin wannan kawai batun rike hannun kwararru ne, ko kawai rufin asiri na siyasa ne?
A lura cewa damuwarmu a nan ita ce wannan saba wa doka ne da kuma yiwuwar dawwama a kan mulki na son zuciya!
Na Zarin Biliyoyin Daloli da Tambayoyi Masu Neman Amsa
Bari mu dugunzuma cikin biliyoyin daloli.
Netherlands wata kasace a nahiyar turai, tana da fadin kasa mai girman 37,378 Km² an kiyasta ta sami Yuro biliyan 50.4 (daidai da naira triliyan 87.4 a dandalin canji na Webull) daga fitar da kayayyakin noma a shekarar 2023. Jimlar Yuro biliyan 45.7 ya fito ne daga kayayyakin noma da aka samar a Netherlands da kuma Euro biliyan 4.7 wanda ya fito ne daga sake fitar da kayayyakin noma da ake samarwa a wasu wurare. Abubuwan da ake nomawa sun hada da hatsi, amfanin gona na masana’antu, shuke-shuken abinci, dankali, ‘ya’yan itatuwa yayin da a ke fitar da dabbobi da suka hada da shanu, aladu, tumaki, awaki, kaji, madara, da kwai. Akwai kusan kungiyoyin noma masu hannun jari 55,680. Yawancin masu hannun jari suna da shekaru sama da 64. Matsakaicin yanki na noma a kowane hannun jari shi ne kadada 32.8 bisa ga rahoton Statistics Netherlands (CBS).
A halin da ake ciki Jihar Kaduna mai girman kasa 46,053 Km², ta iya samar da Nm1,099,299.44m kawai ne a shekarar 2018 ta fuskar GDP ga bangaren noma bisa ga bayanai daga KDBS yayin da kalubale ne samun bayanai na baya-bayan nan.
SAPZs:
Jihar Kaduna ta samu cin gajiyar Bankin Raya Afirka, wato ta shirin Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZs), na kudi Nm540m da Bankin ya bai wa Nijeriya, inda jihar Kaduna na daga cikin jihohin da suka fara cin gajiyar shirin. Shirin dai shi ne don kawo sauyi a harkar noma ta hanyar samar da shiyyoyin tattalin arziki a yankunan karkara a cikin jihohin da za su amfana ta hanyar bunkasa ababen more rayuwa, da kafa wuraren sarrafa masana’antu na noma guda 15, da cibiyoyi 15 na canjin yanayin noma, da samar da kayayyakin amfanin gona da ma’aikatan aikin gona. Wadanda za su ci gajiyar shirin za su hada da kananan manoma, masu sana’o’in noma masu zaman kansu, dillalan noma, masu sarrafa kayan amfanin gona, da masu aikin noma-preneurs. SAPZs za su kyale kamfanonin abinci da kayan aikin gona su zama kusa da manoma, tallafawa, sarrafawa, rage asarar abinci, da habaka harkan noma (samfurin Netherlands).
Bugu da kari, bankin ci gaban Musulunci (IDB) da asusun bunkasa noma na kasa da kasa, sun bayyana cewa sun ware dalar Amurka biliyan daya (Naira triliyan 1.5) don kara samar da yankunan sarrafa masana’antu aikin gona na musamman (SAPZs) a jihohi 24 na Nijeriya.
NG-CARES:
Hakazalika, jihar kuma tana cin gajiyar asusun NG-CARES (COBID-19 Action Recobery Economic Stimulus) tare da dimbin adadin dalar amurka miliyan 20 (biliyan NGN31) kason farko da na biyu, ana hasashen shigowar su cikin jihar. Wannan kudi, jihar za ta yi amfani da shi don inganta rayuwar ‘yan jihar a muhimman fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, tsaro, da ababen more rayuwa. Haka nan, don samar da wadatar abinci, da tallafa wa kananan masana’antu.
Akwai tambayoyi a nan, ta yaya Kaduna ta yi amfani da wannan dama ta biyu na rayuwa?
1. Ina wadannan makudan kudade?
2. Mene ne tasirin wadannan kudade a rayuwar ‘yan jihar?
3 Shin akwai wani bambanci a zahiri a fannin noma ko magance kalubalen ci gaban jihar?
4. Ina SAPZ na Jihar Kaduna suke?
5. Shin SAPZs na Jihar Kaduna sun bunkasa ne ko kuma suna cikin wani yani a fadar gwamnatin jihar ta Sir Kashim Ibrahim?
6. Ko an ware kudaden ne don sayen iri, taki, maganin kashe kwari, kayan aikin noma, sannan a baiwa karnukan siyasa damar sayar da su a kasuwannin bayan fage?
7. Shin waanda ke da alhakin gudanar da kuma sarrafa wannan manyan kudade suna sane da kyakkyawar labarin Netherlands da yadda Jihar Kaduna za ta iya kwaikwayon kasar koko sun gwane ne kawai a fagen wasan kwaikwayo na siyasa?
8.Bari mu karkare da labarin tirelolin manyan motoci 20 makare da shinkafa da gwamnatin tarayya ta ba kowace jiha, ina suke?
A Karshe
Kalubalen da jihar Kaduna ke fuskanta, alamu ne na manyan batutuwan da ke tunkarar Nijeriya baki daya. Akwai shakku idan jihar na kokarin tsara hanya da za a fita wannan rudani ko kasancewar samun wani dabarun sarrafa albarkatun kasa da shirin ci gaba mai dorewa.
Saboda haka, abin da ya faru nan gaba zai zama gwaji na gaskiya na shugabanci, iya kawo amfani mai kyau ga mutane da kuma tabbatar da cewa Kaduna ba kawai za ta rayu ba, amma za ta ci gaba cikin nasara a shekaru masu zuwa.
Alhaji Adamu Rabiu (Bakondare) ya rubuto daga Kaduna