A jiya Laraba, agogon Amurka ne Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a kan wani kuduri na neman tsagaita wuta a yankin Gaza wanda mambobin kwamitin marasa kujerar dindindin su 10 suka gabatar.
Ba a samu nasarar amincewa da kudurin ne ba sakamakon hawa kujerar na ki da Amurka mai kujerar dindindin ta yi.
- Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Fiye Da Biliyan 465 A Matsayin Kasafin Kuɗin 2025
- Kasar Sin: Ya Kamata Nahiyar Turai Ta Girmama Manufar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
A jawabin da ya yi bayan kada kuri’ar, babban wakilin kujerar dindindin ta kasar Sin a MDD Fu Cong ya ce, sakamakon kuri’ar da aka kada ya ba kasar Sin kunya ainun musamman yadda Amurka ta yi amfani da cikakken ikonta na hawa kujerar na ki wajen dakushe fatan da ya rage wa al’ummar Gaza na rayuwa tare da kara tura su cikin duhu da zullumi.
Fu Cong ya nunar da cewa kimanin mutum 44,000 suka mutu a Gaza amma duk da haka Amurka ta yi amfani da ikonta na hawa kujerar na ki ba tare da wata-wata ba.
Ya kara da cewa, “wai shin kisan mutum 44,000 bai isa ya sa Amurka ta ji tausayi ko kamar kwayar zarra ba a zuciyarta?” (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)