Bello Hamza" />

Wadanda Ake Tuhuma Sun Musanta Cewa Melaye Ne Ya Ba Su Bindigogi

Mutane biyun da ake tuhuma wadanda suka tsunduma Dino Melaye, cikin aikata laifukan hadin baki, mallakan bindigogi ba bisa ka’ida ba da kuma sayar da bindigogin, sun musanta zargin hakan da ‘yan sanda suka yi masu.

Mutane biyun, Kabiru Seidu, wanda ake wa lakabi da Osama, da Nuhu Salihu, wanda aka fi da kira da, Small, an gabatar da su ne a gaban wata babban kotun Majistare da ke Lokoja, ranar Litinin, tare da Dino Melaye, wadanda ake tuhuman sun bayyana wa Kotun cewa zargin hakan da ake masu duk karya ne, sannan kuma ko a lokacin da aka dauki bayanansu bayan an kama su sun bayyana cewa, su ba su aikata laifin komai ba.

Laifin da ake zargin sun da shi a cewar mai gabatar da karan, Dakta Aled Izinyon SAN,  ya saba wa sashe na 97 (1) da sashen kundin Penal Code na 27 (1) (a) (1) na mallakan bindiga.

Izinyon, ya shaida wa Kotun cewa, babbar kotun Jiha wacce babban Mai shari’a Nasir Ajanah ke shugabanta ta bayar da belin Sanata Melaye.

Ya ce kuma. Wadanda ake tuhuma na daya da na biyu su kam suna nan a wajen ‘yan sanda ba a bayar da belinsu ba kamar yadda kotun Majaistare din ta bayar da umurni a ranar 3 ga watan Mayu.

A lokacin da aka sake karanta masu abin da ake tuhuman na su da shi, Melaye da sauran mutanan biyu sun musanta zargin da ake yi masu, suka ce duk tuhumomin bakwai karya ne.

Bayan an karanta masu laifin da ake tuhuman na su da shi ne sun kuma karyata, sai Izinyon ya nemi kotun da ta ba shi daman barin kotun domin a koma da su wajen mai gabatar da kara a sake daukan shaidar na su sai a dawo da su don su kare kan na su.

Sai dai, lauyan da ke wakiltan babban Lauyan da ke kare Dino Melaye, Cif Mike Ozekhome,, Yemi Mohammed Esk, ya ki yarda da wannan bukatar, yana mai cewa, wannan fa tuhuma ce ta aikata laifi, wacce tilas ne shaidu su bayar da shaidar su a sarari gaban kotu.

“Hakan yana nufin dakile shari’ar ne da kashi 50, ai shari’a tana da kusurwowi guda uku ne, ‘Mai gabatar da kara, wanda ake zargi, da kuma sa idon al’umma,’ wannan ne ma ya sanya ake yin dukkan shari’u a kotuna a bayyane.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Sulyman Abdullahi, cewa ya yi, zai so dukkanin shari’un da ke kotunsa a yanke cikin hanzari, amma sai ya duba ya ga dokar da kotun ta tanada tukunna.

“In kuwa kotun ba ta ce komai kan hakan ba, zan koma na duba dokar aikata laifuka ta Jihar Kogi.

“Wannan shari’a ce wacce wannan kotun za ta so kowa ya kawo hujjar da yake takama da ita a gaban kotu. Ni ban natsu da barin rantsuwa a madadin shaida ya zo gaban kotu ya bayar da shaida da bakinsa ba.

“Ban yarda da bukatar mai gabatar da kara ba, ina kuma son a yi wannan shari’ar ne ta hanyar da aka saba yin dukkanin shari’u, ina shirye da na fara karban shaidu a rana-rana, in har akwai bukatar hakan,” in ji shi.

Sai ya daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni.

Exit mobile version