Daga Bilkisu Xin,
Yanzu haka kumbon Shenzhou-13, wanda aka harba a ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 2021, ya shafe watanni uku da wani abu yana aiki a sararin samaniya. Baya ga tsawon lokacin da Shenzhou-10 da aka harba a ranar 11 ga watan Yuni na shekarar 2013 kuma ya dawo a ranar 26 ga watan Yuni na wannan shekarar. Wang Yaping, shafe fiye da kwanaki 100 tana aiki a sararin samaniya, abin da ya sa ta zama ‘yar sama jannati ta farko a kasar Sin da ta shafe kwanaki sama da 100 tana kewayawa a sararin samaniya.
Ya zuwa yanzu, ‘yan sama jannatin Shenzhou-13 sun shafe fiye da watanni 3 a tashar sararin samaniyar kasar Sin, wato ke nan rabin lokacin da aka shafe a rayuwa na watanni shida a sararin samaniya.
A cikin wannan lokaci, ‘yan sama jannatin kasar Sin guda uku, sun kammala wasu ayyuka masu muhimmanci, ciki har da zagaye a wajen kumbon. Wang Yaping, wadda ta je sararin samaniya a karo na biyu, ta zama ‘yar sama jannatin kasar Sin ta farko da ta fara tafiya a wajen kumbon, inda ta kafa wani sabon tarihi a masana’antar sararin samaniyar kasar Sin, da kuma ba da gudummawar “kwarewar mace ‘yar sama jannati” ga bunkasuwar masana’antar a duniya baki daya.
Mafarkin Wang Yaping na zuwa sararin samaniya, ya samo asali ne daga aikin da ya shafi kumbon jigilar ‘yan sama jannati na farko na kasar Sin a shekarar 2003. Bayan cimma nasarar harba kumbon Shenzhou-5, Wang Yaping, wadda ta kasance matukin jirgin saman soja a lokacin, ta fara mafarkinta na zuwa sararin samaniya mai nisa.
Wang Yaping ta bayyana cewa, lokacin da na kalli kyakkyawar wutar jelar rokar da aka harba, kwatsam sai wani tunani ya fado a cikin zuciyata, muna da ‘dan sama jannati na farko a kasar Sin, yaushe ne za mu samu ‘yar sama jannati a kasarmu? A wannan lokaci ne, na fara mafarki game da ziyartar sararin samaniya wanda ya dade yana kasancewar a cikin zuciyata. Ni ma ina so in kalli yanayin da sararin samaniya yake, kuma ina so in ba da gudummawa ta dan kadan kan cimma burinmu na Sinawa na zuwa sararin samaniya.
A shekarar 2010, Wang Yaping ta zama daya daga cikin ‘yan sama jannati mata na farko na kasar Sin, saboda kwarewar da take da su na tashi sama da kuma kyawawan halaye na tunani. A watan Yuni na shekarar 2013, ta shiga kungiyar kumbon Shenzhou-10 tare da sauran ‘yan sama jannati maza biyu, wato su Nie Haisheng da Zhang Xiaoguang don ziyartar sararin samaniya. Wang Yaping ta ce, a wannan lokacin, ban a jin wani tsoro a raina, sai dai akwai wasu kalmomi guda shida, wato alhaki, nauyi da kuma cimma mafarki
A ranar 7 ga watan Nuwamba na shekarar 2021 agogon Beijing, ‘yan sama jannatin Shenzhou-13, sun gudanar da ayyukansu na farko na yin zagaye a wajen kumbon. Bayan fita daga kofar kumbon, Wang Yaping ta matsa wajen hannun matakala zuwa wurin gudanar da aikin hadewa don taimakawa Zhai Zhigang wajen hada na’urar dakatar da hannun mutum-mutumi bayan fita daga kunbon. Wang Yaping ya matsa zuwa wajen da za a hade sassan kumbun tare da taimakon Zhai Zhigang don kafa hannun na’urar. Daga baya kuma, ta tsaya kan hannun mutum-mutumi ta yi gwajin motsi na yau da kullun a waje. “Mataki na farko” da ‘yar sama jannati ta kasar Sin ta yi ya yi daidai kamar yadda aka tsara.
Kafin Wang Yaping, tun daga shekarar 1984, akwai mata guda 15 a wasu sassan duniya duniya, da suka taba gudanar da ayyukan zagaye a wajen kumbo. A wannan karon, fitowar Wang Yaping daga cikin kunbom ya kuma jawo hankalin duniya da kuma yabawa. A wannan karon, fitowar Wang Yaping ta kuma jawo hankali da kuma samun yabo daga duniya baki daya. Tsohuwar ‘yar sama jannati ta NASA Cady Coleman ta rubuta wa Wang Yaping cewa: “Idan kin kalli waje ta tagar, za ki ga manyan taurari, da kasa daga wuri mai nisa, kar ki manta cewa, mata a duniya ma sun kalli wajen tagar ta idanunki, ciki har da ni.
“Irin wannan nasarar da aka cimma, ta kara karfin kasar Sin a fannin bincike sararin samaniya. Game da aikin shigar da ‘yan sama jannati mata cikin ayyukan zuwa sararin samaniya, tawagar ayyukan Shenzhou-13 ta yiwa kumbo da tashar sararin samaniya cikakken shiri. Kakakin hukumar kula da sararin samaniyar kasar Sin, kuma mataimakin darektan ofishin injiniyan sararin samaniyar kasar Lin Xiqiang, ya bayyana cewa, tawagar ta Shenzhou-13 ta yi nazari kan halaye na zahiri da bukatu na ‘yan sama jannati mata, tare da tsara shirin musamman dake dora muhimmanci kan tabbatar da zaman rayuwa da kiwon lafiya, ta yadda za a ba da tabbaci ga ‘yan sama jannati mata, don su saba da yanayin zama da aiki yadda ya kamata a cikin dogon lokaci.
Dangane da samun horo, ‘yan sama jannati mata da maza suna amfani da ma’auni iri daya ne. A lokacin da ake yin horo na tsawon lokaci a karkashin ruwa, ‘yan sama jannatin na bukatar sanya rigar samun horo mai nauyin kilogiram 200 da za su shafe tsawon sa’o’i shida ko bakwai, kuma yana da nauyi sosai. Domin girman jikinta bai kai na ‘yan sama jannati maza ba, Wang Yaping ba za ta iya sarrafa rigar ta sararin samaniya ba. Don haka, tana bukatar karfi ninka sau biyu bisa na ‘yan sama jannatin maza don kammala aikin.
Domin rage gibin dake tsakaninta da ‘yan sama jannati maza, sai ta rika yin horo akai-akai. Bayan kowane horo, ko da yake ta gaji sosai, amma Wang Yaping tana farin ciki sosai, saboda kwarewarta ta kara inganta, kuma tana kara kusantar tabbatar da mafarkinta.
“Kowa yana cike da kwarin gwiwa kan ‘yan sama jannatin mata da ke fita daga kumbo, kuma ni ma ina da kwarin gwiwa.” Kamar yadda Wang Yaping ta taba fada kafin soma gudanar da ayyukan Shenzhou-13. Bayan shiga tashar sararin samaniya da kuma fita daga kumbo yadda ya kamata, burinta ya cika.
Zaman rayuwar Wang Yaping a tashar sararin samaniya wani aiki ne na musamman, wato koyar da “Darasi a karo na Biyu a Sararin Samaniya” a tashar. A yayin gudanar da ayyukan Shenzhou-10, Wang Yaping ta taba koyar da daliban firamare da sakandare miliyan 60 darasi daga Kumbon Tiangong-1. Yanzu, bayan shekaru takwas, a ranar 10 ga watan Disamba na shelarar 2021, Wang Yaping ta kara zama malama dake koyar da darasi a tashar sararin samaniya ta gabatar da shirye-shiryen bidiyo kai tsaye zuwa doron duniya, wanda ya sa mutane da yawa jin dadin kallo da jin mamaki.
Wang Yaping ta bayyana cewa, wannan ya sa na ji mahimmancin koyarwa a sararin samaniya, yara da dama sun soma kauna da ma sha’awar sararin samaniya saboda haka, wasu dalibai suka nemi koyon fasahar injiniyan sararin samaniya, har wasu kuma sun zama abokan aikina a yanzu, wanda kuma ya sa ni alfahari.
Wang Yaping ta kara da cewa, “tashar sararin samaniya ta kasar Sin, wani gagarumin aiki ne na masana’antar sararin samaniya ta kasarmu a sabon zamani, ina sa ran gudanar da karin bincike a tashar ta kasar Sin, da kuma gudanar da bincike da ya shafi rayuwar dan Adam mai ban sha’awa a nan”