A duk ranar 19 ga watan Agusta ne ake bikin ranar jin kai ta duniya, ranar da asali aka kirkire ta domin alhinin jami’an jin kai da aka kashe, ko aka jikkata yayin da suke bakin aiki, tare da jinjinawa daukacin ma’aikatan jin kai da na lafiya dake ci gaba da samar da hidimomin ceton rayukan jama’a, da kare mutanen dake cikin matsanancin yanayin bukatar agaji.
To sai dai kuma a bana, bikin ranar ya zo daidai gabar da yanayin da ake ciki, ke kara tunatar da duniya irin muggan laifukan da ake aikatawa ga bil’adama musamman a yankin gabas ta tsakiya.
- Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025
- Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana
Tashe-tashen hankula na ci gaba da bazuwa tun daga Gaza, zuwa Sudan, da Syria da Yemen, lamarin da ya haifar da mummunan bala’i da yanayin bukatar jin kai, wanda ke nuni da cewa duk da ci gaban da duniya ke samu ta fuskar ilimi, kimiyya da fasahohi, a hannu guda bil’adama na ci gaba da fuskantar manyan kalubalen rayuwa da suka hada da yunwa, da muzgunawa da rashin tsaron rayuka.
Alkaluman baya bayan nan na nuna cewa a Gaza, wurin da kusan mutane miliyan biyu ke matse a yankin da bai wuce sakwaya mita 45 ba, adadin mutane da yaki ya hallaka ya munana. Mahukuntan lafiya a wurin na cewa an hallaka sama da mutane 62,000, tun sake barkewar tashin hankali a zirin, ciki har da yara kanana kimanin 18,000. Baya ga karasa gurgunta tsarin kiwon lafiyar birnin, da yunwa da ta haifar da mace-macen jama’a.
Haka ma abun yake a Sudan, kasar da tashe-tashen hankula suka raba mutane kimanin miliyan 12 da muhallansu, adadin da ya kai kusan daya bisa hudu na daukacin jama’ar kasar. Wadannan misalai ne na irin matsanancin hali da al’ummun kasashen Yemen da na Syria ke fuskanta, karkashin ayyukan bil’adama ba wai bala’i daga indallahi ba!
Don haka, a wannan gaba da ake waiwaye-adon-tafiya, game da wadannan matsaloli na jin kai dake addabar wasu duniya, ya wajaba sassan kasa da kasa, su sauke nauyin dake wuyansu na raya ruhin jin kan bil’adama, ta hanyar shiga tsakani, da warware rigingimu, da gudanar da shawarwarin zaman lafiya, da tallafawa ma’aikatan jin kai, ta yadda za su gudanar da ayyukansu lami lafiya. A hannu guda kuma, a himmatu wajen magance tushen aukuwar tashin hankali a dukkanin sassan duniya, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp