Connect with us

FILIN FATAWA

Wadanne Abubuwa Ake So Mace Ta Fi Mijinta Da Su?

Published

on

Assalamu alaikum. Wasu tambayoyi nake rokon Malam da ya taimakamin da amsoshinsu in Allah ya sa malam ya sansu. 1.Shin akwai wasu abubuwa uku da ake so mata tafi mijin da za ta aura da su, sannan shi ma akwai abu guda uku da ake so ya fita da su? Kuma ko akwai wadanda suka yi musharaka a kansu? Da fatan Malam ya san su kuma za a taimaka min da su. Na gode.

To dan’unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku: ta fi shi a kyau, ta fi shi kananan shekaru, ta fi  son shi sama da yadda yake sonta. Ana  so miji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta. Ana so su hadu a abubuwa uku: ya zama akwai yaren da yake hada su, ya zama addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya. Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za’a samu jin dadin aure.

Don neman karin bayani ka nemi shirin da na yi a Freedom Radio kano, ranar : 3 ga Ramadhan 1434 hi, a shirinsu na Minbarin Malamai

Na Sha Nonon Matata, Yaya Auranmu?

Don Allah Malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa, ya aurensu yake?

To dan’uwa Allah Madaukakin Sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila, don haka ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa maganganu guda biyu:

  1. Ya Halatta. saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi S.A.W “Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa”, Bukhari lamba ta : 5102, ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
  2. Bai Halatta ya sha ba. saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi S.A.W ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure .

Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, sai dai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau.

Don neman Karin bayani duba: Bidayatul-mujtahid 2\67. Allah ne mafi sani

Hukuncin Mai Kallon Hotunan Batsa Wai Don Rage Sha’awa

Assalamu alaikum. Malam tambaya ce daga wata baiwar Allah take cewa:- Mun rabu da Mijina, kuma ni na Kasance mace ce mai yawan bukata gashi ba na iya Azumi, ina yawan kallon hotuna na batsa dan ragewa, amma ba na samun nutsuwa, ko da shawarar da za a ba ni kan hakan?. Tambaya ta biyu ita ce: Mace ce a duk lokacin da suke saduwa da mijinta nononta kawai yake sha kuma gashi tana da karamar jinjira wai har ya kan shanye ruwan nonon duka yarinyar ba ta samun nasha, idan har tafiya zai yi yakan so ta tatsi nonon ta bashi ya tafi da shi, to wai dan Allah ya wannan alamarin ya ke a Musulunci, meye kuma matsayin wannan?

Wa alaikumus salam. Kallon hotunan batsa haramun ne. Babu wani dalilin da zai sa ya zama halal gare ki wai don ke kina da tsananin bukatar Jima’i. Allah yana cewa: “Kuma Kace Ma Muminai Mata Su Rintse Idanuwansu (Daga Kallon Dukkan Abinda Bai Halatta Garesu Ba) Kuma Su Kiyaye Farjojinsu (Daga Zina, Madigo, Da Sauransu). Kuma Kar Su Rika Bayyanar Da Adonsu Sai Dai Abinda Ya Fito Fili Daga Cikinta”. Kin ga a cikin wannan ayar Allah ya haramta miki duk irin wadannan miyagun kallace-kallacen, domin yin hakan zai iya kai ki zuwa ga aikata zina. (Allah shi kiyayemu). Maimakon haka gara ki je ki nemi daidaitawa da mijinki, ya mayar da ke a matsayin matarsa. idan kuma hakan ba ta samu ba, ki yi fatan Allah ya fito miki da wani miji nagari.

  1. Miji ya tsotsi nonon matarsa yayin da suke gabatar da sunnah wannan addini bai haramta ba. Sai dai kuma bai kamata shi mijin nata ya mayar da nonon tamkar abincinsa ba. Wannan ya zo da bakon abu wanda zai iya zama cutuwa a gare shi ko ga ita matar tasa ko kuma yarinyar da take shayarwa. Don haka ya kamata ya ji tsoron Allah ya dena ketare iyaka. Mutum ya tsaya inda addininsa ya tsaida shi, kuma ya kyautata dukkan mu’amalarsa ta auratayya. Shan nono wanda ya ke haramta aure shi ne wanda aka yi shi alokacin da mutum yake yaro karami bai isa yaye ba. Kuma sai an sha kamar sau biyar (cikakkun sha tare da koshi). Wallahu A’alam.Advertisement

labarai

%d bloggers like this: