Dandalin Ishak Idris Gulbi" />

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Asabar 24 Zuwa Alhamis 29 Ga Sha’aban 1441, Bayan Hijirah

Asabar

Saudiya ta ce a bana ba sallolin azumin watan Ramadan, haka nan babu sallar Idi kowa ya yi su a gida in har cutar kwaronabairos ta ci gaba da yaduwa.
An yi gobara a ofishin babban akanta na kasa da ke Abuja, aka yi wata gobarar a shalkwatar hukumar yi wa kamfanoni rajista ta kasa da ke Abuja, aka sake yin wata gobarar a ginin shalkawatar hukumar zabe ta kasa da ke Abuja, da bayanin cewa duk gobara ce da ba ta shafi muhimman kayayyaki ba, in ban da tebura da kujeru.
Gwamnatin tarayya ta ce dokar tilasta kulle da ta sa tana haifar da, da mai ido.
Turawa na cewa cutar kwaronabairos za ta yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Afirka su dubu dari uku cikin kwanaki kadan, sai dai na ji Nijeriyawa/’Yan Nijeriya na cewa bakinsu ya sari danyen kashi. Sai dai su turawan su yi ta mutuwa ba dai mu ba.
Ana kokarin kai ruwa rana tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da ma’aikatanta. Inda take cewa za ta cirewa kowanne ma’aikaci kashi ashirin da biyar cikin dari na albashinsa da za a raba, a cire watan Afrilu da na Mayu, a matsayin gudunmawarsu ga yaki da cutar kwaronabairos a jihar Kaduna. Su kuma ma’aikatan sun ce ba su yarda ba. In har ya zama dole sai sun ba da gudunmawa to kashi biyar suka amince a cire, ba ashirin da biyar ba.
Gwamnan jihar Barno Farfesa Zulum har ya biya ma’aikatan jiharsa da ‘yan fansho albashinsu na watan nan na Afrilu, saboda karatowar azumi ga kuma kulle ana ciki.
Saura kiris da an bai wa hammata iska tsakanin sojoji da ‘yan sanda, a randar kusa da ginin Lugard da ke cikin garin Kaduna. ‘Yan sanda sun tare hanya saboda masu karya dokar kulle, sai ga motar loziriyos makare da sojoji za ta wuce, ‘yan sanda suka tare su, suka ce ba su isa su wuce ba, saboda umarni ne daga kwamishinar/kwamishiniyar lafiya ta jihar Kaduna. Nan kaya-kaya har aka ji wa wani soja rauni. Sai ga Samuel Aruwan da wasu manyan soja da na ‘yan sanda sun iso wajen, suka kashe wutar. Sai dai na ji wani yana cewa bashi ‘yan sandan suka ci wajen soja.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna kaduwarsa a kan rasuwar ‘yan gudun hijira su wajen goma sha biyu a sansanin Ngala da ke jihar Barno sakamakon wata gobara.
Sai ga labarin rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Lahadi
Gwamnan jihar Kano Ganduje, ya cire kwamishinansa na ayyuka Mu’azu Magaji saboda kalaman da ake zargin ya yi da ke nuna yana farin ciki da rasuwar Abba Kyari.
Bayanan da ke fitowa daga jihar Kaduna na cewa matashin nan da aka ga bidiyonsa na karakaina mai suna Tasiu Mohammed, da ake tunanin ya harbu da kwaronabairos, ya rasu amma ba cutar ce ta yi ajalinsa ba. An ce ya fito daga jihar Ogun ne za shi Jigawa.
Sojojin sama sun kai wa ‘yan kungiyar Boko Haram da ke dajin Sambisa hari.

Litinin
Ana ci gaba da kidinafin jama’a, jiya an sako wani abokin aikinmu a foliteknik, aka kuma yi kidinafin wani ma’aikacin Rediyon Nijeriya.
Wasu mahara sun kai hari kananan hukumomi uku da ke jihar Katsina, suka kashe mutane da dama, har shugaban kasa Buhari ya yi tir da harin.
An hana mukarraban gwamnatin tarayya da suka halarci jana’izar Abba Kyari shiga fadar shugaban kasa saboda zargin sun saba wa ka’ida da sharuddan jana’izar.
Gwamnatin jihar Katsina ta kafa dokar kulle a karamar hukukar Katsina saboda rigakafin yaduwar cutar kwaronabairos.
Gwamnatin jihar Bauci ta ce ta kasa kafa dokar kulle a jihar ne saboda a gaskiya idan ta tilasta wa jama’a yin kulle ba ta da abincin da za ta ciyar da talakan jihar.
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kwashe almajirai baki da ba ‘yan asalin jihar ba, zuwa garuruwansu.
‘Yan sanda a jihar Taraba, sun tarbe wata mota dauke da matafiya sittin da biyar da aka ce sun fito daga jihar Ogun ne, har sai an tantance lafiyarsu kafin a san na yi da su.
Af! Ina ta mamaki ana kulle amma kidinafas da mahara suna ta fita suna karya dokar kulle da cin karensu babu babbaka.

Talata
Ta tabbata mutum arba’in da bakwai ‘yan bindiga suka kashe a jihar Katsina a kananan hukumomi uku.
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wa sojoji hari a Gaidam da ke jihar Yobe, sai dai kamar yadda sojojin suka yi bayani, ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun sojojin, suka kuma kwace ko lalata makaman ‘yan kungiyar.
Sojoji sun kai wa ‘yan kungiyar Boko Haram da ke Darbala a jihar Barno farmaki ta sama.
Jami’an tsaro sun kama wasu kidinafas guda ashirin da uku, suka kashe daya, a jihar Taraba.
Gwamnatin tarayya ta nemi ahuwar kuskure ko saba wa ka’idoji da ake zargin an yi a wajen jana’izar Abba Kyari.
Gwamnatin tarayya ta kara mako biyu, a kulle da ta yi wa tasoshin jiragen sama na kasarnan. Ba wai jirage ba sa tashi ba ne gabadaya, a’a fasinja ne ba a diba.
Na so in ga wani labari da ke cewa kamfanin lantarki na Kaduna ya ce ya dakatat da yanke wutar wadanda ba su je sun biya kudin wuta ba saboda wannan hali da ake ciki na kwaronabairos. Ya kuma ware wasu makudan kudi don tallafa wa talakawa. Na ce ba? Mu da ba a ba mu wutar ya za a yi da mu ke nan?
Gwamnonin jihohin yarbawa za su tilasta wa kowa sa takunkumin hana yada cutar kwaronabairos ko daukarta a jihohin nasu.

Laraba
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a biya malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya da suka tirje wa shiga tsarin IPPIS albashinsu da suke bi na watan Fabrairu, da na watan Maris ba tare da bata wani lokaci ba.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a biya duka ma’aikatan gwamnatin tarayya albashinsu na wannan watan na Afrilu ba tare da bata wani lokaci ba, ko sa samu sauki daga kullen da aka tilasta musu saboda cutar kwaronabairos.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a hanzarta rage cunkoso a gidajen gyara hali da ke kasar nan don gudun yaduwar cutar kwaronabairos a gidajen.
Ministar ayyukan jinkai Sadiya Faruk, ta ce za a ci gaba da raba abinci da kudi ga wadanda Allah Ya tsaga da rabonsu har wata biyu nan gaba.
Sarkin Musulmi ya ba da umarnin ba taruka na lakca na Ramadan ko makamancin hakan saboda rigakafin yaduwar cutar kwaronabairos.
Gwamnonin jihohin Arewa sun bukaci a samar da karin wuraren gwada jama’a don gano masu cutar kwaronabairos a jihohinsu na Arewa.
Gwamnatin jihar Kano, da kwamitin shugaban kasa a kan cutar kwaronabairos, za su gudanar da binciken dalilan da suka sa ake ta mutuwa a Kano.
Gwamnatin tarayya ta gargadi masu sayen wani magani wai da ke maganin kwaronabairos a Kano da su daina.
Kasar Ingila za ta soma gwajin wani magani da ta kirkiro na cutar kwaronabairos.
Danyen man Amurka ya fadi kasa warwas, kasa da dala daya kowacce ganga, faduwar da ta sa ciko zai biyo gyartai. Maimakon a saya, sai ita ce ma za ta biya kudin wahalarsa.
Wasu sun fille kan wani a sabon harin da suka kai jihar Binuwai.
A jihar Filato kidinafas ne wasu har daga jihar Taraba, ke nikar gari har jihar ta Filato su sace musu sarakuna ko iyalansu.
An samu saukin cutar Lassa da ta Foliyo a Nijeriya kusan ma babu wani sabon harbuwa da cutar lassa a kasar nan a ‘yan kwanakin nan.
Siga/sikari da madara da kayan miya sun yi tashin gwauron zabi a kasuwa, talaka na ta wayyo Allah!

Alhamis
Majalisar Sarkin Musulmi ta bukaci al’umar musulmi a soma duban janjirin watan Ramadan daga yau da almuru, da an gani a sanar da basarake na musulunci mafi kusa, ko a kira 08037157100 ko 07067416900.
Gwamnatin tarayya ta dage jarabawar WAEC da ta NECO sai nan gaba.
An raba naira biliyan 780 da ‘yan kai tsakanin gwamnatin tarayya, da jihohi da kananan hukumomi na watan Maris, da ke nuna yau za a fara jin dilin-dilin.
Malaman jami’o’i da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a hanzarta biyansu albashinsu na watan Fabrairu da na Maris, sun ce tsugune fa ba ta kare ba. Ko an biya su, ba za su janye yajin aikin da suke kan yi ba. Domin ba don an ki biyansu albashin suke yajin aikin ba.

Kungiyar gwamnonin kasar nan ta ba da shawarar a rufe dukkan kan iyakokin jihohin kasar nan don tarbe yaduwar kwaronabairos.
A yau Babban Bankin Nijeriya zai soma raba wata naira biliyan hamsin ga wadanda Allah Ya tsaga da rabonsu. Mutum dubu tamanin ya mika bukatarsa ta tallafin.
Hukumar kula da kare hakkin bil’Adama ta kasa ta ce tana nan tana ci gaba da hada hancin alkaluman wadanda jami’an tsaro suka kashe ko cin zarafinsu wajen tilasta musu bin dokar kulle.
Gwamna Ganduje na Kano ya ce mutum daya ya san ya riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar kwaronabairos a jihar, sauran da suka rasu za a bincika a ji me ya kashe su
An dakatar da aikin gwajin gano masu cutar kwaronabairos a jihar Kano saboda karewar kayan aikin gwajin.
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga su ashirin da daya a Zurmi ta jihar Zamfara, sai dai sojojin sun ce an kashe musu sojoji hudu.
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi shelar warkewarsa garau daga cutar kwaronabairos da ya sanar ya harbu da ita. Sannan gwamnatin jiha ta ba da wadannan lambobi da za a kira in an ga wanda ya harbu da cutar kwaronabairos ko mutum shi da kansa yake jin alamun ya harbu: 08051217710 da 09058008251 ko 08118588175 ko 08118588176.
Ooni na Ile Ife zai raba wa gwamnonin jihohin kasar nan talatin da shida, kowannensu motoci biyu na feshin kashe kwayoyin cutttuka kyauta. Don feshi a birane da kauyukansu. Wato zai raba musu motocin kyauta.
Ministan lantarki ya ce har yanzun akwai sauran rina a kaba a game da ba ‘yan Nijeriya wuta kyauta ta tsawon wata biyu. Domin kamar yadda ya ce, za a yi ne domin kowa ya amfana, amma kalilan ke da wutar.

Exit mobile version