Yayin da muke kallon katafaren fadin Arewacin Nijeriya, yana da matukar muhimmanci mu zurfafa bincike cikin dimbin tarihi, da al’adun gargajiya, da kuma baiwar, da albarkatun kasar da sashen yake da ita don fahimtar tushen kalubalen da take fuskanta a wannan zamanin.
Yankin dai ya sa mo asali ta hanyar haduwar al’adu, tarihi daban-daban, da suka zama tushen hadin kai, a karkashin jagorancin shugabanni masu hangen nesa wadanda suka yi fata da kuma hasashen makomar wadata da walwalar jama’ar ta a shekarar 1960.
- Majalisar Dattawa Za Ta Kafa Dokar Kare Hakkin ‘Yan Aikatau A Nijeriya
- Nijeriya Ta Ƙaryata Batun Kafa Sansanin Sojin Amurka Da Faransa A Ƙasarta
Taron Gwamnonin Jihohin Arewa 19 da aka kammala a ranar 30 ga Afrilu, 2024 a Kaduna, ya sa masu lura da al’amuran yau da kullum yin la’akari da sabani da kuma waiwayen banbance-banbancen da ake da su a yankin da kuma hakikanin abin da yake faruwa a yayin da ake fama da matsalar rashin iya gudanar da mulki da rashin kulawa a hannun gwamnoninta, wadanda ke kewaye da nadaddun da ba su cancanta ba, inda wasu bisa rashin sanin ciwon kan su ya zuwa yanzu lamarin ya nuna ba su da wani tasiri na zama a kan kujerar mulkin jihohinsu domin kuwa sun dau hanyar yin kaca-kaca da jihohin na su.
Gwamnonin Jihohin Arewa 19, kowannen su an ba shi hakkin tafiyar da al’umma da kuma amana da walwala da tsaron su, sai dai kash! sun bar yankin ya shiga cikin mawuyacin hali na rashin tsaro, garkuwa da mutane, tabarbarewar tattalin arziki,rashin aikin yi, rashin ababen more rayuwa, durkushewar masana’antu da tabarbarewar ilimi da dai sauransu.
Watsi Da Karagar Mai Martaba
Tarihin Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, da Tafawa Balewa, ya bayyana a zahiri, yadda suka kwatanta tsarin shugabanci na sadaukarwa, rashin son kai, da kishin kasa. Jagorancin da suka gudanar a shekarun baya shi ya kafa yankin a kan nagartaccen tubali da kuma wata fitilar ci gaban yankin. Kaico abin bakin ciki hakan bai kasance ba kuma bai kankama ba tukuna.
A yayin da muka mayar da hankali a kan harkar gudanar da mulkin jihohin Arewacin Nijeriya a halin yanzu, wani tsautsayi na ficewa daga wannan kyakkyawan gado da turbar bayyana inda gwamnonin ke ci gaba da kasancewa a cikin rudani a fagen siyasa. Babban abin da suka fi mayar da hankali a kai na ban mamaki shi ne a kan nasarorin da za a samu a zabuka, da kuma cikin rashin kunya, goyon bayan da wani gwamna ke ba wa magabacinsa da ake tuhuma da wawure dukiyar jiharsa inda kuma wasu gwamnonin zargen iyayen gidansu su keyi da cin ammanar jahohin su.
Abu Mai Fa’ída da Riba ga Arewacin Nijeriya
Girma da fadin Jihohin Arewa 19 da suka hada da Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) da ya kai kilomita 662,497 kusan kashi 71.7 na fadin Nijeriya mai girman kilomita 923,768, wannan wani yanki ne mai matukar muhimmanci.
Jihohin Arewa sun shahara wajen noma da kiwo,inda suke iya samar da amfanin gona mai dimbin yawa da suka hada da wadanda za a iya amfani da su don samun tsabar kudi da noman kayan abinci kamar su Citta (Ginger), Gyada, Waken Soya, Ridi (Sesame), Auduga, Wake, Shinkafa, Masara, Dawa, Dankali, Doya Tumatir, Albasa, kiwon dabbobi, da dai sauransu. Lalle, kar kuma mu manta da shahararriyar dalar gyada ta Kano a shekarun baya.
Rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS), mai taken rahoton kasuwancin kasashen waje a watanni uku na farko shekara 2021, da rahoton kungiyar abinci da aikin noma ta duniya (FAO) da Hukumar kula da fitar da Kayayyaki zuwa kasashen waje (Nigerian Edport Promotion Council) sun yi bayanin kan rahotannin da suka fayyace alkalumman da ke da ban sha’awa kamar haka:
Ridi – Nijeriya (Arewa) ita ce ta kasa ta 3 a duniya tare da kiyasin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje na Naira bilyan41.94 kuma fitar da tsaba na ridi da aka kimanta a Naira bikyan 98.27 a shekarar 2020.
Gyada – Nijeriya (Arewa) ita ce kasa ta 3 a duniya da metric ton miliyan 4.49 a shekarar 2020.
Waken Soya – Nijeriya (Arewa) ita ce mafi girma a Afirka wajen fitar da kayayyaki da suka kai Naira TiriliyanN1.72.
Citta – Nijeriya (Arewa) tana da kashi 40% na samar da citta a duniya yayin da jimillar Naira Tiriliyan 5.57 kudin da aka samu daga sayowa da fitarwa a shekarar 2021.
Bugu da kari, Arewacin Nijeriya na da ma’adanai albarkatun kasa kamar su cassiterite, manganese, iron, chromium, nickel, columbite, da zinare.
Sai dai duk da wadannan ababen da za su kawo ci gaba, rashin ingantaccen shugabanci, rashin tsaro, tsadar kayan amfanin gona, rashin wuraren ajiya na zamani wanda ya ta’azzara sakamakon rashin tallafi ga manoma da kuma rashin samar da farashin adalci ga manoma sun taimaka wajen jefa yankin cikin halin kaka-ni-kayi.
Tabbas, akwai rashin basira (The Theory of Comparatibe Adbantage ta bace masu).
Tsabar rashin dabara, rashin hadin kai da kuma rashin mayar da hankali.
Kungiyar Gwamnonin Arewa ko Hukumar kididdiga ta Nijeriya ko Hukumomin Tsaro suna da rashin cikakkun bayanai da za a iya fahimta dangane da rashin tsaro, fashi da makami, garkuwa da mutane, kisa da dai sauransu da suka addabi yankin tsawon shekaru da dama. Amma wani rahoto na baya-bayan nan da Asusun kula da lamuran yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) – mai taken rahoton shekara-shekara na ofishin kasa na shekarar 2021 ga Nijeriya ya ce ‘An kai hare-hare 25 a makarantu,yara 1,440 ne aka sace, kuma an kashe yara 16, wanda ya jawo rufewar makarantu 618 a jihohin Arewa shida’.
Har ila yau, ‘tattalin arzikin Nijeriya ya yi asarar kusan dala bilyan100 a cikin shekaru goma da suka gabata. Bugu da kari,mutane kusan miliyan 2 a halin yanzu suna ci gaba da gudun hijira, inda yara miliyan daya kuma suka rasa zuwa makaranta saboda rikicin Boko Haram da sauran ta’addanci’.
Kafar sadarwar Aljazeera ta ruwaito a watan yuni shekarar 2021 an bayyana cewa ‘Rikicin da aka kwashe shekaru 12 ana yi a Arewa maso gabashin Nijeriya ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 350,000 wadanda mafi yawansu yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar, tare da shelar cewa yara 170 suna mutuwa a kowace rana saboda tashe tashen hankali da tasirinsa ya yi kamari, kamar rashin samun abinci, wuraren kiwon lafiya, matsuguni, da ruwa mai tsafta.’
Hukumar UNDP ita kuma ta yi gargadin cewa idan aka ci gaba da rikici, adadin wadanda za su rasa rayukansu zai iya karuwa zuwa fiye da miliyan daya a shahekar 2030.
Wannan dai lamari ne mai muni kuma tashe-tashen hankulan da ake ci gaba da yi na ci gaba da yin tasiri sosai ga ci gaban yankin da kuma rayuwar al’ummar.
Amma duk da girman wadannan kalubalen, martanin gama gari da kungiyar gwamnonin jihohin Arewa 19 suka yi a wurin taron tattaunawa da suka yi a gidan Sir Kashim Ibrahim, ya yi kama da tsabar rashin sanin gudanar da jagoranci, ba gaggawa ,ba samar da sabbin dabaru da abubuwan da ake bukata don magance sarkakiyar su rikice-rikicen .
Rashin samar da hanyar hadin kai, rashin hadin kai don samar da zaman lafiya da ‘yan’uwantaka a tsakanin ‘yan Arewacin Nijeriya abu ne da ke nuni da cewa, akwai rashin hadin kai a tsakanin gwamnonin kuma shi ke kawo cikas ga kokarin yaki da ‘yan fashi da makami da masu tayar da kayar baya da garkuwa da mutane da kuma jefa rayuwar jama’a cikin hadari da durkusar da kuma lalata tattalin arzikin yankin har ma da lalata tsarin zamantakewar al’umma.
Allah ya jikan su Gamji dan kwarai, yau ga ranar su!
Abin takaici kuma tir
Kamfanin ci gaban Arewacin Nijeriya (NNDC), wanda aka yi hasashen zai zama mai samar da ci gaban yankin, da farfado da tattalin arziki da dora alhakin jagorancin manufofin yankin, ya bayyana yana cikin wani yanayi na rashin kyakkyawan tsare-tsare, ko wata manufa ta hangen nesa mai tafiya tare da ci gaba.
Yayin da gwamnonin suka yanke shawarar yin la’akari da rahoton sake fasalinsa a taronsu na gaba. Wannan ya zama shaida ta rashin hangen nesa da ci gaban yankin, bugu da kari, wannan tafiyar hawainiya ta bambanta da bukatar gaggawar manufofin dabarun da za su iya haifar da sabon zamani na wadata ga yankin Arewacin Nijeriya.
Yawon Shakatawa Zuwa Kasar Amurka
Ziyarar gwamnoni Goma (10) ta baya-bayan nan a Afrilu 2024 don taron tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro, wanda cibiyar zaman lafiya ta Amurka (USIP) ta shirya, wanda niyyar ita ce a matsayin taron tuntuba da kuma habaka hadin kai wajen samar da zaman lafiya, ya zama abin bincike a garemu a nan.
Tafiyar ta kasance karkatacciya kuma watsi ne da damar da aka samu ta samo hanyar dakile ta’addanci da kuma hanyar samo wanzuwar zaman lafiya.Domin sakamakon da muke tsammani na samun mafita na zahiri kuma mai ma’ana bai samu ba. A maimakon haka sakamakon karshe da suka samu shine kawai “Za su yi yunkuri da yin amfani da darussan da suka koyo a jihohinsu”.
Ya kamata wannan tafiya ta kasance ta zama taro ne har da kafar tsaron gida ta Amurka wato (Home Land Security) don koyo dabaru da kuma aiwatar da mafi kyawun ayyukan dakile ta’addancin a cikin jihohin Arewacin Nijeriya.
Makomar yankin kasar da ake kira Abuja
Menene matsayin Abuja ga kungiyar gwamnonin 19 na Arewacin Nijeriya, bisa la’akari da tarihi, al’adun kasa da sauransu? Ko an yada ita ta zama agola ne? Ya kamata a ba ta matsayin ‘Kujerar masu sa Ido’ wato (Obserber Status) a cikin wannan Dandalin Arewacin Nijeriya mai gwamnoni 19.