Aminu Ahmad Muhammad Tsagem" />

Wadanne Darussa Mu Ka Koya Daga Azumin Ramadan?

Ramadan

Shika-shikan Musulunci guda biyar ne; na farko (1) shi ne Kadaita Allah daya ne, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) bawansa ne kuma manzonsa ne.  (2) Tsaida sallah. (3) Azumin watan Ramadan. (4) Bada Zakka. (5) Ziyartar Dakin Allah (Hajji) ga wanda ya samu ikon zuwa.

Kasancewar daya daga cikin shika-shikan Musulunci , wato azumi, ya na da matukar amfani da tasiri, wani nau’in ibada ne wanda ya wajabta hana ci, sha da kuma kaucewa iyali tun daga fitowar alfijir har faduwar rana.

Allah ya na cewa a cikin Alkur’ani “Ya ayuhal lazina amanu kutiba alaikum siyam kama kutiba alal lazina min kabliku la’allakum tattakun “(Kur’an 2:183).

Azumi wajibi ne a kan kowane Musulmi, mace da namiji, amma wanda ya balaga, kuma a na azumi ne a watan tara na kalandar Musulunci, watau Ramadan.

Kazalika, fassarar waccan ayar wacce ta wajabta yin azumi ta na cewa, “Ya ku wadanda sukai imani kuma suka bada gaskiya ga Allah an farlanta makui azumi kamar yadda aka farlanta ma  wadanda suka gabace ku ko kun samu tsoron Allah (rabo).”

Azumi a bangaren addinin Musulunci wani nau’in ibada ne mai daraja, wanda ya wajaba a kan dukkan masu hali (wealth) da kuma  marasa shi (non-wealth) ta  fannin yin sa, domin nuna daidaito a wurin Mahaliccin dukkan duniya. Shi watan Azumi wata ne na neman kusanci ga mahalicci ta hanyar yin ayyuka kamar istigfari, salati ga Allah da Manzonsa, yawaita karatun Alkur’ani mai girma da kuma yin tafsirin ayoyin Alkur’ani, domin nusar da Musulmai cewa akwai gobe kiyama, inda za a yiwa dukkanin bayin Allah tambayoyi a kan abinda kowa ya aikata a zamansa na duniya.

Har wayau, abu mafi girma a cikin watan shi ne ciyarwa da shayarwa  a kan mabukata da marasa galihu, wadanda ba su da cin yau balle na gobe (domin an tabbatar duk wanda ya ciyar da mai azumi Allah zai ninka ma sa ladan abinda ya yi ko da barin dabino ne).

A cikin watan Azumi ne a ranar 27 ga watan (yawanci) a ke neman daren Lailatul-Kadri, wato daren da a ke son bawa ya nunka ayyukan ibadarsa, domin samun dace da daren da ya fi wata dubu.

A karshen watan Azumi ne kuma a ke son ba wa ya fidda Zakkatul Fitri. Ita Zakkatul Fitri a na son a bada ta ne a kan nau’o’in abincin da mutane su ka fi ci, kamar  masara, dawa, shinkafa, alkama da sauransu (a yankinmu) ga mabukata  da kuma marasa shi, domin su samu sauki.

Amma a dayan bangaren masu hali su na kiyasta abinda su ka mallaka ne na dukiyoyinsu da a ka yi kasuwanci da su a hada kudaden a raba wa mabukata da marasa galihu a cikin al’ummar.

Wadanne darusa ne mu ka koya daga azumin watan Ramadan? A iya cewa  wadannan su ne darusan da su ka kamata kowa ya dauka daga shi:

– Daidaito tsakanin masu hali da marasa shi a kan ibadar azumi.

– Sanya wa bawa neman kara kusanci da mahalicinsa.

– A na samun raguwar kamuwa da cututtuka a jikin ’yan adam.

– Taimaka wa marasa galihu da mabukata a cikin al’umma.

– Rage radadin talauci a cikin al’umma (raba kayan bukata ga marasa shi).

– Rage aikata manyan laifuka da ayyukan alfasha a cikin al’umma.

– Ya na kara dankon zumunci a cikin al’umma ta haduwa wuraren ibada, kamar masallatai, tafsiri da sallar Tahajjud da ittikafi.

– Zaburar da masu hali da matsakaita masu shi a al’umma su rika tunawa da wadanda ba su da shi, domin neman lada a wurin Mahalicci.

Allah Ubangiji dai ya maimaita ma na Ramadan na badin-badada. Amin.

Aminu Tsagem marubuci ne kuma mamba a kungiyar mawallafa ta kasa, wato ANA, reshen jihar Katsina. Kuma za a iya tuntubar sa a wannan layin 08065032730.

Exit mobile version