Al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin makomar kowace al’umma da kowace kasa tana da nasaba da juna. Hakan na nufin ya kamata mu yi rayuwa tare duk rintsi duk wuya, muna more daukaka da wahala tare da kuma kokarin mayar da duniyarmu al’umma guda mai jituwa, inda za mu mai da burin mutane na samun ingantacciyar rayuwa ta zama gaskiya. Shekaru 12 da suka gabata, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aiki ta farko a matsayinsa na shugaban kasar Sin, ya gabatar da wannan ra’ayi mai cike da hangen nesa. Tun daga wannan lokacin, ra’ayin ko tunani ya bunkasa zuwa wani tsari na musamman da ake aiwatarwa, tare da samun kaso mafi girma na amincewa daga kasashen duniya. A yau, ba wai kawai ra’ayin ya kunshi nuna nagartattun dabi’un bai daya ba ne, har ma ya kasance shimfidar tsarin tunani na yin gyare-gyare na Majalisar Ɗinkin Duniya yayin da take cika shekaru 80 da kafuwa.
Tunanin al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya shi ne ginshikin tunanin Xi Jinping kan harkokin diflomasiyya, wanda ke wakiltar zurfafa fahimtar kasar Sin game da muhimman dokokin dake kula da ci gaban zamantakewar dan Adam, kuma yake ba da amsa ta musamman ta Sinawa ga tambayar “Wace irin duniya ce ya kamata mu gina, kuma ta yaya za mu gina ta?” Tun farkon wannan zamani da muke ciki, wannan hangen nesa ya sauya daga shawarar kasar Sin zuwa yarjejeniya ta kasa da kasa, daga buri zuwa aiki na hakika, kuma daga faffadan ra’ayi na falsafa zuwa tsarin bayanai game da aiwatar da manufofi. Kana ya zama fayyatacciyar ka’idar zamaninmu, wanda ta shimfida hanyar hadin gwiwar duniya da gudanar da mulkinta. Har ila yau, gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin yunkurin samar da kyakkyawar duniya mai cike da zaman lafiya, aminci, wadata, budaddiya, hadaka, da kuma tsabta. Kazalika ra’ayin yana kira da a samar da sabon tsarin gudanar da harkokin duniya bisa tuntuba, da ba da gudunmawar hadin gwiwa, da fa’idodi na bai daya, masu daukar dabi’un da suka dace da dan Adam. Yana kuma habaka sabon nau’in alakar kasa da kasa, ta hanyar kaddamar da shirin Raya Duniya, da shirin Tsaron Duniya, da shirin Wayewar Kai na Duniya dake aiki a matsayin ginshikan wannan tunanni. Haka ma hadin gwiwa mai inganci karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya mai amfani wajen aiwatar da wannan hangen nesa, tana bai wa kasashe damar yin aiki tare wajen magance kalubalen duniya da samun wadata tare. Wannan hangen nesa a karshe yana jagorantar duniya zuwa ga makoma mai cike da zaman lafiya, tsaro, wadata da ci gaba. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp