Connect with us

Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 23 Zuwa Alhamis 26 Ga Shawwal 1441, Bayan Hijira

Published

on

LITININ

Assalamu alaikum barkanmu da sake haduwa a wannan makon. Za mu fara waiwayen kanun labarun namu da litinin, ashirin da uku ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi gaisuwar ta’aziyyar Ibidunmi Ighodolo matar fasto Huah Ighodolo da ta riga mu gidan gaskiya a wani otel.
An bayyana cewa babu abin da ya auku ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sakamakon wata hatsaniyar da ta auku a cikin fadar shugaban kasa ranar alhamis tsakanin iyalansa da har ta kai ga an harba bindiga da tsare wasu mukarraban.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da hare-haren da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wuraren Guibio har ya shafi bangaren ayyukan jinkai.
Sojojin sama sun dakile wani sabon hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai Barno. Sannan sojoji sun farmaki ayarin kwamitin yaki da kwaronabairos na jihar Barno, har mutum daya ya riga mu gidan gaskiya.
Wani fadan kabilanci a jihar Binuwai ya yi sanadiyyar kashe mutum a kalla goma, ashirin ba a san inda suke ba.
‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari Mongunu da ke jihar Barno, suka kashe sojoji da farar hula.
Wasu ‘yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare ‘Yan Kara da ke jihar Katsina, suka kashe mutane da dama, suka yi kidinafin wasu, a yankunan Daudawa da su Funtuwa, da Faskari da Kankara ga jama’a na ta gudun hijira daga garuruwansu.
Shalkwatar Tsaro ta ce ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe fiye da mutum tamanin da daya a Guibio da ke jihar Barno.
Wata gada da ta rifta sakamakon ruwan sama a jihar Kwara, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da bacewar wasu mutum biyu.
Shugaban Kasar Ghana Akufo-Addo ya sanar da za a bude jami’o’i da sauran manyan makarantu da ke kasar a yau litinin bayan kulle su sakamakon kwaronabairos.
Ana ci gaba da zanga-zanga a kasashen duniya irin su Jafan, da Jamus, da Niw Zilan da sauransu na taya Amurkawa da ke zanga-zangar Allah Ya tsine wa ‘yan sanda turawa da suka kashe George Floyd bakar fata.
Af! sun dauka na manta da batun ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya ne, da ke ci gaba da korafin shekara daya da wata biyu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi! Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

TALATA

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa a watanni biyar da suka gabata, akwai bayanai da ke nuna an yi fyade guda dari bakwai da goma sha bakwai. Aka danganta karuwar fyaden ga dokar kulle da aka sa jama’a ciki.
Kungiyar Amnesty International ta kare hakkin bil’Adama, ta bukaci gwamnatin tarayya ta nuna da gaske take yi wajen magance matsalar tsaro da ke ci gaba da tabarbarewa a arewacin Nijeriya.
‘Yan sanda sun damke wasu daga cikin wadanda suka kai hari Kadisau da ke jihar Katsina, har suka kashe fiye da mutum hamsin da daya.
Jami’an tsaro na sibildifes sun damke mutum goma sha daya da ke sayar wa ‘yan kungiyar Boko Haram manfetur da sauran kayayyakin da sukan bukata a jihar Barno.
Jami’an tsaro sun damke mutum shida da suke zargi suna da hannu a kisan mutum tara da aka yi a rikicin da ya auku a karamar hukumar Agatu da ke jihar Binuwai.
Mutanen kauyuka goma sha shida suka tsere daga kauyukan nasu da ke jihar Katsina zuwa garuruwa daban-daban gudun hijira. Wata ta ce haka suke cunkushe mutum goma sha tara a daki daya, a inda suka samu mafaka.
A jihar Zamfara wuraren Dan Sadau wasu mahara sun kashe na kashewa suka kwashi na kwashewa maza da mata ashirin da shida a shekaranjiya lahadi.

LARABA

Gwamnatin Tarayya ta ba da sharuddan da in har ma za a bude makarantu a yanzun, to dole sai an kiyaye da su tukuna kafin a bude.
Kotun Daukaka Kara ta amince da hukuncin Babbar Kotun Tarayya na dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban APC na kasa baki daya. Har ila yau kotun ta raba shi da duk wata alfarmar da yake cin gajiyarta a matsayinsa na shugaban APC har da al’amura da suka shafi tsaronsa. Da ma Oshiomholen shi ya daukaka kara cewa bai yarda da hukuncin kotun farko ba.
Gwamnan jihar Edo Obaseki ya fice daga jam’iyyar APC har Oshiomhole da kotu ta ce daga yanzun ba shi ba ne shugaban APC ya ce wa Obasekin “Good Riddance to Bad Rubbish” Wato Allah Raka Taki Gona” ko “Umma ta gai da Aisha”
A ranar Litinin likitoci da aka fi sani da RESIDENT DOCTORS da ake wa lakabi da likitocin da ke hanyar kwarewa, suka soma yajin aiki na kasa bakidaya, ko da yake wadanda ke Fatakwal ba su shiga yajin ba saboda sun ce suna tausayin masu lalurar kwaronabairos.
Gamayyar kungiyon ma’aikatan lafiya da aka fi sani da JOHESU na barazanar za su tafi yajin aiki.
Hukumar shirya jarabawar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu JAMB, ta fitar da cewa idan dalibi ya ci makinta dari da sittin to ya ci jarabawarta da zai iya samun gurbin karatu.
Gwamnatin jihar Legas ta dakatar da batun bude masallatai da coci-coci saboda karuwar da kwaronabairos ke yi a jihar a kullum.
Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ta fitar da sanarwar sallamar malamanta na kwantaragi, da wadanda ke mata bisitin, da masu yi mata aikin wata-wata tana biyansu, daga shekaranjiya goma sha biyar ga watan nan da muke ciki, tare da ba su notis na wata daya, da kudin wata daya ka’idar sallamarsu.
Farfesa Ango Abdullahi a madadin Kungiyar Dattawan Arewa NEF ya rubuta wa shugaban kasa Muhamnadu Buhari koke a kan kashe-kashen da ake yi wa mutanen Arewa a Arewa. Ita kuma fadar shugaban kasa ta hannun Femi Adeshina ta ce Farfesa Ango Abdullahi shi kadai yake kidansa yake rawarsa da bazar kungiyar. Adawa ce kawai take damunsa in ji fadar shugaban kasa.
Matasan Arewa da kashe-kashen da ake yi wa mutanen Arewa ya ishe su, sun kaddanar da zanga-zanga a Katsina. Zanga-zangar da suka ce sun sa dan ba ne ranar Talata, domin ta gama-gari ce da za a dauki kwanaki ana gudanar da ita a fadin kasar nan. A zanga-zangar tasu ta jiya, suna ta sukar gwamnan jihar Katsina Masari da shugaban kasa Muhamnadu Buhari a kan gazawarsu wajen kare mutanen Arewa.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekerar nan.

ALHAMIS

Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta sako Nastra Ashir Shariff da ya jagoranci matasan da suka yi zanga-zanga a jihar Katsina saboda matsalar tsaro a Arewa. Kamar yadda matasan suka shaida wa BBC Hausa, an kama Ashir ne saboda wai ya zagi Femi Adeshina da kuma jagorantar zanga-zangar. Matasan suka ce nan Femin ya zazzagi dattijo farfesa Ango Abdullahi ba wanda ya ce masa don me. Don kawai Angon ya yi korafi a kan gwamnati ta gaza kare mutanen arewa daga makasa.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta mike tsaye wajen kare rayukan talakawan Nijeriya don da alamu ta gaza har aka kashe wasu kauyawa su wajen dari da ashirin a jihar Barno.
Amurka ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nuna da gaske take yi wajen kare rayukan talakan Nijeriya. Amurka ta ce da alamu gwamnatin Nijeriya ta gaza bangaren tsaron rayuka.
An yi zargin a ranar Laraba da daddare wasu ‘yan bindiga sun kewaye yankin Idi da Rambadawa a mazabar Tara da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.
Wani Sanata ya yi korafi a kan yadda ‘yan bindiga suka addabi jihar Neja har suka kashe ‘yan sanda a kalla hudu.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya halarci wani taro na Afirka da Kasar Caina ta hanyar intanet a Abuja don tattauna yadda za a bullo wa kwaronabairos ta bayan gida.
Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi sun raba naira biliyan dari biyar da hamsin da bakwai da ‘yan kai na watan Mayu. Da ke nuna zuwa makon gobe za a soma jin dilin-dilin na wannan watan.
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman bangaren tsaro, da shugaban ‘yan sandan Nijeriya da na sashen tsaro na DSS duk sun isa jihar Katsina jiya, a kan matsalar tsaro.
Ana takaddamar wane ne ya kamata ya rike jam’iyyar APC bayan dakatar da Oshiomhole, tsakanin wanda aka zaba Abiola Ajimobi, da wanda ya nada kansa bictor Giadam, da Hilliard Etta da aka ce ya rike wa Ajimobi.
Hukumar Zabe ta Kasa ta ba jam’iyyun da suke son fafatawa a zaben gwamna na jihar Edo kwana goma don kammala zabukan fid-da-gwani.
Hukumar EFCC ta ce a cikin wata shida ta kwato wata naira miliyan dari hudu a jihar Sakkwato.
Yanzun karfe hudu saura minti ashirin da biyar na kusan asubah an tsuge da ruwan sama a nan cikin garin Kaduna. Haka ma jiya goshin almuru har zuwa dare ana ta ruwan sama.
Mutum miliyan tara da dubu dari daya suka harbu da kwaronabairos a duniya zuwa Larabar nan.
Af! Kai dai ga mutum. Da ciwo wanda ka amincewa aka zama daya ana tare kowanne lokaci, ashe shi da zuciya biyu yake tare da kai ba don Allah ba. Dama kawai yake ta nema ya maka sharri. Allah Ka mayarwa da kowa aniyarsa, in sharri ce ta kare a kansa Amin.

Advertisement

labarai