Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin Afirka Liu Yuxi, ya yi kira ga kasashen duniya, da su goyi bayan rawar da nahiyar Afirka ke takawa, wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron kanta. Liu ya bayyana haka ne, yayin zaman muhawarar bainar jama’a da kwamitin sulhu na MDD ya shirya, kan tasirin manufofin raya kasa game da aiwatar da shawarar Afirka na kawo karshen amon bindigogi.
Liu Yuxi ya ce, idan babu zaman lafiya da ci gaba a Afirka, hakika ba za a samu kwanciyar hankali da wadata a duniya ba. Yana mai cvewa, bisa halin da ake ciki yanzu, kwamitin sulhu na bukatar yin nazari sosai, kan wasu batutuwa kamar yadda za a karfafa hadin gwiwar kasa da kasa don kara taimakawa Afirka, wajen fuskantar kalubalen da ke gabanta, da yadda za a samar da hadin gwiwa tsakanin manufofin raya kasa don tinkarar matsalolin da ke haifar da rikice-rikice, da yadda za a ciyar da hadin gwiwar MDD da Afirka don ba da tallafi mai karfi.
Don haka, ya ce, yana da mahimmanci a goyi bayan rawar da Afirka ke takawa, na samar da zaman lafiya da tsaron kanta. Yana mai cewa, ‘yan Afirka sun fi kowa sanin nahiyarsu, kuma kasashen Afirka, su ne jigon kiyaye zaman lafiya da tsaron kansu. (Ibrahim)