Masu iya magana suka ce waiwaye adon tafiya. Duba da iftila’in gobarar da ya sake samun babbar kasuwar Litinin (Monday market) ta birnin Maiduguri ya sa naga dacewar yin waiwaye izuwa shekaru 44 baya domin sake kawo wa masu karatu wani rohoto da Marigayi Ado Saleh Kankiya ya hada na bude babbar kasuwar Litinin din da aka yi a shekarar 1983 bayan ta kone a shekarar 1979 an sake gina ta.
Wannan rohoton an buga shi a jaridar ‘GASKIYA TA FI KWABO’ a ranar Alhamis 11 ga watan Augusta a shekarar 1983 (har yanzu ina da jaridar). Ga yadda rohoton ya kasance kamar haka:
A RANAR Alhamis, 4/8/83, Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Mohammed Goni ya yi bikin bude sabuwar babbar kasuwar Maiduguri wadda aka gina a kan #13 miliyan da sabuwar tashar Telebijin ta Jihar.
Da yake jawabi wajen bude babbar kasuwar, Gwamnan ya yi gargadi ga ‘yan kasuwar da za a rabawa runfunan da su tabbatar da cewar suna biyan kudaden runfunan cikin lokaci.
Alhaji Mohammed Goni ya yi nuni da cewar, muddin dai ana so kasuwar ta zauna da gindinta ta yadda za ta rinka biyan bukatun kanta na yau da kullum har kuma ta yi tanadin wani abu don gobe, to kuwa ya zama wajibi ne ‘yan kasuwa su shiga kasuwar su tabbatar da cewar suna biyan kudaden hayan runfunar su a kan kari.
Da ya juya a kan tarihin kafuwar kasuwar, Gwamnan ya fadi cewa, a cikin watan Yuni na shekarar 1979 an wayi gari babbar kasuwar ta Maiduguri ta kama da wuta ta cinye kurmus sai toka kawai, wannan in ji Gwamnan, shi ya yi sanadiyar asarar dimbin dukiyar ‘yan kasuwar a wancan zamanin da rayukan wasu mutane.
“Ko da yake gwamnatocin da suka gabata suna da shirin gina sabuwar kasuwa ta zamani a Maiduguri amma haka bai samu ba bisa ga dalilin da ban sani ba har yau, sai da muka hau Gwamnati.” In ji Gwamnan.
“Ba ko shakka wannan rana muhimmiya ce gare mu tun da mun zo gwamnati a yayin da wannan kasuwa ta zame toka kawai amma yau cikin ikon Allah ga shi muna bikin bude wannan damfareriya kuma ginannnar kasuwa wadda ba irin ta a duk fadin kasar nan.”
A kan yadda za a raba rufunan, Gwamnan ya ba da tabbatacin cewa za a yi rabon ne cikin adalci ba tare da la’akari da bambancin siyasa da addini ko kabila ba. Don haka sai ya roki ‘yan kasuwar da Allah bai ba su nasarar samun runfuna a cikin kasuwar ba da su yi hakuri su nema a wajen sababbin kantunan da ake ginawa a kan titin Sir. Kashim kusa da kantin Lebentis.
Alhaji Mohammed Goni ya fadi dai cewa, babu dai yadda za a ce kowa ya samu irin wadannan runfuna.
Da yake gabatar da nasa jawabin, Kwamishinan Raya Karkara na Jihar Alhaji Abba Zanna Mustapha ya fadi cewa, “Kasuwar ta kunshi runfuna iri dabam – dabam har 7,170.”
Kwamishinan ya ce wannan adadi na runfuna sun hada da dakunan ajiyar kayayyakin abinci (nama da kifi) har guda 310 da wurin sayar da abinci 60 da wurarren gyare – gyaren na’urori 10 da ofishin ‘yan sanda da na ‘yan kwana – kwana da masallaci da dai sauraren muhimman wuraren da a kan samu cikin kasuwanni irin na zamani.
Daga bisani kwamishinan ya za ga ya da Gwamnan dukkan sassan kasuwar.
Da yake bude sabuwar tashar Telebijin ta jihar, Alhaji Mohammed Goni ya ce ya zama wajibi ne ga gwamnatinsa ta kafa gidan Telebijin din kashin kanta.
Domin a cewarsa, “Kafofin watsa labarai na Gwamnatin Tarraya da ke Jihar ba su watsa irin ayyukan a zo a gani da Gwamnatinsa take yi.”
Gwamnan ya yi nuni da cewar irin wannan halayen gidaje watsa labaran na Gwamnatin Tarayya suka sanya Jihohin Kano da Anambra da Pleteau da Ikko suka kafa gidajen Telebijin din kashin kansu.
Alhaji Mohammed Goni ya ba da tabbacin cewa Gwamnatinsa ba ta nuna wani bambanci ko son kai ba wajen bayar da dama ga sauran Jam’iyyun siyasa na Jihar wajen amfani da gidan Telebijin din.
Tun farko da yake gabatar da jawabinsa, kwamishinan al’ummar cikin gida na watsa labarai da al’adun gargajiya na Jihar, Alhaji Abba Tor ya fadi cewa, “Saboda ganin yadda aikin ginin gidan Telebijin din zai dauka lokaci dangane da fatarar da ake fama da ita a kasar nan, ya sanya aka kasa aikin cikin hawa – hawa.”
A cewarsa, shirin farko da aka fara aiki da shi an kashe #1.5 miliyan, yayin da ake iya ganin shirye – shiryen tashar daga nisan kilomita 50 daga wajen garin Maiduguri. Alhaji Abba Tor ya ba da tabbacin cewa ana nan ana shirin wata doka da za a mika wa majalisar Dokokin Jihar don a samu a hada gidan Rediyon jihar da na Telebijin din da su zama abu gudu, watau a rinka kiran su Gidan Rediyo da Telebijin na Jihar.
A wata kuma, wakilinmu ya fahimci cewar yayin da Gwamnan ke bikin bude kasuwar su kuma ‘yan kwangilar kasuwar watau ‘SOGHAI NIG. LTD’ suna ciki suna kokarin kare ayyukan da suka rage kamar debe wa da sauran datti wanda ba a rasa ba.
Har ila yau dai kuma ba a sa wata rana takamaimai ba da za a bayar da izini ga ‘yan kasuwa su dawo cikin sabuwar kasuwar.
Wakilinmu ya fahimci cewa, dalilai biyu ya sa Gwamnantin jihar ta hanzarta bikin bude kasuwar, duk da kuwa akwai sauran aiki. Na farko dai shi ne neman biyan bukata siyasa na a ce Gwamna Alhaji Mohammed Goni ya yi aiki. Na biyu kuwa shi ne Bankin First Bank ya ba Gwamnatin Jihar rancen kudn ginin kasuwar ya fara uzurawa Gwamnatn Jihar da ta fara biyan bashin.
Wannan shi ne rohoton da Marigayi Ado Saleh Kankiya ya hada na bude babbar kasuwar ta Litinin da aka yi a shekarar 1983 bayan an sake gina ta.
A cikin shekarar 2015 ma an samu irin wannan iftila’in na gobara a cikin wannan babbar kasuwar inda aka tafka mummunar asara mai yawa. Bayan shekaru takwas kuma sai ga shi kasuwar ta sake konewar fiye da wanda aka yi a shekarun 1979 da kuma 2015. Ko wacce hanya da mataki ya kamata gwamnati da hukumar kasuwar ya kamata su bi wajen magance iftila’in gobara a wannan babbar kasuwa?
Za ku iya tura sakon kar-ta-kwata (tedt) ta wannan lambar 08069195272 ko kuma ku kira 08098331260 domin ba da shawarwarinku tare da gudunmawarku.
Mohammed Bala Garba (Mohammed Bawayo) ke muku fatan alheri daga birnin Maiduguri.