Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ayyukan masu rajin neman samun ‘yancin kan Taiwan tare da masu goya musu baya daga waje, babbar barazana ce ga zaman lafiyar zirin Taiwan.
Wang wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da atisayen soji da Sin ke gudanarwa a kusa da tsibirin na Taiwan, ya kara da cewa, kamar dai yadda ruwa da wuta ba za su hadu wuri daya ba, haka ma burin ballewar yankin Taiwan, ya saba da burin wanzar da zaman lafiya da daidaito a zirin na Taiwan.
Ya ce, “Domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan, ya zama wajibi mu tabbatar da rashin amincewa da duk wani mataki na ingiza burin ‘Samun ‘yancin kan Taiwan”.
A ranar Asabar ne rundunar dake gabashi ta sojojin ’yantar da al’ummar kasar Sin, ta sanar da kaddamar da atisayen shirin ko ta kwana da sauran ayyukan rawar-daji a kewayen tsibirin na Taiwan.
A wata sabuwa kuma, kakakin rundunar, Shi Yi ya bayyana a Litinin din nan cewa, rundunar ta kammala atisayen shirin ko-ta-kwana, da sauran ayyukan rawar-daji cikin nasara. (Saminu Alhassan)