Wakilai daga jihohi 19 sun isa Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Juma’a, domin halartar taron ƙasa na jam’iyyar PDP wanda za a gudanar a ranar Asabar 15 ga Nuwamba da Lahadi 16 ga Nuwamba. Jihohin da suka halarta sun haɗa da Adamawa, da Akwa Ibom, da Anambra, da Bauchi, da Bayelsa, da Benue, da Borno, da Cross River, da Delta, da Edo, da Ebonyi, da Enugu, da FCT, da Imo, da Kaduna, da Jigawa, da Kano, da Katsina, da kuma Ekiti.
Taron na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke fuskantar rikice-rikice na cikin gida da kuma shari’a a kotu. Kwamitin aiki na ƙasa (NWC), ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum, ya dakatar da Sakatare na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu; Sakatare mai Shirya taro, Umar Bature; da Lauyan jam’iyyar na ƙasa, Kamaldeen Ajibade, bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓawa jam’iyya. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin kotun tarayya wanda ya dakatar da taron na ɗan lokaci saboda rashin bin ƙa’idojin gudanarwa, ciki har da gazawar isar da sanarwar taron ga INEC.
- Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar
- Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike
Sai dai umarnin Alƙali Akintola ya baiwa jam’iyyar dama ta ci gaba da taron. An kammala shirye-shiryen wajen taron a Filin Wasanni na Lekan Salami, inda aka ƙawata shi da launukan jam’iyyar. Ana sa ran wakilai sama da 3,000 daga jihohin tarayya 36 da FCT, tare da shugabanni, masu ruwa da tsaki, da kuma masu sanya ido daga ƙasashen waje zasu halarci taron.
Za a gudanar da zaɓen manyan muƙamai na kasa a wannan taro, ciki har da zaɓen Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sakatare, da sauran manyan jami’an NWC da mataimakansu. A wajen taron, aiyuka na tafiya a ƙarshe, inda aka ɗora tallace-tallace da hotunan yaƙin neman zabe a wurare masu muhimmanci a ciki da wajen filin wasa.
An yi hasashen wannan taro a matsayin ɗaya daga cikin masu jawo cece-kuce mafi girma a tarihin PDP, musamman ma ganin cewa wani ɓangare na jam’iyyar ya janye daga halarta, wanda hakan ya ƙara tsananta yanayin siyasar zaɓen.














