• English
  • Business News
Monday, May 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wainar Da Aka Toya A Taron Majalisar Zartarwar Jihar Zamfara Na 18

by Leadership Hausa
1 year ago
in Labarai, Kananan Labarai
0
Wainar Da Aka Toya A Taron Majalisar Zartarwar Jihar Zamfara Na 18
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar yin riƙo da gaskiya da riƙon amana a harkokin gudanar da mulki, inda ya buƙaci ɗaukacin ’yan majalisar zartarwar jihar da su ba da fifiko wajen gudanar da ayyukansu a kan haka.

A ranar Litinin ne gwamnan ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta Jihar, wanda aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Gusau.

  • Tinubu Da IBB Sun Yi Ganawar Sirri A Neja

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa majalisar ta tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi ci gaban jihar kamar samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da kuma tsaro.

A cewar sanarwar, wannan shi ne taron majalisar zartarwa karo na goma sha takwas tun bayan da aka ƙaddamar da “shirin ceto Zamfara.”

Labarai Masu Nasaba

Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano

Cutar Cholera Ta Ɓarke A Filato, Mutane 4 Sun Mutu

Majalisar ta tattauna kan ci gaban da aka samu a fannin samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da tsaro da dai sauransu.

A wajen taron, Gwamna Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ganin jihar ta cimma manufofinta na ci gaban al’umma.

Gwamnan ya ja hankalin ’yan majalisar kan su kasance masu himma da ƙwazo wajen gudanar da ayyukansu.

Bugu da ƙari, an gabatar wa majalisar ta Zamfara da cikakken rahoto kan halin da ake ciki na aikin gyaran sakatariyar jihar da ake yi. Rahoton ya bayar da cikakkun bayanai kan ci gaban da aka samu kawo yanzu, ciki har da kammala aikin gyare-gyare kashi na farko.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AyyukaCi Gabaharkar tsaroMajalisar ZartarwaTaroZamfara
ShareTweetSendShare
Previous Post

EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfara 4 A Borno

Next Post

Boko Haram Ta Sako ‘Yan Gudun Hijira 9 Da Ta Sace A Borno

Related

Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano
Labarai

Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano

49 minutes ago
Cutar Cholera Ta Ɓarke A Filato, Mutane 4 Sun Mutu
Kiwon Lafiya

Cutar Cholera Ta Ɓarke A Filato, Mutane 4 Sun Mutu

1 hour ago
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kwato Makamai A Borno

5 hours ago
Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba
Labarai

Yanzu-yanzu: Matatar Ɗangote Ta Sake Karya Farashin Man Fetur

7 hours ago
 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 
Labarai

 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 

8 hours ago
Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi
Labarai

Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi

9 hours ago
Next Post
Boko Haram Ta Sako ‘Yan Gudun Hijira 9 Da Ta Sace A Borno

Boko Haram Ta Sako 'Yan Gudun Hijira 9 Da Ta Sace A Borno

LABARAI MASU NASABA

Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano

Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano

May 12, 2025
Nazarin CGTN: Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Latin Amurka Na Kara Samun Karbuwa Tsakanin Jama’a

Nazarin CGTN: Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Latin Amurka Na Kara Samun Karbuwa Tsakanin Jama’a

May 12, 2025
Cutar Cholera Ta Ɓarke A Filato, Mutane 4 Sun Mutu

Cutar Cholera Ta Ɓarke A Filato, Mutane 4 Sun Mutu

May 12, 2025
Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

May 12, 2025
NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC

NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC

May 12, 2025
Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Matakan Cimma Nasarar Sassan Tsaron Kasa

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Matakan Cimma Nasarar Sassan Tsaron Kasa

May 12, 2025
Sojoji

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kwato Makamai A Borno

May 12, 2025
Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Yanzu-yanzu: Matatar Ɗangote Ta Sake Karya Farashin Man Fetur

May 12, 2025
 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 

 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 

May 12, 2025
Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi

Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi

May 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.